Buhari da Muslim

451. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Sa’id xan Musayyib ya ba ni labari da Abu Salmah xan Abdurrahman cewa: “Lallai Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya mike lokacin da wannan aya ta sauka cewa: “Ka yi wa […]

Buhari da Muslim

451. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Sa’id xan Musayyib ya ba ni labari da Abu Salmah xan Abdurrahman cewa: “Lallai Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya mike lokacin da wannan aya ta sauka cewa: “Ka yi wa danginka makusanta gargaxi…” (k:26:214), ya ce: “Ya jama’ar kuraishawa! Ko ya faxi wata kalmar kamarta cewa: Ku sayi (fanshi) kawunanku, ba ni wadatar muku komai a wajen Allah. Ya Bani Abdul Munaf ban iya wadatar muku komai daga wajen Allah. Ya Abbas xan Abdulmuxallib ban iya wadatar maka komai daga wajen Allah. Ya Safiyya gwaggon Manzon Allah ban iya wadatar miki komai daga wajen Allah. Ya Faxima ’yar Manzon Allah ki roke ni cikin dukiyata, ban iya wadatar miki komai daga wajen Allah.” Asbag ya karbo shi daga XanWahab daga Yunus daga Xan Shihab.

 
Babi na Goma Sha Biyu:
Shin mai sadakar wakafi zai iya amfani da abin sadakar wakafinsa? Lallai Umar (Allah Ya yarda da shi), ya sharxanta cewa: “Babu laifi ga wanda ya shugabanci gona ya ci daga gare ta bisa kyautatawa. Kuma lallai mai sadakar wakafi yakan shugabanci sadakar da waninsa. Haka wanda ya sanya taguwar hadayarsa ko wani abu don Allah yana da ikon amfani da ita, kamar yadda waninsa zai iya amfani da ita, matukar dai bai sharxanta komai ba.”
452. An karbo daga kutaiba ya ce: “Abu Awanata ya ba mu labari daga kattada daga Anas (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ga wani mutum yana kora taguwar hadayarsa, sai ya ce, masa: “Ka hauta.” Sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Taguwar hadaya ce.” Sai Annabi ya ce masa a ta uku, ko ta huxu: “Kaiconka! Ka hauta.”
453. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Zinad daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ga wani mutum yana kora taguwar hadaya. Sai ya ce: “Ka hauta.” Sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Taguwar hadaya ce.” Ya ce, “Ka hauta, kaiconka a ta biyu ko ta uku.”
 
Babi na Goma Sha Uku:
Idan mutum ya yi sadakar wakafi na wani abu kafin ya mika shi ga waninsa ya halatta. Domin Umar (Allah Ya yarda da shi), ya yi wakafi, sai ya ce: “Babu laifi ga wanda ya shugabance shi ya ci, bai kebance in Umar ya shugabance shi ko waninsa ba.” Annabi (SAW) ya ce ga Abu Xalha cewa: “Ina ganin ya kamata ka sanya ta (raba ta sadakar) a cikin danginka makusanta.” Sai ya ce, “Zan aika ta, sai ya raba ta a cikin makusantarsa da ’ya’yan baffaninsa.”
 
Babi na Goma Sha Huxu:
Idan mutum ya ce: “Gidana, na bayar da shi sadaka domin Allah amma bai ce ga fakirai ba ko waninsu ba haka ya halatta.” Yana iya bayar da shi ga danginsa makusanta ko duk inda ya so. Annabi (SAW) ya ce wa Abu Xalha lokacin da ya ce: “Fiyayyiyar dukiyata ita ce, wadda take Burha’u kuma na bayar da ita sadaka domin Allah.” Sai Annabi (SAW) ya halatta haka.” Waxansu sun ce: “Ba ya halatta har sai mutumin ya bayyana ga wanda ya bayar, koda yake maganar farko ita ce, mafi inganci.”