Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 22
676. An karbo daga Abdulgaffar dan Dawud ya ce: “Yakub dan Abdurrahman ya ba mu labari daga Amru dan Abu Amru daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya isa Khaibara, lokacin da Allah Ya ba da nasara a kan manyan masu tsaro. Sai aka ba shi labarin kyan […]
676. An karbo daga Abdulgaffar dan Dawud ya ce: “Yakub dan Abdurrahman ya ba mu labari daga Amru dan Abu Amru daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya isa Khaibara, lokacin da Allah Ya ba da nasara a kan manyan masu tsaro. Sai aka ba shi labarin kyan Safiyya ’yar Huyayyi dan Akhdab. Kuma lallai an ka she mijinta lokacin tana an gwanci. Manzon Allah (SAW) ya zabe ta wa kansa, ya fita tare da ita, har sai da muka isa Saddar-Rauha’u lokacin da hailarta ya dauke. Sai (Annabi) ya sadu da ita, sa’an nan aka samar da wani abinci domin walima bisa karamar shimfida. Sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya ce mini: “Yi izini ga jama’ar da ke gefenka, sai haka ta kasance walimar Manzon Allah (SAW) bisa aurensa da Safiyya. Sa’an nan muka fita zuwa Madina, ya ce, “Sai na ga Manzon Allah (SAW) yana lullube ta da alkyabbarsa lokacin tana bayansa. Sa’an nan ya zauna bisa gafen rakuminsa ya bar Safiyya ta dora kafarta bisa gwiwarsa domin ta hau rakumin.”
Babi na dari da Goma Sha Biyu: Cinikin mushe da gumaka:
677. An karbo daga kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Zaid dan Abu Habib daga Adda’u dan Abu Rabah daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai shi ya ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Lokacin yana Makka a Shekarar Budi (cin Makka), bisa cewa: “Hakika Allah da ManzonSa sun haramta cinikin giya da mushe da alade da gumaka. Sai aka ce ya Manzon Allah! Shin ka gani idan aka yi amfani da kitsen fa? Domin ana turara allon jiragen ruwa kuma ana turara fatu da shi, kuma mutane na (abin) kunna fitilu da shi.” Sai (Annabi) ya ce, “A’a, haramun ne,” sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya ce, game da haka: “Allah Ya la’ani Yahudawa, domin lallai lokacin da Allah Ya haramta musu kitse, sai suka dauka suka sayar suka ci kudinsa.” Abu Asim ya ce, Abdulhamid ya ba mu labari ya ce, Yazid ya ba mu labari ya ce, Adda’u ya rubuta zuwa gare ni cewa: “Na ji Jabir Allah (Ya yarda da shi) ya ce ya ji daga Annabi (SAW).”
Babi na dari da Goma Sha Uku: Cin kudin kare:
678. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Abubakar dan Abdurrahman daga Abu Mas’ud mutumin Madina (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cin kudin kare da sadakin (kudin) zina da kudin da aka samu ta hanyar bokanci.”
679. An karbo daga Hajjaju dan Minhal ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari ya ce, Aunu dan Abu Juhaifa ya ba ni labari ya ce, “Na ga Babana ya sayi wani bawa mai yin kaho, sai ya yi umurni da karya abin yin kahon. Sai na tambaye shi game da haka, ya ce: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya hana amfani da kudin jini da kudin kare. Kuma ya hana amfanin da kudin da baiwa ta samo ta hanyar zina. Kuma ya la’anci mace mai kara gashi da wanda ake mata karin gashi, kuma ya la’anci mai cin riba da mai wakiltawa. Kuma ya la’anci mai yin hoto.”