Buhari da taron kungiyar G7
Shugaban kasa Muhammad Buhari na daya daga cikin shugabannin Afirika shida da aka gayyata, suka halarci taron kungiyar kasashen duniya bakwai mafi bunkasa a duniya ta fannin masana’antu (G7) karo na 41, da aka gudanar a kasar Jamus kwanakin baya, tsakanin Alhamis 7 zuwa Juma’a 8 ga watan da muke ciki na bana. Ita dai […]
Shugaban kasa Muhammad Buhari na daya daga cikin shugabannin Afirika shida da aka gayyata, suka halarci taron kungiyar kasashen duniya bakwai mafi bunkasa a duniya ta fannin masana’antu (G7) karo na 41, da aka gudanar a kasar Jamus kwanakin baya, tsakanin Alhamis 7 zuwa Juma’a 8 ga watan da muke ciki na bana. Ita dai wannan kungiya tana kunshe ne da kasashe bakwai mafiya bunkasa a duniya ta fuskar masana’antu. Sukan gudanar da taro ne duk shekara, inda suke tattauna muhimman al’amuran da ke kalubalantar duniya a lokacin. Wasu kasashen da aka gayyata sun hada da Laberiya, Senegal, Tunisiya, Etofiya da Irak. Taron dai ya samu halartar dukkan membobin kungiyar da suka hada da Amurka, Ingila, Faransa, Italiya da kuma Jamus, sannan akwai Jecob Zuma Shugaban kasar Afirika ta Kudu a matsayinsa na Shugaban kungiyar Hadin Kan Afirika.
Abu mai muhimmanci shi ne, Shugaba Buhari ya tafi da muhimman bukatun kasar nan, wadanda cikinsu har da batun tsaro, wanda shi ne kan gaba. Sauran bukatun sun shafi batun tattalin arzikin kasa, batun almundahana, dusashewar masu zuba jari daga kasashen waje, makamashi da kuma muhimman ginshikan bunkasa rayuwar al’umma. Sai kuma aka yi dace, dama wadannan batutuwa su ne kan gaba a taron, inda dama duk shekara kungiyar kan hadu ta tattauna batun tattalin arziki, ta’addanci da sauran al’amuran da suka shafi ’ya’yan kungiyar da dangantakarsu da sauran duniya. Ke nan wannan taron nan ya tattara kasashe masu kamanni da juna ta fuskar matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya, ciki kuwa har da Najeriya, wacce shugabanta Buhari ya wakilta.
Duk da cewa sakamakon taron ya gamu da martanoni daban-daban, ciki kuwa har da na mashahuriyar mujallar nan ta ‘Time’ wadda ta fassara sakamakon taron da cewa abin takaici ne amma dai alkawarin da taron ya yi na cewa zai taimaka wa Najeriya abin faranta rai ne. Yanzu ya rage ruwan Shugaba Buhari ya yi amfani da wannan dama da kasashen G7 suka ba Najeriya domin cin gajiyar al’amarin yadda ya dace. Kodayake ya kamata ya jinkirta har sai ya samu nasarar nada muhimman jami’an gwamnatinsa da kuma zayyana tsare-tsarensa.
Haka kuma, wannan tallafi da G7 ta yi wa kasar nan tayi, ya kamata a dube shi da idon basira, a amshe shi ta la’akari da abin da zai amfani kasar nan da kuma sassan duniya da ake kawance da su. Abin lura kuma shi ne, mafi yawan cikas din da tattalin arzikin kasashe masu tasowa ke fuskanta, ciki kuwa har da Najeriya yana faruwa ne a sakamakon tsare-tsaren tattalin arzikin kasa da kasuwanci da irin wadannan kasashe na G7 ke aiwatarwa. Ya kamata a lura da cewa, duk wani tallafi da irin wadannan kasashe ke shirin bayarwa, suna hada su ne da wasu bukatu na kashin kansu, ta yadda su ma za su amfana ta fuskar tattalin arziki.
Haka kuma, idan har ana maganar wani kawance tsakanin manyan kasashe da kuma masu tasowa, babban abin da zai yi tasiri shi ne idan an gudanar da shi cikin adalci, wato musamman ma al’amuran kasuwanci. Idan za a duba tarihi, za a ga cewa mafi yawan tsare-tsaren kawancen kasuwanci tsakanin manyan kasashe da masu tasowa, yana shafar kananan kasashen ne, inda manyan kan kasance wadanda suka fi amfana nesa ba kusa ba. A wannan batu, muhimmin abin da za a ce Najeriya za ta amfana da taron nan, shi ne idan aka karkata shi ta fuskar yadda al’amuran kasuwanci za su bunkasa tsakanin kasar da duniya. Don haka, a maida hankali sosai wajen ’yancin kasuwanci, a ba shi muhimmanci fiye da wani tallafi da za a ce za a ba kasar na kai tsaye, wanda kasuwanci mai ’yanci shi ne zai iya bunkasa tattalin arzikin kasa sosai.
A nan, muna fata gwamnatin nan za ta yi nazarin tsarin kasuwanci da kasashen waje domin ya dace da tunanin bunkasa kasa kamar yadda sabuwar gwamnatin ta zo da shi, musamman ma dai tsarin yarjejeniyar fahimta da Shugaba Buhari ya gabatar a taron na G7. Irin kasashen da aka gayyata a taron na bana, yana nuni da inda miyan tsarin kasuwancin manyan kasashen ya fuskanta, musamman ma ya nuna inda suke so su fuskanta a wannan fanni. Don haka lallai ne kasar nan ta yi himma wajen cin gajiyar shirin yadda zai amfani al’ummar kasa ta fuskar tattalin arziki, tsaro da sauransu.