Buhari da Muslim: Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 01
606. An karbo daga Saltu dan Muhammad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Abdullahi dan dawus daga Babansa daga dan Abbas Allah Ya yarda da su, ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada ku rika taryan ayarin ’yan kasuwa do ku sayar musu da kaya. […]
606. An karbo daga Saltu dan Muhammad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Abdullahi dan dawus daga Babansa daga dan Abbas Allah Ya yarda da su, ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada ku rika taryan ayarin ’yan kasuwa do ku sayar musu da kaya. Kuma kada mazaunin gari ya sayar wa mutumin kauye da kayansa ya bar shi ya sayar da kansa.” Ya ce, “Na ce, wa dan Abbas mene ne ma’anarsa cewa “Kada mutum birni ya sayar wa mutumin kauye da kayansa? Ya ce, “Yana nufin kada ya zama kamar dillali.”
Babi na Saba’in: Wanda ya hana mutumin birni ya sayar wa mutumin kauye da kaya bisa jinga (lada):
607. An karbo daga Abdullahi dan Sabbah ya ce: “Abul A’alah Alhanafi ya ba mu labari daga Abdurrahman dan Abdullahi dan Dinar ya ce, “Babana ya ba ni labari daga Abdullahi dan Umar (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya hana mutumin birni ya sayar wa mutumin kauye da kayansa don wayon riba.” Da wannan dan Abbas ya ba da labari.
Babi na Saba’in da daya:
Mazaunin birni ba ya sayar wa mutumin kauye da kaya bisa hanyar dillanci. dan Sirin ya karhanta (hana) game da haka, da shi da Ibrahim, ga mai sayarwa da mai saye. Ibrahim ya ce, “Labarawa na cewa, sayar mini da wannan tufafi, alhali na nufin, “na sayarwa.”
608. An karbo daga Almakkiyu dan Ibrahim ya ce: “dan Juraij ya ba ni labari daga dan Shihab daga Sa’id dan Musayyib cewa: Lallai shi ya ji Abu Huraira (RA) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada mutum ya yi ciniki bisa cinikin dan uwansa, kuma kada ku yi ha’inci, kada mazaunin gari ya sayar wa mutumin kauye da kayansa bisa dillanci.”
609. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Mu’azu ya ba mu labari ya ce, dan Aunu ya ba mu labari daga Muhammad ya ce, “Anas dan Malik ya ba ni labari cewa: “An hana mana mutumin birni ya sayar wa mutumin kauye da kaya bisa dillanci.”
Babi na Saba’in da Biyu:
Hani game da taryar mahaya (ayari). Kuma lallai ciniki haka ba karbabbe ne ga duk wanda ya yi shi domin mai aikata haka, mai sabo ne, kuma mai laifi idan ya kasance yana da sanin haka, kuma shi yaudara ne ba ya halatta:
610. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Abdulwahab ya ba mu labari ya ce, Ubaidullahi ya ba mu labari daga Sa’id dan Abu Sa’id daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da taryar mahaya (ayari), kuma ya hana mazaunin gari ya sayar wa mutumin kauye da kayansa (ta hanyar dillanci).”
611. An karbo daga Ayyash dan Walid ya ce: “Abdul A’alah ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga dan dawus daga Babansa ya ce, “Na tambayi dan Abbas (RA), cewa: “Mene ne ma’anar maganarsa (Annabi) cewa, “Kada mazaunin gari ya sayar wa mutumin kauye da kaya? Sai ya ce, “Kada ya zamo masa kamar dillali.”
612. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yazid dan Zurai’u ya ba mu labari ya ce, Tamimi ya ba ni labari daga Abu Usman daga Abdullahi (RA) ya ce: “Wanda ya sayi dabbar da hantsarta ke da nono na yaudara, idan ya sha nonon, to ya mayar da ita Sa’i daya na dabino.” Ya ce, “Annabi (SAW) ya hana game da taryar kayan kasuwanci daga wajen gari.”
613. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (RA), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada sashinku ya yi ciniki bisa cinikin sashi. Kuma kada ku rika kamen (taryen) kayan fatauci har sai an sauke su a kasuwa.”