Buhari da Muslim

Babi na Ashirin da Biyu: Bisa fadar Madaukaki cewa: “Mun yi wa’adi ga Musa dare talatin…har zuwa fadarsa- ni ne farkon mumminai (K:7:142:143).” Nan ma mun takaita game da fassarar kalmomi. 328. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru dan Yahaya daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda […]

Buhari da Muslim

Babi na Ashirin da Biyu:

Bisa fadar Madaukaki cewa: “Mun yi wa’adi ga Musa dare talatin…har zuwa fadarsa- ni ne farkon mumminai (K:7:142:143).” Nan ma mun takaita game da fassarar kalmomi.

328. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru dan Yahaya daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Daga Annabi (SAW) ya ce: “Mutane za a sumar da su Ranar Kiyama, sai in kasance farkon wanda zai farka. Sai in iske Musa (AS) yana rike da wani ginshiki daga ginshikin Al’arshi ban sani ba shin ya farka ne gabanina ko kuwa an bar shi ne bai mutu ba tun sumar da shi da aka yi a Dutsen Duri?”

329. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad Alju’afi ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari ya ce Ma’amar ya ba mu labari dga Hammam daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Ba domin (saboda) Isra’ila ba da nama ko ya kwana bai yin bashi (wari). Kuma ba domin Hawwa’u ba da mace ba ta butulce wa mijinta ba a tsawon zamani.”

 

Babi na Ashirin da Uku:

Malalen teku, Abin da aka ambata game fashewar teku a kan jama’ar da suka yi taurin kai. Kuma akan ce wa yawan mace-mace-Dawafan. Alkumali- kwarkwata, Hakikun na nufin gaskiya. Sukida na nufin dukkan abin da mutum ya yi nadama kansa, akan ce ya fada hannunsa.

 

Babi na Ashirin da Hudu:

Labarin Khadir tare da Musa (AS):

330. An karbo daga Amru dan Muhammad ya ce: “Yakub dan Ibrahim ya ba mu labari ya ce, babana ya ba ni labari daga Salih daga Dan Shihab cewa: “Lallai Ubaidullahi dan Abdullahi ya ba shi labari daga Dan Abbas (RA) cewa: “Lallai shi ya yi musu da Hurru dan Kaisu Alfazari game da abokin Musa (AS).

Dan Abbas ya ce, “Shi ne Khadir, sai Ubayyu dan Ka’ab ya wuce su, Abdullahi dan Abbas ya kira shi ya ce: “Lallai ni na yi musu da abokina wannan game da mutumin da Musa ya nemi haduwa da shi bisa tsibiri. Shin ko ka ji Manzon Allah (SAW) yana ambaton sha’aninsu? Ya ce: “Na’am, na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wata rana Musa yana tsakanin manyan Bani Isra’ila sai wani mutum ya zo masa ya ce: “Shin ko ka san wanda ya fi ka sani? Ya ce: “A’a, sai Allah Ya yi wahayi zuwa ga Musa cewa: “Gaskiya akwai wanda ya fi ka, shi ne bawanmu Khadir.” Sai Musa ya nemi (roki) hanyar haduwa da shi, sai aka sanya masa kifi ya zamo masa alama. Aka ce masa idan ka rasa kifin nan ka koma lallai za ka hadu da shi. Sai ya kasance yana bin kifi a kogi.

Sai yaron Musa ya ce masa: Shin ko ka ga lokacin da muka taro zuwa ga falalen nan hakika ni na manta da kifin nan, babu abin da ya mantar da ni shi face Shaidan ko in tuna shi. Sai Musa ya ce: “Wannan ai shi muke nema, sai suka juya bisa gurabansu suna neman labari (bincike). Sai suka iske Khadir, sai ya kasance abin da ya faru game da ci gaban labarinsu shi ne wanda Allah Ya bayar da labari cikin LittafinSa (Alkur’ani).”

331. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba mu labari ya ce, Sa’id dan Jubair ya ba ni labari ya ce, “Na ce, wa Dan Abbas lallai Naufal Bakkali yana riyawa cewa: Lallai Musan da ya hadu da Khadir ba Musan Bani Isra’ila ba ne, wani Musan ne. Sai (Dan Abbas) ya ce: “Makiyin Allah ya yi karya, Ubayyu dan Ka’ab ya ba ni labari daga Annabi (SAW) cewa: Lallai Musa ya taba mikewa yana huduba cikin manyan Bani Isra’ila sai aka tambaye shi: “Wa ya fi kowa sani cikin mutane? Sai ya ce: Ni ne, sai Allah Ya zarge shi saboda bai mayar da sani wajen Allah ba.

Ya ce masa: Gaskiya ce akwai wani bawa a Mahadar Teku Biyu shi ya fi ka sani. Sai ya ce ya Ubangiji! Yaya zan hadu da shi? Ya ce, “Sai ka dauki kifi ka sanya shi cikin sanho (kwando) duk inda ka rasa shi to, a nan yake. Sai ya dauki kifin ya sanya cikin sanho, sa’an nan ya tafi shi da yaronsa Yusha’u dan Nun har sai da suka kai ga falalen nan, suka dora kawunansu suka yi hutu. Musa ya yi barci kifi ya motsa ya fice ya fada cikin teku ya kama hanyarsa cikin teku kamar kawalweniyar kan hanya (akwai alama).

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa