Buhari da Muslim: Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 03
Babi na Tamanin: Musanyar zinari da zinari bisa jinkiri: 625. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Dahhaku dan Makhlad ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba ni labari, cewa: “Lallai Abu Salih Azzayat ya ba shi labari cewa, lallai shi ya […]
Babi na Tamanin: Musanyar zinari da zinari bisa jinkiri:
625. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Dahhaku dan Makhlad ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba ni labari, cewa: “Lallai Abu Salih Azzayat ya ba shi labari cewa, lallai shi ya ji Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Musanyar zinari da zinari, dirhami da dirhami, sai na ce, masa: Lallai dan Abbas bai fadinsa (wannan hukunci), sai Abu Sa’id ya ce, “Na tambaye shi sai na ce, “Ka ji shi daga Annabi (SAW) ko ka same shi cikin littafin Allah? Ya ce, “Dukkan wannan ban ce ba, ku ne kuka fi sani game da Manzon Allah fiye da ni, amma lallai ni, Usama ya ba ni labari cewa: Lallai Annabi (SAW) ya ce, “Babu riba a musanya (canji) face idan da jinkiri.”
Babi na Tamanin da daya: Cinikin (musanya) azurfa da zinari bisa jinkiri:
626. An karbo daga Hafsu dan Umar ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Habib dan Abu Sabit ya ce, “Na ji Minhal ya ce, na tambayi Barra’u dan Azib da Zaid dan Arkam (Allah Ya yarda da su) game da musanya (canji) kowane daga cikinsu yana cewa: “Wannan ya fi kyau a kaina,” kuma dukkansu sun ce, “Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin zinari da azurfa bisa bashi.”
Babi na Tamanin da Biyu: Cinikin zinari da azurfa hannu da hannu:
627. An karbo daga Imran dan Maisarata ya ce: “Abbadu dan Awwam ya ba mu labari ya ce, Yahya dan Abu Is’hak ya ba mu labari ya ce, Abdurrahman dan Abubakarata ya ba mu labari daga Babansa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da cinikin azurfa da azurfa, da zinari da zinari face daidai da daidai (misali da misali). Kuma ya umurce mu da mu sayi zinari da azurfa yadda muka so, ko mu sayi azurfa da zinari yadda muka so.”
Babi na Tamani da Uku:
Cinikin muzabanat, shi ne sayen danyen dabino da tsoho (busasshen) dabino, ko sayen danyen inabi da tsohon inabi busasshe da cinikin ’ya’yan itacen da aka san yawan abin da za a girba. Anas ya ce, “Annabi (SAW) ya hana game da muzabanat da muhakalat (cinikin alkamar cikin kono da wanda aka sussuka.”
628. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu daga dan Shihab ya ce, Salim dan Abdullahi, daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada ku sayar da ’ya’yan itace har sai sun fara nuna. Kuma kada ku sayar da sabon dabino da tsohon dabino busasshe.” Salim ya ce Abdullahi ya ba ni labari daga Zaidu dan Sabit cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya yi rangwame bayan haka, a cikin cinikin Ara’ya (’ya’yan itace wanda aka san abin da za a samu) da danye, koda dabino, amma bai yi sauki a cikin waninsa.”
629. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin muzabanat, ma’anar muzabanat ita ce: Cinikin ’ya’yan dabino a bisa itace da tsohon dabino busasshe bisa awo. Ko cinikin zabibi danye da tsohon zabibi busasshe bisa awo.”
630. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Dauda dan Husain daga Abu Sufiyan bawan dan Abu Ahmad daga Abu Sa’idil Khudri (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin muzabanat da muhakalat, ma’anar muzabanat ita ce, cinikin tsoho (busasshe) da wanda ke bisan itace dabino.”