Buhari ga Majalisa: Ba zan amince da dokar hana jama’a fadin albarkacin bakinsu ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta kin amincewa da kudurin dokar amfani da shafukan sadarwa na intanet, inda ya ce doka da ’yan Majalisar Dattawa ke kokarin yi matukar ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan ba zai amince da ita ba.Shugaban ya mayar da martani ne ga yunkurin Majalisar Dattawa na […]

Buhari ga Majalisa: Ba zan amince da dokar hana jama’a fadin albarkacin bakinsu ba
Buhari ga Majalisa: Ba zan amince da dokar hana jama’a fadin albarkacin bakinsu ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta kin amincewa da kudurin dokar amfani da shafukan sadarwa na intanet, inda ya ce doka da ’yan Majalisar Dattawa ke kokarin yi matukar ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan ba zai amince da ita ba.
Shugaban ya mayar da martani ne ga yunkurin Majalisar Dattawa na juya akalar yadda ake amfani da shafukan sadarwa na intanet, inda ya nanata aniyar gwamnatinsa wajen bayar da kariya ga ’yancin fadin albarkacin baki,
A wata sanarwa da Kakakinsa Malam Garba Shehu ya bayar, da ta kunshi martani ga cin zarafin al’umma wajen amfani da kafofin sadarwa na intanet, wadanda (Social media), ya bayyana cewa: “Shugaba Buhari na sane da matsayin al’umma game da kudurin dokar, amma ya ce babu wani abin tashin hankali, tunda dimokuradiyya ta kafa Majalisar Dattawan.
A cewar Malam Garba Shehu an rantsar da Shugaban kasa ne don ya kare martabar kundin tsarin mulki, don haka ba zai amince da duk wata doka da ta yi hannun riga da tsarin mulkin ba. Shugaban ya bayyana cewa, tofa albarkacin baki wani jigon al’amari ne a harkokin tafiyar da mulkin dimokuradiyya.
Shugaba Buhari ya soki lamirin wannan kudurin doka ne don tabbatar da kafuwar dimokuradiyya da kare martabar tsarin mulki da ya bai wa ’yan kasa ’yancin tofa albarkacin bakinsu.
Wannan kudurin dokar ya takura yadda ake amfani da shafukan sadarwa na intanet, kuma Sanata Bala Ibn Na’Allah ne ya gabatar da shi. Kodayake a cewarsa, kudurin ba takura wa mutane zai yi ba, illa dai kawai duk abin da mutum zai baza a shafukan ya tabbatar hakikanin gaskiya ne.
kungiyoyin kwadago da na dalibai da ’yan jarida da wasunsu ma har yaba wa Shugaba Buhari suka yi, saboda nuna rashin goyon bayansa game da kudurin dokar takaitawa ko takura wa masu amfani da shafukan sadarwar intanet.
Kwamitin Cibiyar ’Yan jarida ta Duniya (IPI ta yaba wa shugaba Buhari kan yadda ya caccaki wannan kudurin doka da majalisar  ke shirin tattaunawa a kai, inda ya yi nuni da cewa, ‘dokar adawa da kafafen yada labarai ce.’
A cewar Malam Kabiru Yusuf, wanda shi ne shugaban cibiyar ta Najeriya: “kudurin na da manufar cutar da masu amfani da shafukan sadarwar intanet, tare da tauye ’yancin fadin albarkacin baki. Cibiyar IPI na godiya ga Shugaba Buhari ganin yadda ya yi hanzarin sukar wannan mummunar doka,” inji shi.
Shi ma Shugaban kungiyar kwadago, Kwamared Peters Adeyemi ya soki lamirin dokar, ya ce dokar wadda ke da nufin daure wadanda suka saba mata na tsawoin shekara biyu, ta bijiro ne a daidai lokacin da ake so ’yan majalisa su himmatu wajen aiki da dokokin da za su tabbatar da kafuwar dimokuradiyya, sannan su hana cin hanci da rashawa a kasar nan.
Wannan doka dai da aka bijiro da kudurinta ta hadu da cikas, domin har masu zanga-zangar adawa da ita sun shiga farfajiyar mjalisar, inda suka daga kwalaye da rubuce-rubuce a kyallaye da ke nuni da ’yancin fadin albarkacin baki.