Buhari da Muslim: Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi
Babi na Ashirin da Tara: Wanda ya tara da matarsa a cikin Ramadan, an ambata daga Abu Huraira ya daukaka shi cewa: Wanda ya ci abinci da rana a Ramadan ba tare da wata illa (lalura) ba, kuma ba wata cuta to yin azumin zamani ba zai biya masa ba koda ya azumce shi, da […]
Babi na Ashirin da Tara:
Wanda ya tara da matarsa a cikin Ramadan, an ambata daga Abu Huraira ya daukaka shi cewa: Wanda ya ci abinci da rana a Ramadan ba tare da wata illa (lalura) ba, kuma ba wata cuta to yin azumin zamani ba zai biya masa ba koda ya azumce shi, da shi dan Mas’ud ya ba da fatawa. Amma Sa’id dan Musayyab da Sha’abi da dan Jubair da Ibrahim da kattada da Hammad sun ce, “Zai biya wannan yinin da ya wuce masa.”
395. An karbo daga Abdullahi dan Munir ya ce: “Ya ji Yazid dan Haruna ya ce, Yahya dan Sa’id ya ba mu labari cewa: “Lallai Abdurrahman dan Alkasim ya ba shi labari daga Muhammad dan Ja’afar dan Zubair dan Awwam dan Khuwailid daga Abbad dan Abdullahi dan Zubair ya ba shi labari cewa: “Lallai shi ya ji A’isha (Allah Ya yarda da ita), tana cewa: “Lallai wani mutum ya zo ga Annabi (SAW) ya ce, “Lallai shi ya kone (halaka),” (Annabi) ya ce, “Me ya faru da kai? Ya ce, “Na tara da matata a cikin Ramadan, sai aka zo wa Annabi (SAW) da awon da ake kira Arak na dabino, ya ce, “Ina wanda ya konen nan? Ya ce, “Ga ni,” ya ce, “Ka yi sadaka da wannan.”
Babi na Talatin: Idan mutum ya tara da matarsa cikin Ramadan kuma ba ya da komai da zai yi sadaka da shi sai ya yi kaffara:
396. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Humaid dan Abdurrahman ya ba ni labari cewa: “Lallai Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wata rana muna zaune a wurin Annabi (SAW) sai wani mutum ya zo masa ya ce: “Ya Manzon Allah! Na halaka,” (Annabi) ya ce, “Me ya faru? Ya ce, “Na fada (sadu da) matata alhali ina azumi.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Shin kana da baiwa da za ka ’yanta? Ya ce, “A’a.” Ya ce, “Shin kana da ikon yin azumi wata biyu jere? Ya ce, “A’a.” Sai ya ce, “Shin za ka iya ciyar da miskinai sittin? Ya ce, “A’a.” Ya ce, “Sai Annabi (SAW) ya zauna haka bai ce komai ba. Muna cikin haka sai aka zo wa Annabi (SAW) da awon Arak na dabino. Shi Arak wani sanho ne (ma’auni) sai (Annabi) ya ce, “Ina mai tambaya ya ce, “Ga ni.” Ya ce, “Karbi wannan ka yi sadaka da shi,” sai mutumin nan ya ce, “Shin akwai wanda ya fi ni bukata kuwa? Ina rantsuwa da Allah tun daga abin da ke tsakanin tsaunukanta biyu, yana nufin Harra biyu na Madina, babu wasu iyalan da suka fi iyalaina bukata (talauci).” Sai Annabi (SAW) ya yi murmushi har sai da hakoransa suka bayyana. Sa’an nan ya ce, “Ka ciyar da iyalanka da shi.”
Babi na Talatin da daya: Wanda ya sadu da matarsa a cikin Ramadan shin zai iya ciyar da iyalansa daga abin kaffara idan sun kasance mabukata?:
397. An karbo daga Usman dan Abu Shaiba ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Zuhuri daga Humaid dan Abdurrahman daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Wani mutum ya zo ga Annabi (SAW) ya ce: “Lallai ya tara da matarsa a cikin Ramadan,” sai (Annabi) ya ce, “Shin kana da abin da za ka ’yanta wuya (bawa)? Ya ce, “A’a.” Ya ce, “Shin za ka iya azumin wata biyu jere? Ya ce, “A’a.” Ya ce, “Shin kana da abin da za ka ciyar da miskinai sittin? Ya ce, “A’a.” Ya ce, “Sai aka zo wa Annabi (SAW) da awon Arak dabino na cike da shi, shi ne ake kira Zabil ya ce, “Ka ciyar da wannan a matsayin kaffararka.” Ya ce, “Shin akwai wanda ya fi ni bukata kuwa? Koda abin da ke tsakanin tsaunukan nan biyu babu wanda ya fi mu bukata.” (Annabi) ya ce, “Ka ciyar da iyalanka da shi.”