Buhari da Muslim…..Fassarar Sheikh Is’haq Yunus Almashgool, Bauchi

Babi na Tamanin da Tara: Sayen abinci zuwa ajali (wani lokaci):643. An karbo daga Umar dan Hafsu dan Ghiyas ya ce: “Babana ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce, na ambata ga Ibrahim game da hukuncin jingina sai ya ce, “Babu laifi da shi.” Sa’an nan ya ce, “Ya […]

Buhari da Muslim…..Fassarar Sheikh Is’haq Yunus Almashgool, Bauchi
Buhari da Muslim…..Fassarar Sheikh Is’haq Yunus Almashgool, Bauchi

Babi na Tamanin da Tara: Sayen abinci zuwa ajali (wani lokaci):
643. An karbo daga Umar dan Hafsu dan Ghiyas ya ce: “Babana ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce, na ambata ga Ibrahim game da hukuncin jingina sai ya ce, “Babu laifi da shi.” Sa’an nan ya ce, “Ya ba mu labari daga Aswad daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) cewa; “Lallai Annabi (SAW) ya sayi abinci daga wajen wani Bayahude zuwa ajali (wani lokaci) sai ya yi masa jinginar taguwarsa na sulke.”

Babi na Casa’in: Idan mutum ya yi nufin sayen dabino mai kyau da dabino tsoho bisa fifitawa:
644. An karbo daga kutaiba ya ce: “Daga Malik daga Abdul Hamid dan Sahlu dan Abdurrahman daga Sa’id dan Musayyib daga Abu Sa’idul Kuhudri daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya taba sanya wani mutum aiki a Khaibara sai ya zo da dabino mai kyau. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Dukkan dabinon Khaibara haka suke masu kyau? Ya ce, “A’a, wallahi ya Manzon Allah! Lallai mu, muna karbar sa’i daga wannan (mai kyau) bisa sa’i biyu (wadda ba ta kai kyan wannan), kuma muna karbar sa’i biyu bisa sa’i uku.  Sai manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada ka sake aikata haka, ka sayar da mara kyau bisa kudi. Sai ka sayo mai kyau da wannan kudin.”

Babi na Casa’in da daya:
Wanda ya sayar da dabino da aka yi mata kilili ko bayar da hayar gona wadda aka shuka. Abu Abdullahi (Buhari) ya ce, “Ibrahim ya fada ya ce min, Hisham ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba mu labari ya ce, “Na ji dan Abu Mulaika yana ba da labari daga Nafi’u bawan dan Umar cewa: “Duk wata dabino da aka sayar bayan an yi mata kilili ba a ambaton ’ya’ya ga mai saye face ga wanda ya yi mata kilili, ya ce, haka hukuncin bawa da mai girbi, Nafi’u ya ambaci wadannan uku.”
645. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) cewa; “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wanda ya sayi dabino wadda aka yi mata kilili, to ’ya’yanta na mai sayarwa ne face sai mai saye ya yi da sharadin haka kuma mai sayarwa ya yarda.”

Babi na Casa’in da Biyu: Sayar da shuka bisa abinci da aka auna:
646. An karbo daga kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin ’ya’yan itacen gonarsa bisa tsohon dabino na awo. Ko kuma sayar da danyen inabi da tsoho busasshe bisa awo. Ko kuma sayar da shuka bisa abincin awo, ya hana game da wadannan dukkansu.”

Babi na Casa’in da Uku: Cinikin dabino dukkansa bisa asalinsa:
647. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Duk mutumin da ya sayi itacen dabino sa’an nan ya sayar da tushensa to ’ya’yan na ga wanda ya yi mata kilili ne. Sai idan mai saye ya yi sharadin haka kuma mai sayarwa ya yarda.”

Babi na Casa’in da Hudu: Cinikin kayan marmari kamar ganye da kayan miya:
648. An karbo daga Is’hak dan Wahab ya ce; “Umar dan Yunus ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba ni labari ya ce, “Is’hak danAbu dalha mutumin Madina daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi): Lallai shi ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya hana game da muhakala (sayar da alkama mara kyau da mai kyau) da mulamasa (shafar tufafi ban da budewa) da munabaza (jifar tufafi kafin budawa) da muzabana (inabi danye da tsoho).”