Buhari da Muslim: Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 02
Babi na Saba’in da Shida: Cinikin zabibi da zabibi da abinci bisa abinci: 619. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin muzabanat, muzabanta kuwa shi ne: “Cinikin sabo (danyen) dabino da […]
Babi na Saba’in da Shida: Cinikin zabibi da zabibi da abinci bisa abinci:
619. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin muzabanat, muzabanta kuwa shi ne: “Cinikin sabo (danyen) dabino da tsohon dabino busasshe bisa awo. Da cinikin sabo (danyen) inabi da tshohon inabi busasshe bisa awo,”
620. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya hana game da cinikin muzabanat, sai ya ce: “Ma’anar muzabanat ita ce cinikin danyen kayan lambu (babu gwaji) da wani kayan lambun bisa gwaji da yarjejeniyar idan awon ya karu na ga mai sayarwa, amma idan ya ragu na kaina (mai saye).” Ya ce, Zaidu dan Sabit yana cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya yi rangwame bisa cinikin ’ya’yan itace idan aka lisafce (abin da za a samu lokacin diba).”
Babi na Saba’in da Bakwai: Cinikin sha’ir da sha’ir:
621. An karbo daga Abdullahi danYusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Malik dan Ausu ya ba shi labari cewa, lallai shi ya nemi musanyar zinari dari. Sai dalhatu dan Ubaidullah muka yi magana game da wannan sha’ani sai ya yarda zai musanya mini zinarina. Sai ya karbi tsabar dinaren bisa hannunsa yana juya su ya ce: “Mai tsaron taskata zai komo daga daji.” Lokacin Umar yana jin haka, sai ya ce, “Wallahi kada ka rabu da shi har sai ka karbi kudinka (canjinka) daga gare shi, saboda Manzon Allah (SAW) ya ce, “Cinikin zinari da zinari akwai riba a ciki face an biya hannu da hannu, haka alkama da alkama akwai riba face hannu da hannu, haka sha’ir da sha’ir akwai riba, face hannu da hannu, haka dabino da dabino akwai riba a ciki face hannu da hannu.”
Babi na Saba’in da Takwas: Cinikin zinari da zinari:
622. An karbo daga Sadakat dan Fadalu ya ce: “Isma’il dan Ulaiyyata ya ba mu labari ya ce, Yahya dan Abu Is’hak ya ba ni labari ya ce, Abdurrahman dan Abubakarata ya ce, Abubakarata (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kada ku sayar da zinari da zinari face misali da misali (daidai), haka azurfa da azurfa face misali da misali, kuna iya sayar da zinari da azurfa ko azurfa da zinari duk yadda kuka so.”
Babi na Saba’in da Tara: Cinikin azurfa da azurfa:
623. An karbo daga Ubaidullahi dan Sa’ad ya ce: “Baffana ya ba mu labari ya ce, dan uwana Zuhuri ya ba mu labari daga Baffansa ya ce, Salim dan Abdullahi ya ba ni labari daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Abu Sa’id ya ba shi labari da misalin wannan Hadisin daga Manzon Allah (SAW). Sai Abdullahi ya hadu da shi ya ce, “Ya Abu Sa’id mene ne wannan kake ba da labari daga Manzon Allah (SAW)? Sai Abu Sai’id ya ce, “Game da musanya ce, na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Musanya zinari da zinari misali da misali, azurfa da azurfa misali da misali.”
624. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abu Sa’idul Khudiri (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada ku sayar da zinari da zinari face misali da misali, kuma kada sayar da kudi kadan a kan kudi mai yawa. Kuma kada ku sayar da azurfa da azurfa face misali da misali, kuma kada ku sayar da kudi kadan bisa kudi mai yawa, kuma kada ku sayar da wanda ba shi hannu da wanda ke hannu.”