Buhari da Muslim
Babi na Talatin da Biyu: Bayanin karya gicciye da kashe aladu:196. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari, ya ce, Zuhuri ya ba mu labari ya ce, Sa’id dan Musayyib ya ce: “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “kiyama ba […]
Babi na Talatin da Biyu: Bayanin karya gicciye da kashe aladu:
196. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari, ya ce, Zuhuri ya ba mu labari ya ce, Sa’id dan Musayyib ya ce: “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “kiyama ba za ta tsayuwa ba, har sai dan Maryam ya sauka a cikinku yana mai hukunci da adalci. Kuma zai karya alamar gicciye zai kashe aladu, zai kore karbar haraji zai watsa dukiya har ya zamo babu mai karba.”
Babi na Talatin da Uku:
Shin halal ne a fashe tukwanen giya kuma suna dauke da giyar ko salkar da ke dauke da giya? Kuma idan mutum ya karya gumaka ko gicciye ko ganga ko dukiyar da ake amfani. An zo wa Shuraih da ganga wadda aka karya bai yi hukuncin komai ba ga haka.
197. An karbo daga Abu Asim Dahhak dan Makhlad ya ce: Daga Yazid dan Ubaid daga Salmat dan Akwa’u (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ga wani hasken wuta da ake kunnawa a ranar yakin Khaibara ya ce: “Saboda me aka kunna waccan wuta? Suka ce, “Saboda dahuwar jakunan gida. Sai ya ce, “Ku karya ta, ko watsa mata ruwa.” Suka ce, “Shin ba za mu watsa mata ruwa mu wanke ba? Ya ce, “To ku wanke.”
198. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, dan Abu Najih daga Mujahid daga Abu Ma’amar daga Abdullahi dan Mas’ud (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya shiga garin Makka lokacin a gefen Ka’aba akwai gumaka dari uku da sittin wadanda suke kafe. Sai ya rika sukarsu da sandar da ke cikin hannunsa. Kuma ya rika cewa: “Gaskiya ta zo karya ya tafi (gushe)… Har karshen aya.”
199. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas dan Iyad ya ce, daga Ubaidullahi daga Abdurrahman dan kasim daga Babansa kasim daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai ta kasance ta taba rataya labule wanda ake yi masa launi da hotuna. Sai Annabi (SAW) ya keta shi, sai ta rika amfani da su ta hanyar yi masa abin zama biyu da su a cikin daki ya rika zama a kansu.”
Babi na Talatin da Hudu: Wanda ya yi yaki domin kare dukiyarsa:
200. An karbo daga Abdullahi dan Yazid ya ce: “Sa’id dan Abu Ayyub ya ba mu labari ya ce, Abu Aswad ya ba ni labari daga Ikramat daga Abdullahi dan Amri (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda aka kashe saboda dukiyarsa ya yi shahada.”
Babi na Talatin da Biyar: Wanda ya karya akushi ko wani abu ga waninsa:
201. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya dan Sa’id ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) wata rana ya kasance tare da wasu matansa, sai wata mace daga uwayen muminai ta aika mai yi mata hidima da wani akushi a cikinsa da abinci, sai daya daga cikin matan (ko baiwar) ta fadar da (akushin) daga hannunta akushin ya fashe sai (Annabi) ya karba ya hada shi, ya sanya abincin a cikinsa. Ya ce, “Ku ci, Annabi ya karbe wannan akushi har sai da suka kare ci. Ya musanya da wani akushi mai kyau, ya rike fasasshen.”