Buhari da Muslim: Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 04
660. An karbo daga kutaibah ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga danShihab daga Urwat daga A’ishat Allah Ya yarda da ita, ta ce; “Sa’adu danAbi Wakkas ya yi husuma da Abdu dan Zama’at a kan wani yaro (bawa). Sai Sa’ad ya ce, “Wan nan ya Manzon Allah! dandan’uwana ne Utbat danAbi Wakkas ya […]
660. An karbo daga kutaibah ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga danShihab daga Urwat daga A’ishat Allah Ya yarda da ita, ta ce; “Sa’adu danAbi Wakkas ya yi husuma da Abdu dan Zama’at a kan wani yaro (bawa). Sai Sa’ad ya ce, “Wan nan ya Manzon Allah! dandan’uwana ne Utbat danAbi Wakkas ya yi mini alkawarinsa (kyautarsa a jahiliyya) cewa, lallai shi dansa ne. Ka duba kamanninsa? Abdu dan Zama’a ya ce, “Wannan dan uwana ne, ya Manzon Allah!, an haife shi bisa shimfidar Babana daga wata baiwarsa ce.” Sai Manzon Allah (SAW) ya yi dubin kamarshi ya ga bambancin kama a fili da Utbat sai ya ce: “Na kane ya Abdu, domin daga shimfida aka sani, amma mazinaci dutse ke kansa (idan ya taba aure). Saudat diyar Zama’at ki tsare kanki daga gare shi, ba ta sake ganinshi ba har ta rasu (kamar yadda ya gabata).”
661. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga Sa’ad daga Babansa cewa; “Abdurrahman dan Aufu Allah Ya yarda da shi ya ce ga Suhaib: “Ka ji tsoron Allah kada ka jingina kanka ga wani ba babanka ba.” Sai Suhaib ya ce, “Babu abin da zai faranta mini rai ko da an ba ni tarin dukiya kaza-da- kaza, a ce na fadi haka, amma dai lallai ni, an sace ni ina yaro.”
662. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Urwat dan Zubair ya ba ni labari cewa: Hakika Hakeem danHizam ya ba shi labari cewa, lallai shi ya ce: “Ya Manzon Allah! Shin ka gani ayyukan da na kasance ina aikatawa a jahiliyya domin neman lada irin su sadar da zumunta, ‘yanta bayi, da sadaka, shin zan samu lada cikinsu? Hakeemu Allah Ya yarda da shi ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ka musulunta da dukkan ayyukan alherin da ka yi (a jahiliyya) da suka wuce.”
BABI NA dARI DA BIYU:-
Hukuncin fatun mushe kafin jemewa.
663. An karbo daga Zuhiar dan Harbu ya ce: “Yakub dan Ibrahim ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba mu labari daga Abi Salih ya ce, dan Shihab ya ba ni labari cewa: Lallai Ubaidillahi danAbdullahi ya ba shi labari cewa, lallai Abdullahi danAbbas Allah Ya yarda da su ya ba shi labari cewa: “Hakika wata rana Manzon Allah (SAW) ya shude da wata akuya matacciya, sai ya ce: “Shin ba za ku debe fatarta ba, ku yi amfani da ita ba? Suka ce, “Lallai ita, matacciya ce,” ya ce, “An haramta cin mushe ne kadai.”
BABI NA dARI DA UKU:-
Hukuncin kashe alade. Jabir ya ce, “Annabi (SAW) ya hana cinikin alade.”
664. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga dan Shihab daga dan Musayyib cewa: Lallai shi ya ji Abahuraira Allah Ya yarda da shi yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ina rantsuwa da Wanda raina yake hannunSa ya yi kusa dan Maryamu ya sauka cikinku yana mai hukunci da adalci. Zai karya kuros, ya kashe alade.Ya hana biyan jiziya (haraji) ya watsa dukiya har ya kasance babu mai karbarta.”