Buhari da Muslim

Babi na Goma Sha daya: Idan wakili ya sayar da wani abu batacce (mara kyau) cikin batacce ne: 47. An karbo Is’hak ya ce: “Yahya dan Salih ya ba mu labari ya ce, Mu’awiyya dan Sallam ya ba mu labari daga Yahya ya ce: “Na ji Ukbatu dan Abdulghafir ya ce, lallai shi ya ji […]

Buhari da Muslim
Buhari da Muslim

Babi na Goma Sha daya: Idan wakili ya sayar da wani abu batacce (mara kyau) cikin batacce ne:

47. An karbo Is’hak ya ce: “Yahya dan Salih ya ba mu labari ya ce, Mu’awiyya dan Sallam ya ba mu labari daga Yahya ya ce: “Na ji Ukbatu dan Abdulghafir ya ce, lallai shi ya ji Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Bilal ya zo ga Annabi (SAW) da wasu dabinai na Barni (wani nau’in dabino), sai Annabi (SAW) ya ce, masa: “Daga ina ka samo wannan? Bilal ya ce, “Ya kasance ina da wasu dabinai marasa kyau, sai na sayar da su bisa sa’i biyu a kan sa’i daya na wannan, domin in ciyar da Annabi (SAW) da shi. Sai Annabi (SAW) ya fadi masa game da haka cewa: Awah! (Ka kiyaye) Awah! (Ka kiyaye), hakika wannan riba ce! Hakika wannan riba ce! Kada ka sake aikata haka, idan kana son haka, to, lallai ka sayar da mara kyau sa’an nan ka sayi mai kyau da shi (kudin).”

Babi na Goma Sha Biyu: Wakiltawa a cikin dukiyar wakafi (dukiyar da aka bari domin jama’a su yi amfani da ita kyauta domin daukaka kalmar Allah) da ciyar da ita da kuma bayanin wakili zai iya ciyar da da abokansa da ita, kuma wakili zai ci bisa kyautatawa:
48. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru ya ce, game da dukiyar sadakar Umar (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Babu laifi ga wakili ya ci daga dukiyar sadaka (wakafi) kuma yana iya ciyar da abokansa mabukata, ban da wanda ke neman tara wa kansa dukiya da haka. Sai dan Umar ya kasance yana bin (karbar) sadakar Umar yana kyauta da ita ga mutane daga mutanen Makka wadanda suke sauka a gidansa.”

Babi na Goma Sha Uku: Wakilci a cikin haddodi (kamar bulalar zina ko shan giya):
49. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga dan Shihab daga Ubaidullahi daga Zaid dan Khalid da Abu Huraira (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Ya Unaisa ka tafi zuwa ga wanccan mata, idan ta yi furuci da yin zina ka jefe ta.” (Wannan Hadisi yana karantar da wakilta wani wajen zartar da dokar Allah).
50. An karbo daga dan Sallam ya ce: “Daga Abdulwahab Sakafiyyu daga Ayyub daga dan Abu Mulaikata daga Ukbatu dan Haris ya ce: “An zo da Nu’aman ko ya ce, da dan Nu’aman mashayin giya (zuwa ga Manzon Allah (SAW). Sai Manzon Allah (SAW) ya umarci wandanda suka kasance a cikin gida da su yi masa bulala.” Ukbatu Ya ce, “Sai na kasance daga cikin wadanda suka yi masa bulala, mun doke shi ne da takalma marasa rufi da bulalar tankar dabino.”

Babi na Goma Sha Hudu: Wakilci bisa dabbar hadaya da lura da su:
51. An karbo daga Isma’il dan Abdullahi ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Abdullahi dan Abubakar dan Hazmi daga Amrata ’yar Abdurrahman cewa: Lallai ita, ta ba shi labari ta ce, “A’isha (Allah Ya yarda da ita cewa: “Na tubka ratayar taguwar hadaya ta Manzon Allah (SAW) da hannuna sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya rataya ta da hannayensa. Sa’an nan ya aika ta tare da Babana (zuwa Makka). Babu abin da ya haramta wa Manzon Allah (SAW) wanda Allah Ya halatta masa har sai da ya soke hadayarsa.”