Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 11
636. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Musa dan Ukbata ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar daga Zaidu dan Sabit (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya yi rangwame game da cinikin Ara’ayat idan aka sayar da da ita bisa sanin […]
636. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Musa dan Ukbata ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar daga Zaidu dan Sabit (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya yi rangwame game da cinikin Ara’ayat idan aka sayar da da ita bisa sanin yawan abin da za a samu bisa awo.” Musa dan Ukbata ya ce, “Ara’ayat dabinai ne sanannu wadanda za ka zo ka saye su.”
Babi na Tamanin da Shida:
Cinikin ’ya’yan itace kafin su fara nuna. Laisu ya ce, daga Abu Zinad ya ce, Urwata dan Zubair ya kasance yana ba da labari daga Sahlu dan Abu Hasmat mutumin Madina daga kabilar Bani Harisa cewa, lallai shi ya ba shi labari daga Zaid dan Sabit (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mutane sun kasance a zamanin Manzon Allah (SAW) suna cinikin ’ya’yan itace. Idan mutanen suka girbi (debi) dabino masu shi suka zo karbar hakkinsu, sai mai sayarwa ya rika cewa, dabinona sun ruba. Ko ya ce, dabinona, cuta ya same shi, ko ya ce, kusam (cutar zubar dabino) ya kama dabinona. Su rika kawo wasu hujjoji marasa kyau. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, lokacin da husuma ta yawaita game da haka: “Ko dai a’a, kada ku sayar da su face sai ’ya’an itacen sun fara nuna.” Ya yi haka kamar mai bayar da shawari saboda yawan husumarsu.” Ya ce, “Kharijata dan Zaid dan Sabit ya ba ni labari cewa: “Lallai Zaidu dan Sabit ya kasance ba ya sayar da ’ya’ya itacen gonarsa face tauraruwa Saraya ta bayyana (lokacin zafi a Hijaz) lokacin da fatsi-fatsi (rawaya) ya bayyana da ja-ja.” Abu Abdullah (Buhari) ya ce, “Aliyu dan Bahru ya ruwaito shi.
637. An karbo daga Hakam ya ce: “Unaisat ya ba mu labari daga Zakariya’u daga Abu Zinad daga Urwat daga Sahlu daga Zaidu.
638. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin ’ya’yan itace har sai sun fara nuna, ya hana mai saye da mai sayarwa.”
639. An karbo daga dan Mukatil ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Humaid dawili ya ba mu labari daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin ’ya’yan itacen dabino har sai sun fara nuna.” Abu Abdullahi (Buhari) ya ce, “Yana nufin har sai sun yi ja.”
640. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya dan Sa’id ya ba mu labari daga Salim dan Habban ya ce, Sa’id dan Mina’u ya ba mu labari ya ce, “Na ji Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya hana a sayar da ’ya’yan itace har sai sun fara nuna., sai aka ce, “Mene ne ma’anar tushakah? Ya ce, “Sai sun fara ja ko rawaya ko an fara ci.”
Babi na Tamanin da Bakwai: Cinikin dabino kafin ya fara nuna
641. An karbo daga Aliyu dan Haisam ya ce: “Mu’allah ya ba mu labari ya ce, Hushaim ya ba mu labari ya ce, Humaid ya ce, Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) cewa: “Lallai shi ya hana game da cinikin ’ya’yan itace har sai sun fara nuna. Kuma ya hana game da ’ya’yan dabino har sai sun fara nuna,” sai aka ce, yaya ne fara nunansu? Ya ce, “Jaja ko rawaya.”
Babi na Tamanin da Takwas: Wanda ya sayar da da ’ya’yan itace kafin su fara nuna, sai cuta ya kama su, to, yana ga mai sayarwa:
642. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Humaid daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin ’ya’yan itace har sai sun fara nuna. Sai aka ce, masa: Yaya fara nunansu? Ya ce “Idan sun yi ja.” Manzon Allah (SAW) ya ce: “Shin ka gani idan Allah Ya hana mata albarkar ’ya’yanta, yaya za ka karbi dukiyar dan uwanka?” Laisu ya ce, Yunus ya ba ni labari daga dan Shihab ya ce, “Da a ce, wani mutum zai sayi ’ya’yan itace kafin su fara nuna, sa’an nan lalura ta samu ’ya’yan, to hasara ta mai shi ne.” Ya ce, Salim dan Abdullahi ya ba ni labari daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kada ku sayar da ’ya’yan dabino (itace) har sai sun fara nuna, kuma kada ku sayar da danyen dabino da tsoho, busasshe.”