Buhari da Muslim(93)

Sai na fita na tafi zuwa ga mumbari alhali wasu jama’a na zaune a gefensa wasu na ta kuka. Sai na zauna tare da su na dan lokaci. Sa’an nan abin da ke raina na bacin rai ya rinjaye ni, na tafi zuwa ga dakinsa na bisa wanda ke cikinta, sai na ce wa yaronsa […]

Buhari da Muslim(93)
Buhari da Muslim(93)

Sai na fita na tafi zuwa ga mumbari alhali wasu jama’a na zaune a gefensa wasu na ta kuka. Sai na zauna tare da su na dan lokaci. Sa’an nan abin da ke raina na bacin rai ya rinjaye ni, na tafi zuwa ga dakinsa na bisa wanda ke cikinta, sai na ce wa yaronsa baki. “Ka nemi izini wa Umar,” ya shiga ya yi wa Annabi (SAW) magana sa’an nan ya fito ya ce: “Na ambace ka wurinsa ya yi shiru.” Sai na koma zuwa jama’ar can da suka wurin mumbari na zauna. Sai abin da ya same ni na bakin ciki ya rinjaye ni, na tafi yaron ya ambata misalinsa, na komo na zauna tare da jama’ar da ke wurin mumbari, sa’an nan abin da ya same na bakin ciki ya rinjaye ni, na tafi ga yaron nan na ce, “Ka nemi izini wa Umar, sai ya ambaci kamar haka (maganar farko). Lokacin da na juya sai ga yaron yana kira na, ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya yi maka izini, sai na shiga gare shi. Sai ga shi (Annabi) yana jingine (kwance) bisa turbayar tabarma babu komai tsakaninsa daga shimfida. Har jikinsa ya fitar da alamar yashi (tsakuwa) a gefen jikinsa yana jingine bisa wani matashi na fata wanda aka cika da kaba. Sai na yi masa sallama, sa’an nan na ce, lokacin ina tsaye: “Shin ka saki matanka ne? Sai ya daukaka ganinsa gare ni ya ce, “A’a, sa’an nan na ce, “Lokacin ina tsaye: “Shin za ka saurari hirata, ya Manzon Allah! Mu, jama’ar kuraishawa mun kasance muna da rinjaye bisa ga mata, amma lokacin da muka iso ga mutane da matansu ke da rinjaye a kansu, ya fadi labarinsa sai Annabi (SAW) ya yi murmushi. Sa’an nan na ce: “Da dai ka gan ni lokacin da na shiga wajen Hafsa na ce, mata: Kada don makwabciyarki wadda ta fi kyau ta rude ki alhali ita ce Manzon Allah (SAW) ya fi so, sai (Annabi) ya yi murmushi kashi na biyu. Sai na zauna lokacin da na gan shi ya yi murmushi, sa’an nan na daukaka ganina cikin dakinsa ina rantsuwa da Allah ban ga wani abu cikinsa ba wanda ke dauke gani (daraja) face fatu guda uku. Na ce: “Ka roki Allah, Ya yalwata wa al’ummarka. Domin lallai Farisawa da Romawa an yalwata musu an ba su duniya duk da yake ba su bauta wa Allah.”
Lokacin (Annabi) ya kasance na jingine sai ya ce: “Shin kana cikin shakka ne dan Khaddab? Ai wadancan mutane ne wadanda aka gaggauta (saka) musu da kyawawan abubuwa a cikin rayuwar duniya.” Sai na ce, “Ya Manzon Allah! Ka gafarta mini, sai Annabi (SAW) ya kebance saboda wannan magana lokacin da Hafsa ta watsa shi zuwa ga A’isha, don kuwa haka ya kasance ya ce: “Ni ba mai shiga ba ne, gare su har wata daya saboda tsananin bacin ransa a gare su lokacin da Allah Ya zarge shi. Lokacin da kwanaki ashirin da tara suka shude sai ya shiga ga A’isha ya fara da ita, sai A’isha ta ce masa: Ai ka yi rantsuwa ba za ka shigo ba gare mu har wata daya, yau kuma mun wayi garin yinin ashirin da tara ne, na lasafce ta iyakar lissafi. Sai Annabi (SAW) ya ce, “Wata kwanaki ashirin da tara ne, kuma wannan wata ya kasance ashirin da tara.” A’isha ta ce, “Ayar ba da zabi ta sauka ya fara da ni farkon macen da ya ce: “Lallai ni, mai yi miki wa’azi ne da wani al’amari kuma bai dace ki yi gaggawar yanke hukunci ba har sai kin nemi shawarwarin iyayenki biyu.” Ta ce, “Hakika na sani iyayena ba za su kasance daga masu umartata da rabuwa da kai ba.” Sa’an nan ya ce, “Allah Ya ce, “Ya kai wannan Annabi! Ka fadi wa matanka…” har zuwa karshen maganar. (k:33:28). . Na ce, “Shin cikin wannan ne, har sai na nemi shawarwariin iyayena? Lallai ni, ina son Allah da ManzonSa da Ranar karshe. Sa’an nan ya bayar da wannan zabi ga sauran matansa, sai suka fadi misalin abin da A’isha ta fadi.”