Buhari da Muslim
Babi na Goma Sha Biyar: Wanda ya yi yaki domin kalmar Allah ta zamo itace madaukakiya: 500. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Amru daga Abu Wa’il daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wani mutum ya je zuwa ga Annabi (SAW) sai ya […]
Babi na Goma Sha Biyar: Wanda ya yi yaki domin kalmar Allah ta zamo itace madaukakiya:
500. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Amru daga Abu Wa’il daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wani mutum ya je zuwa ga Annabi (SAW) sai ya ce: “Daga cikin mutane akwai wanda ke yakin nan domin samun ganima, wani kuma yana yakin ne saboda neman suna, wani kuma yana yakin ne saboda nuniya (riya), wane ne ke yakinsa ta hanyar daukaka kalmar Allah? (Annnabi) ya ce: “Wanda duk ya yi yakin saboda kalmar Allah ta daukaka, to shi ne yake yaki domin Allah.”
Babi na Goma Sha Shida:
Wanda duddugensa suka yi kura wajen yakin daukaka kalmar Allah. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ba ya kasancewa ga mutanen Madina da wanda yake a gefensu daga kauyawa, su saba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rayukansu daga ransa. Wancan saboda kishirwa ba ta samunsu, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyar Allah, kuma ba su takin wani mataki wanda yake takaitar da kafirai kuma ba su samun wani samu daga makiyi face an rubuta musu da shi, ladar aiki na kwarai. Lallai ne Allah ba Ya tozarta ladar masu kyautatawa.” (k:9:120).
501. An karbo daga Is’hak ya ce: “Muhammad dan Mubarak ya ba mu labari ya ce, Yahya dan Hamza ya ba mu labari ya ce, Yazid dan Abu Maryam ya ba mu labari ya ce, Ababa dan Rifa’ah dan Rafi’u da Khadeej ya ce; “Abu Absin Abdurrahman dan Jabrin cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wata kura ba za ta taba duddugen wani bawa wajen daukaka kalmar Allah ba kuma a ce wuta ta kona shi (wato duk wanda ya samu wata kura ko rauni a wajen daukaka kalmar Allah kuma a kona shi da wuta).”
Babi na Goma Sha Bakwai: Share kura daga kan wani mutum wajen aikin daukaka kalmar Allah:
502. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Abdulwahab ya ba mu labari ya ce, Khalid ya ba mu labari daga Ikrama cewa: Lallai danAbbas ya fada masa cewa shi da Aliyu dan Abdullahi sun je ga Abu Sa’id suka saurara daga hadisinsa, suka tafi shi da dan uwnsa cikin wani kangonsu (gonarsu) suna ban ruwa. Lokacin da ya gan mu sai ya zo ya zabi wuri ya zauna ya ce: “Mun kasance muna daukar tubali dai-dai lokacin ginin Masallaci, Ammar kuma ya kasance yana daukar tubali bibbiyu. Sai Annabi (SAW) ya shude da shi ya rika share masa kura daga kansa ya ce: “Allah Ya jikan Ammar, wata kungiya azzaluma za ta kashe shi. Ammaru na kiransu zuwa ga Allah suna kiransa zuwa wuta.”
Babi na Goma Sha Takwas: Wanka bayan kare yaki ko saboda kura:
503. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdatu ya ba mu labari daga Hisham dan Urwatu daga Babansa daga A’isha (RA) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) lokacin da ya komo da Khandak ya aje makami, sai ya yi wanka, sai Jibrilu ya zo masa lokacin kura ta rufe kansa ya ce masa: “Ka aje makami! Wallahi ban aje shi (nawa takobin) ba,” sai Manzon Allah (SAW) ya ce, sai ina? Ya ce, “Ta nan, ya yi nuni zuwa kabilar Bani kuraizah.” A’isha ta ce, “Sai Manzon Allah (SAW) ya fita zuwa gare su.”