Buhari da muslim(9)

Babi na Goma: Shin mutum zai iya daukar tsintuwa don kada ya bar ta ta tozarta har wanda bai cancanta ba ya kama ta?:156. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Salmata dan Kuhail ya ce, “Na ji Suwaid dan Ghafalat ya ce, “Na kasance tare da Salman […]

Buhari da muslim(9)
Buhari da muslim(9)

Babi na Goma: Shin mutum zai iya daukar tsintuwa don kada ya bar ta ta tozarta har wanda bai cancanta ba ya kama ta?:
156. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Salmata dan Kuhail ya ce, “Na ji Suwaid dan Ghafalat ya ce, “Na kasance tare da Salman dan Rabi’ata da Zaid dan Suhan a wani yaki. Sai na tsinci wata tsumagiya (bulala), sai ya ce mini jefar da ita. Na ce, a’a har sai na iske mai ita idan ba haka sai in yi amfani da ita. Lokacin da muka komo sai muka tafi Hajji muka bi ta Madina sai na tambayi Ubayyu dan Ka’ab (Allah Ya yarda da shi), sai ya ce: “Na tsinci wata jaka da kamar dinari dari a cikinta a zamanin Annabi (SAW) sai na tafi da ita zuwa ga Annabi (SAW) sai ya ce: “Ka sanar da ita shekara daya. Sai na yi shelenta shekara daya. Sa’an nan na tafi zuwa gare shi ya ce: “Ka sake sanar da ita kamar shekara daya. Sai na sanar da ita shekara daya. Sa’an nan na tafi gare shi sai ya ce: “Ka sake sanar da ita shekara daya. Na sanar da ita shekara daya. Sa’an nan na tafi gare shi a kashi ta hudu ya ce: “Ka sanar da yawan adadinta (kimarta) da madaurin jakar da ita jakar. Idan mai ita ya zo shi ke nan, idan bai zo ba ka yi amfani da ita.”
157. An karbo daga Abdan ya ce: “Babana ya ba ni labari daga Shu’aba daga Salmata da kamar wannan ya ce, “Sai na hadu da shi bayan haka a Makka, ya ce: “Ban sani ba shin shekara uku ne ya sanar ko kuwa shekara daya?”
Babi na Goma Sha daya: Wanda ya yi shelar tsintuwa amma bai kai ta ga shugaba ba:
158. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Rabai’ata daga Yazid dan Munab’is daga Zaid dan Khalid (Allah Ya yarda da shi) cewa: Hakika wani Balaraben kauye ya zo ya tambayi Annabi (SAW) game da tsintuwa. (Annabi SAW) ya ce, “Ka sanar da ita shekara daya, idan mai ita ya zo ya ba ka labarin abin da ke cikinta (jakar) da igiyar da aka daure ta, to ka ba shi. Idan kuwa bai zo ba ka yi amfani da ita, sai ya tambaye shi game da bataccen rakumi sai fuskarsa ta yi ja (baci) ya ce: “Me ya hada ka da shi, yana da abin shansa da kofatonsa yana tanadin ruwa yana cin itace, ka bar shi har mai shi ya iske shi. Sai ya tambaye shi game da batacciyar tunkiya. Ya ce, “Taka ce, ko dan uwanka (mai ita) ko ta kerkeci.”
Babi na Goma Sha Biyu: Kamar abin da ya gabata:
159. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Nadar ya ba mu labari ya ce, Isra’il ya ba mu labari daga Abu Is’hak ya ce, Barra’u ya ba ni labari daga Abubakar (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Wata rana na hadu da wani mai kiwon tumaki yana kora tumakinsa, sai na ce, daga wata kabila kake? Ya ce, “Daga kabilar kuraishawa, sai ya ambaci mai shi na fahimce shi. Na ce, “Shin cikin tumakinka akwai mai nono? Ya ce, “Na’am.” Na ce, “Shin za ka tatsa mini nonon? Ya ce, “Na’am.” Sai na umarce shi da ya daure tunkiya daya daga cikin tumakinsa. Sa’an nan na umarce shi da ya karkade kura daga hantsar tunkiyar. Kuma na umarce shi ya karkade kurar daga tafukansa biyu. Sai ya ce, “Yi kamar haka, sai ya dora daya tafin hannunsa bisa dayan ya rika tatsar nono daga tunkiyar alhali ni kuma na sanya wa Manzon Allah (SAW) madarar a wata tukunya (gora) wadda bakinta da wani kyalle na dora (zuba) bisa nonon har ya yi sanyi daga karkashinsa. Sai na tafi zuwa ga Annabi (SAW) na ce: “Ka sha ya Manzon Allah! Sai ya sha har sai da na yi farin ciki.”