Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 21
Babi na Biyar: Mai lamuni bisa salafi (biyan kudin kaya kafin karba): 692. An karbo daga Muhammad dan Sallam ya ce: “Ya’ala ya ba mu labari, ya ce, A’amashi ya ba mu labari, daga Ibrahim daga As’wad daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya sayi wani abinci daga wani […]
Babi na Biyar: Mai lamuni bisa salafi (biyan kudin kaya kafin karba):
692. An karbo daga Muhammad dan Sallam ya ce: “Ya’ala ya ba mu labari, ya ce, A’amashi ya ba mu labari, daga Ibrahim daga As’wad daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya sayi wani abinci daga wani Bayahude bisa bashi, ya yi masa jinginar wata taguwarsa (sulken yaki) na bakin karfe.”
Babi na Shida: Jingina a cikin Salami:
693. An karbo daga Muhammad dan Mahbub ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari, ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce, “Mun yi hira a wajen Ibrahim game da jingina a cikin salami, sai ya ce: “Aswad ya ba ni labari daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Hakika Annabi (SAW) ya sayi abinci daga wajen wani Bayahude zuwa wani lokaci sananne, sai ya yi jinginar taguwarsa (sulken yaki) na bakin karfe.”
Babi na Bakwai:
Salami zuwa ga lokaci sananne. Da shi dan Abbas da Abu Sa’id da Aswad da Alhassan suka kafa hujja. dan Umar ya ce, “Babu laifi a cikin abincin da aka san yawansa da farashinsa sananne zuwa lokaci sananne, matukar dai ba shuka ba ne wadda ba ta fara nuna ba.”:
694. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga dan Abu Najeeh daga Abdullahi dan Kasir daga Abu Minhal daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya isa Madina ya iske su suna salafi (biyan kudi kafin karba) a cikin ‘ya’yan itace shekara biyu ko uku, sai ya ce: “Ku yi salafi a cikin ’ya’yan itace a bisa awo sananne, kuma bisa ajali (karba) sananne.” Abdullahi dan Walid ya ce, Sufiyan ya ba mu labari, ya ce, dan Abu Najeeh ya ba mu labari, ya ce: “A cikin awo sananne, kuma lokacin bayarwa sananne.”
695. An karbo daga Muhammad dan Mudatil ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Sufiyan ya ba mu labari daga Sulaiman Shaibani daga Muhammad dan Abu Mujalid ya ce, “Abu Burdata da Abdullahi dan Shaddad sun aike ni zuwa ga Abdurrahman dan Abza da Abdullahi dan Abu Aufa, na tambaye su game da salafi. Sai suka ce, “Mun kasance muna samun ganimomi tare da Manzon Allah (SAW) sai ya kasance wasu talakawa-kauyawa daga kauyawan mutanen Sham (Siriya) sai mu rika yin salafi da su a cikin alkama da sha’ir da zabibi zuwa lokacin (karba) sananne.” Ya ce, “Na ce, “Shin suna da gonaki ne, ko ba su da da gonaki? Sai suka ce, “Ba mu tambayarsu game da haka.”