Buhari da Muslim(99)

188. An karbo daga Yahya dan Zubair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab ya ce, Ubaidullahi dan Abdullahi dan Abu Sauri daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Ban gushe ba ina kwadayin in tambayi Umar (Allah Ya yarda da shi) game da matan nan […]

Buhari da Muslim(99)
Buhari da Muslim(99)

188. An karbo daga Yahya dan Zubair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab ya ce, Ubaidullahi dan Abdullahi dan Abu Sauri daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Ban gushe ba ina kwadayin in tambayi Umar (Allah Ya yarda da shi) game da matan nan biyu daga matan Annabi (SAW) wadanda Allah Ya yi magana game da su cewa: “In kun tuba zuwa ga Allah, hakika zukatanku sun karkata… (k:66:4).” Sai wata shekara na yi aikin Hajji tare da shi, sai ya tsaya ya sauka bisa hanya don biyan bukatarsa (na bayi), sai na sauka tare da shi da wata butar ruwa, lokacin da ya biya bukatarsa ya zo, sai na rika zuba masa ruwa a hannunsa yana alwala sai na ce: “Ya Sarkin Muminai! Wasu mata biyu ne daga matan Annabi (SAW) wadanda Allah Madaukaki Ya saukar da cewa: “In har kun tuba, to lallai zukatanku sun karkata…” (k:66:4).” Sai (Umar) ya ce, “Ya abin mamaki na da kai dan Abbas! A’isha ce da Hafsa. Sa’an nan Umar ya ci gaba da ba da labarin hadisinsa ya ce: “Lallai ni, na kasance da wani abokina mutumin Madina a cikin kabilar Umayya dan Zaid yana daga madaukakiyar Madina. Mun kasance muna wakiltar juna wajen wahayin abin da ake saukarwa ga Annabi (SAW), yakan wakilce ni wuni daya, ni kuma na wakilce shi wuni daya. Idan na wakilce shi sai in zo masa da labarin abin da ya faru a wannan wuni da waninsa. Idan ya wakilce ni yakan aika mini misalin haka. (Umar) ya ce, “Mu jama’ar kuraishawa mun kasance muna da rinjaye ga mata, amma lokacin da muka gabata (iso) Madina sai muka iske su (da matansu) wasu mutane ne wadanda matansu ke da rinjaye a kansu. Sai matanmu suka rika koyi da dabi’un matan mutanen Madina. Wata rana sai na yi wa matata tsawa sai ta mayar mini da kamar haka. Sai na yi bakin cikin mayar mini tsawar da na yi mata, sai ta ce, “Don me ya sa kake bakin ciki don na rama abin da ka yi mini? Ina rantsuwa da Allah, lallai matan Annabi (SAW) suna amsa masa, har ta kaurace (ta bata da shi) masa wuni daya da dare, sai haka ya firgita ni na ce: “Wadda duk ta aikata haka daga cikinsu hakika ta girmama laifi, ta kuwa tabe. Sai na tara tufafina, na shiga ga Hafsa na ce, “Hafsa shin dayarku tana fusatar da (bata wa) Manzon Allah (SAW) rai wuni guda har zuwa dare? Sai ta ce, “Na’am, sai na ce, “Ta tabe ta yi hasara, shin dayanku za ta amince Manzon Allah (SAW) ya yi fushi da ita har ta halaka? Kada ki yawaita haka ga Manzon Allah (SAW) kuma kada ki rika amsa masa (da bacin rai) cikin komai kuma ka da ki kaurace masa. Ki rika tambaya ta duk abin da ya bayyana miki. Kuma kada makwabciyarki (karama) wadda ta fiki haske (kyau) ta rude ki. Kuma ita ce wadda Manzon Allah (SAW) ya fi so, yana nufin A’isha.
Ana cikin haka muna hirar cewa: kabilar Gassan tana mugun shiri don yakinmu, sai abokina ya kasance a ranar wakilcinsa sai ya komo da yammaci ya buga kofar dakina bugu mai tsanani. Ya ce, “Shin Umar yana barci ne? Sai na firgita na fito zuwa gare shi ya ce, “Wani al’amari mai girma ya faru.” Na ce, “Mene ne shi? Shin kabilar Gassan sun zo ne? ya ce, “A’a, ya fi shi girma da tsawo, Manzon Allah (SAW) ya sake matansa.” Sai Umar ya ce: “Lallai Hafsa ta tabe ta yi hasara, na kasance ina tsammanin kusantar faruwar wannan, sai na tara tufafina tafi na yi Sallah fajiri tare da Annabi (SAW) na shiga wurin zamansa na bisa wanda ya tare wurinta. Na shiga ga Hafsa sai na iske ta tana kuka. Na ce, “Me ya sanya ki kuka? Shin ban kasance ina hana ki ba? Shin Manzon Allah (SAW) ya sake ku ne? Ta ce, “Ban sani ba.”