Buhari da shugabannin Afirka sama da 20 sun bude taron TICAD 7 a Japan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da sama da shugabannin kasashen Afirka 20 ne a yau suka bude taron kasa da kasa kan bunkasa nahiyar Afirka karo na bakwai, da ake yi wa take da TICAD7 da yake gudana a birnin Tokyo. An dai bude taron ne a yau Laraba a birnin Pacifico Yokohama, a Yokohama, […]

Buhari da shugabannin Afirka sama da 20 sun bude taron TICAD 7 a Japan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da sama da shugabannin kasashen Afirka 20 ne a yau suka bude taron kasa da kasa kan bunkasa nahiyar Afirka karo na bakwai, da ake yi wa take da TICAD7 da yake gudana a birnin Tokyo. An dai bude taron ne a yau Laraba a birnin Pacifico Yokohama, a Yokohama, kasar Japan.

Shugaba Buhari zai gabatar da mukala a lokacin taron, a inda zai fayyace alakar Najeriya da Japan da kuma darussan da Najeriyar za ta dauka daga taron da aka yi karo na 6 a Kenya mai taken TICAD6.

 

Wasu daga cikin shugabannin da suka halarci bude taron sun hada da: shugaban kasar Egyp kuma shugaban kungiyar kasashen Afirka Abdel Fattah el-Sisi, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, shugaban Laberiya George Weah, shugaban Sierra Leone Julius Maada Bio, shugaban Nijar  Mahamadou Issoufou, shugaban Ghana  Nana Addo Dankwa Akufo-Addo , da Shugaban Mali Ibrahim Boubakar Keita. Sauran sun hada da: Andry Rajoelina (Madagascar), Uhuru Kenyatta (Kenya), da Paul Kagame (Rwanda).

Sai kuma Mohamed Abdullahi Farmajo (Somalia), Emmerson Mnangagwa (Zimbabwe), Faure Gnassingbe (Togo), Edgar Lungu (Zambiya), da Macky Sall (Senegal), tare da manyan shugabannin majalisar dinkin duniya da na bankin duniya da dai sauran su.