Buhari da Muslim: Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 26
649. An karbo daga kutaiba ya ce: “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya hana game da cinikin ’ya’yan dabino danye da tsoho busasshe har sun fara nunna.” Sai muka ce, wa Anas mece ce nunar su? Ya ce, “Idan ya […]
649. An karbo daga kutaiba ya ce: “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya hana game da cinikin ’ya’yan dabino danye da tsoho busasshe har sun fara nunna.” Sai muka ce, wa Anas mece ce nunar su? Ya ce, “Idan ya fara ja ko rawaya. Shin ka gani idan Allah Ya hana ’ya’yan dabino, to me zai halatta masa cin dukiyar dan uwansa?”
BABI NA CASA’IN DA BIYAR:-
Cinikin Jumar (hudar dabino) da cinsa.
650. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Hisham dan Abdul Malik ya ba mu labari, ya ce, Abu Awanat ya ba mu labari, daga Abi Bishiru daga Mujahid daga dan Umar Allah Ya yarda da su, ya ce: “Na kasance tare da Annabi (SAW) lokacin yana cin Jumar (hudar dabino). Sa ya ce, “Daga cikin itatuwa da akwai wata itaciya tana kama da mutum mumini, mece ce ita? Sai na yi nufin in ce, ita ce dabino, sai na ga nine karamin cikinsu (sahabbai) ya ce, “Itaciyar dabino ce.”
BABI NA CASA’IN DA SHIDA:-
Wanda ya ke ijarah (gudanar) da al’amarin mutane birane bisa ga abubuwan da suka sani a tsakaninsu acikin ciniki da jinga, da awon mudu da na sikeli (nauyi) tare da bin manufarsu bisa niyyarsu da mazhabinsu shararriya. Shuraih ya ce, ga masu saka: “sunnarku na a tsakaninku.” Abdul Wahhab ya ce, daga Ayyub daga Muhammad cewa: “Babu laifi ga sayen abu a farashin goma, ya sayar goma sha daya, ya samu riban abin da zai ci.” Annabi (SAW) ya ce, ga Hind (matar Abu Sufiyan) ki debi abin da zai isheki da ‘ya’yan ki bisa kyautatawa.” Allah Madaukaki Ya ce, “Wanda ya kasance matalauci ne, to ya ci (daga dukiyar maraya) bisa kyautatawa…(4:6).” Alhassan ya yi hayan jaki daga wurin Abdullahi dn Mirdasi sai ya ce; “A nawa? Ya ce, “Da nika biyu, kamar daya cikin shida [1/6] na dirhami). Sai Alhassan ya hau ya tafi, sa’an nan ya sake zuwa ya ce, “Ba ni hayar jakin ya haushi ba tare da wani sharadi ba, sai ya aika masa da rabin dirhami (saboda ba su sanya sharadin abin da zai biya ba).
651. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce; “Malik ya ba mu labari daga Humaid dawili daga Anas dan Malik Allah Ya yarda da shi ya ce: “Manzon Allah (SAW) da Abu daibata ya yi masa kaho, sai Manzon Allah (SAW) ya umurta da a auna masa sa’i daya na dabino, kuma ya umurci (shugabansa) da su saukaka masa harajinsa (Abu daibata bawa ne).”
652. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Hisham daga Urwat daga A’ishat Allah Ya yarda da ita, ta ce: “Hindu uwar Mu’awiyat ta ce, wa Manzon Allah (SAW) lallai Abu Sufiyan mutum ne marowaci (mai mako), shin akwai laifi akaina idan na diba daga dukiyarsa a boye? (Annabi) ya ce, “Ki debi abin da zai isheki da ‘ya’yanki, amma bisa kyautatawa (banda barna).”
653. An karbo daga Is’hak ya ce: “Numair ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari ya ce, Muhammad ya ba ni labari ya ce, “Na ji Usman dan Farkad ya ce, na ji Hisham dan Urwat yana ba da labari daga Babansa cewa: Lallai shi ya ji A’ishat Allah Ya yarda da ita, tana karanta: “Wanda ya kasance mawadaci to ya kame daga (dukiyar maraya), wanda ya kasance kuwa matalauci to ya ci bisa kyautatawa….(4:6).” Wannan aya ta sauka ne bisa ga wanda ke shugabancin maraya, wanda ke lura da shi da gyara (aiki) cikin dukiyarsa. Idan ya kasance matalauci sai ya ci bisa kyautatawa.”
BABI NA CASA’IN DA BAKWAI:-
Cinikin abokin tarayya (gamayya) daga wasu abokan tarayyansa zuwa wasu ta wurin mutum daya daga cikinsu (abokan tarayya).
654. An karbo daga Mahmud ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Abi Salmat daga Jabir Allah Ya yarda da shi cewa: “Manzon Allah (SAW) ya sanya kamun shufu’a (ciniki makwabci) ga duk dukiyar da ba’a raba ba. Idan iyakoki ta fada ko hanyoyin suka juya (raba) to, babu shufu’a.”