Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’haq Yunus Almashgool, Bauchi 22

Babi na Uku: Salami zuwa ga abin da babu asalinsa ga mutum: 686. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Shaibanu ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Abu Mujalid ya ba mu labari ya ce, “Abdullahi dan Shaddadu (da) Abu Burdat sun aike ni zuwa […]

Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’haq Yunus Almashgool, Bauchi 22
Buhari da Muslim Fassarar Sheikh Is’haq Yunus Almashgool, Bauchi 22

Babi na Uku: Salami zuwa ga abin da babu asalinsa ga mutum:

686. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Shaibanu ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Abu Mujalid ya ba mu labari ya ce, “Abdullahi dan Shaddadu (da) Abu Burdat sun aike ni zuwa ga Abu Aufa (Allah Ya yarda da su), sai suka ce, “Ka tambaye shi shin ko sahabban Annabi (SAW) sun kasance suna cinikin salafi a zamanin Annabi (SAW) a game da alkama? Sai Abdullahi ya ce, “Mun kasance muna yin salafi (biyan kudin kaya kafin kawo shi) da kauyawan mutanen Sham (Siriya) a cikin cinikin alkama da sha’iri da zabibi, a bisa awo sananne, zuwa ajali (lokacin kawowa) sananne.”Sai na ce, “Shin za a biya kudin ga masu shi (hatsin) kafin su kawo kayan nan gaba (suna da gonakin ne a kasarsu)? (Abdullahi) ya ce, “Ba mu kasance muna tambayarsu ba game da haka.” Sa’an nan suka sake aike na zuwa ga Abdurrahman dan Abzah na tambaye shi, sai ya ce: “Sahabban Annabi (SAW) sun kasance suna salafi (biyan kudin kaya kafin a kawo) a zamanin Annabi (SAW) ba mu tambayarsu, shin ko suna da hatsin ko babu?”

687. An karbo daga Is’hak ya ce: “Khalid dan Abdullahi ya ba mu labari daga Shaibanu daga Muhammad dan Mujalid da wannan, ya ce: “Mukan yi salafi da su a cikin alkama da sha’iri.” Abdullahi dan Walid ya ce, daga Sufiyan ya ce, Shaibanu ya ba mu labari ya ce, “Da zabibi.”

688. An karbo daga kutaiba ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Shaiban ya ce, “Alkama da sha’iri da zabibi.”

689. An karbo daga Adamu ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Amru ya ba mu labari ya ce, “Na ji Abu Bakhtariyu da’iyu ya ce, “Na tambayi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), game da salami (biyan kudin kayan kafin a kawo) a cikin dabino, sai ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da cinikin dabino har sai an fara ci daga gare shi, ko kuma har sai an auna, sai wani mutum ya ce: “A auna bisa itacen dabino? Sai wani mutum kuma ya ce masa: “Har sai an san yawan abin da za a samu (diba).” Mu’azu ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga Amru ya ce, Abu Bakhtariyu ya ce, Na ji dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Annabi (SAW) ya hana misalinsa.”

Babi na Hudu: Salami a cikin dabino:

690. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Amru daga Abu Bakhtariyu ya ce: “Na tambayi dan Umar (Allah Ya yarda da su), game da salami a cikin dabino, sai ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da cinikin dabino har sai ya fara nuna, kuma ya hana cinikn azurfa bisa jinikiri (bashi) da (zinari) wanda ke hannu.” Ya ce, “Na tambayi dan Abbas game da salami a cikin dabino sai ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da cinikin dabino har sai an fara ci, ko ya fara ci, ko ya ce, har sai an san yawan abin da za a diba.”

691. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari, kuma Shu’abah ya ba mu labari daga Amru daga Abu Bakhtari ya ce: “Na tambayi dan Umar (Allah Ya yarda da su), game da salamin dabino, sai ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da cinikin ’ya’yan itace face sun fara nuna. Kuma ya hana game da cinikin azurfa da zinari bisa bashi.” Kuma na tambayi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), sai ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da cinikin dabino har sai (mai shi) ya fara ci, ko ya ce, face an fara ci, ko sai an auna.” Na ce, “Yaya za a auna, bisa itacen dabino? Sai wani mutum da ke tare da shi ya ce, “Sai an san yawan abin da za a diba.”