Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 23

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai. Littafin Salami (Cinikin kayan da aka biya kudin lokaci guda amma za a kawo kayan nan gaba). Babi na Farko: Salami (da salafi kusan ma’anarsu daya: Biyan kudin kaya da aka yi ciniki kafin kawo kaya) bisa kayan awo wanda aka sani: 680. An karbo daga Amru dan […]

Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 23
Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 23

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.

Littafin Salami (Cinikin kayan da aka biya kudin lokaci guda amma za a kawo kayan nan gaba).

Babi na Farko: Salami (da salafi kusan ma’anarsu daya: Biyan kudin kaya da aka yi ciniki kafin kawo kaya) bisa kayan awo wanda aka sani:

680. An karbo daga Amru dan Zurarat ya ce: “Isma’il dan Ulayyat ya ba mu labari ya ce, dan Abu Najih ya ba mu labari daga Abdullahi dan Kasir daga Abu Minhal daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya iso Madina lokacin mutane suna bada sautun salafi a cikin ’ya’yan itace bisa shekara daya ko biyu. Ko ya ce, shekara biyu bisa shekara uku – Isma’ilu ya yi shakka- sai (Annabi) ya ce; “Wanda zai bada salafi bisa ’ya’yan itace, to ya yi bisa mudu sananne, kuma bisa awo sananne.” (Salami ko salafi duk kusan ma’anarsu daya shi ne: Biyan kudin kayan da aka yi ciniki kafin kawo kayan sananne).
681. An karbo daga Muhammad ya ce: “Isma’ilu ya ba mu labari daga dan Abu Najih da wananan hukunci cewa: “Bisa awo sananne.”

Babi na Biyu: Salami bisa awo sananne:
682. An karbo daga Sadakatu ya ce: “dan Uyainata ya ba mu labari ya ce, dan Abu Najih ya ba mu labari daga Abdullahi dan Kasir daga Abu Minhal daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Annabi (SAW) ya iso Madina lokacin suna yin salami (cinikin) ’ya’yan dabino a karba cikin shekara biyu ko uku. Sai ya ce, “Wanda zai yi cinikin salami a cikin kowane abu, to lallai ya kasance bisa awo sananne da nauyi sananne zuwa ajali sananne.”

683. An karbo daga Aliyu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, dan Najih ya ce, (Annabi SAW) ya ce, “Lallai wanda zai yi salami, to ya yi shi bisa awo sananne, zuwa ajali sananne.”

684. An karbo daga kutaiba ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga dan Abu Najih daga Abdullahi dan Kasir daga Abu Minhal ya ce: “Na ji dan Abbas (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Annabi (SAW) ya isa Madina (ya iske mutane na salami), sai ya ce: “Lallai ya kasance bisa ma’auni sananne, kuma zuwa ajali sananne.”

685. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga dan Abu Mujahid – Hawwala Sanad- ya ce, Yahya ya ba mu labari ya ce, Waki’u ya ba mu labari daga Shu’abah daga Muhammad dan Abu Mujahid ya ce, Hafsu dan Umar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Muhammad ko Abdullahi dan Abu Mujahid ya ba mu labari ya ce, “Abdullahi dan Shaddad ya yi sabani da Abu Burdata a cikin salafi, sai suka aika ni zuwa ga dan Abu Aufa (Allah Ya yarda da shi) na tambaye shi sai ya ce: “Lallai mu, mun kasance muna salafi (wannan ciniki) a zamanin Manzon Allah (SAW) da zamanin Abubakar da Umar a cikin alkama da sha’iri da zabibi da dabino.” Sai na tambayi dan Abza sai ya fada mini misalinsa.