Buhari ga sojoji: Dole ku murkushe Boko Haram
Dalilin da Boko Haram ke kai hare-hare ga cibiyoyin soji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa sojojin kasar nan cewa dole ne su murkushe Boko Haram, inda ya ce yaki da ta’addanci abu ne da ‘tilas a yi nasara a kansa.’ Shugaba Buhari ya bayyana haka ne shekaranjiya Laraba a Maiduguri lokacin da […]
- Dalilin da Boko Haram ke kai hare-hare ga cibiyoyin soji
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa sojojin kasar nan cewa dole ne su murkushe Boko Haram, inda ya ce yaki da ta’addanci abu ne da ‘tilas a yi nasara a kansa.’
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne shekaranjiya Laraba a Maiduguri lokacin da yake bude Babban Taron Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya na Shekarar 2018. Shugaban ya ce “Ina son in karfafa wa sojojinmu cewa kada a karya musu gwiwa ta hanyar yada jita-jita, maimakon haka su ci gaba da mayar da hankali da sadaukar da kai don shafe Boko Haram daga bayan kasa.”
Jawabi na Shugaban Kasa yana zuwa ne bayan da mayaan Boko Haram suka zafafa kai hare-hare ga cibiyoyin soji a yankin Arewa maso Gabas a ’yan makonnin da suka gabata, inda suka sace makamai a cibiyoyin sojin a jihohin Borno da Yobe, tare da hallaka sojoji da dama.
Ya shaida wa sojojin cewa: “A matsayina na Babban Kwamandanku, zan yi iyakar karfina don ci gaba da karfafa muku ta hanyar samar da kayayyakin yakin da suka kamata da karo yawan mayaka da sauran abubuwan da suka wajaba domin ku samu karfin gwiwa a fagen daga.
Ya kara da cewa, yanzu haka yana dubawa da daukar matakain inganta albashi da alawus-alawus.
Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu ta ruwaito Shugaba Buhari yana yaba wa sadaukarwar da sojojin suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kare iyakokin kasar nan. Shugaban ya yi tir da hare-haren da Boko Haram ke kai wa cibiyoyin sojin. Kuma ya gana da shugabannin al’umma da dakarun da ke fagen daga, kuma ya ziyarci sojojin da suka jikkata a asibitin sojojin da barikin Maimalari a Maiduguri.
Ya kara da cewa, “Saboda haka ina mai karfafa gwiwarku da ku jajirce tare da zage damtse wajen ganin bayan wannan yaki, ina sane da munanan hare-haren da aka kai wa jami’an tsaronnu aka hallaka su a garuruwan Zari da Metele da sauransu. Ina jinjina muku tare da kara karfafa ku, ku ci gaba da jajircewa wajen yi wa kasa aiki don kare mutuncinta da martabarta. Mu kuma a namu bangaren, za mu yi kokarin ganin mun agaza wa harkar tsaro ta kowace fuska.”
Za mu mai da martani kan asarar da muka yi – Buratai
A jawabin Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce harkokin tsaron cikin gida sun riga sun inganta idan aka kwatanta da yadda kasar take kafin zuwan Shugaba Buhari a shekarar 2015.
Janar Buratai ya ce, an dauki sababbin dabaru don mayar da martani kan asarar da sojojin suka yi a baya-bayan nan. Ya ce sojoji za su ci gaba da kasancewa ’yan ba-ruwanmu ba za su goya wa wata jam’iyyar siyasa ba sannan za su sauken nauyin da tsarin mulki ya dora musu na kare dimokuradiyyar Najeriya.
A jiya Alhamis Shugaba Buhari ya kira taron shugabannin kasashen yankin Tafkin Chadi shida ciki har da Shugaban Chadi Idris Deby a birnin Jammaina don tattauna sake yunkurowar Boko Haram.
Wata sanarwa da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Labarai Femi Adesina ya fitar ta ce sauran shugabannin kasashen da suka gana a jiya sun hada da Kamaru da Nijar da Afirka ta Tsakiya, kuma an gayyaci Shugaban Jamhuriyyar Benin wanda yake tallafa wa yaki da Boko Haram don ya halarci taron.
Dalilin da Boko Haram ke kai hare-hare ga cibiyoyin soji
Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa akwai kwararan shaidun da suka tabbatar da cewa ’yan ta’addar Boko Haram suna shigo da miyagun makamai, har da masu kakkabo jiragen yaki da rokoki da sauransu daga kasar Libya da sauran kasashen da suke amfani da irin wadannan makaman, inda suke kai hare-harensu a kan jami’an tsaro da kuma fararen hula.
Tuni bangaren Abu Mus’ab Albarnawi ya yi kawance da Kungiyar Daular (IS) ta Abubakar Albagadadi tare da kafa reshen Daular Musulunci a Yammacin Afirka (ISWAP), abin da ya sanya bangaren da yankin Arewacin Borno yake samun makamai masu dimbin yawa, sai kuma bangaren Abubakar Shekau da ke da sansani a dajin Sambisa, inda yake aiwatar da hare-harensa a kudanci da tsakiyar Borno.
Majiyar ta Aminiya ta kalato cewa akwai yarjejeniya ta musamman da hukumomin kasar Chadi, inda ta bai wa jami’ansu damar fatattakar ’yan ta’addar Boko Haram har kan iyakar Najeriya, inda a yanzu haka an warware wannan yarjejeniya kuma ayyukan jami’an tsaron Chadi suka takaita a kan iyakar kasarsu, abin da ya bai wa ’yan ta’addar damar matsawa kan iyakokin kasashen Chadi da Nijar da Kamaru; inda suke cin karensu babu babbaka, ta hanyar kai samame ga jami’an tsaro a cibiyoyinsu da ke kauyuka ko dazuka, suna sacewa tare da kuma yin awon gaba da makamansu, da kayayyakin abincinsu.
Harin da ’yan ta’addar suka kai a baya-bayan nan a ranar Lahadi 18 ga Nuwamba, a kauyen Metele a Karamar Hukumar Guzamala a Jihar Borno ga Bataliyar Soji ta 157, wani soja da aka yi abin a idonsa kuma ya tsira ya tabbatar da cewa ’yan Boko Haram sun samu nasarsr kashe sojoji sama 100, a yayin da wadansu kuma suka bace. Ya ce kuma sun yi awon gaba da motoci da kayayyakin yaki, inda kuma wani rukunin sojoji ya ziyarci wurin da abin ya faru washegari Litinin don yin lissafi tare da gano abubuwan da aka yi asara, musamman kwaso gawarwaki da sojojin da suka jikkata.
“Wani sabon salon tsarin kai harin da Boko Haram suka fito da shi shi ne na kai hari da yamma, lokacin da duhu ya fara shiga, ta yadda da sun kai harin to za su iya samun wurin buya cikin duhu ba tare da samun wata matsala ba. Domin sojin sama na samun matsala wajen gudanar da aikinsu da dare, don haka ’yan ta ‘addan ke cin karensu babu babbaka idan dare ya raba,” inji majiyar da aka sakaya sunanta.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Hedkwatar Tsaro, Birgediya Janar John Agim, ya ce ba zai ce komai ba kan lamarin, domin ba ya gari, ya yi tafiya. “Don haka ba ni da wani muhimmin bayanin da zan iya yi a kan wannan batu,” inji shi.
A bangaren sojin kasa kuwa, sun musanta yawan sojojin da wasu kafafen watsa labarai ke yayatawa cewa sun rasu a wannan kazamin hari.
Kungiyar Gamayyar Jam’iyyun Adawa a Najeriya (CUPP), mai kunhe da jam’iyyu 40, ciki har da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sun mayar da martani a kan harin na baya-bayan nan inda suka yi kira ga Shugaba Buhari ya yi maza-maza ya sallami manyn hafsoshin kasar nan, domin a cewarsu sun gaza kuma lokacinsu ya shude.
To, ko me yake sanya ’yan ta’adda ke cin galaba a akasarin hare-haren da suke kai wa dakarun Najeriya a’ yan kwanakin nan? Wani babban jami’i a soja da yanzu yake fagen fama, wanda kuma ya ki yarda a fadi sunansa ya ce: “Duk mun yi asara ko kuma mun rasa wasu muhimmai daga cikin kayayyakin yakinmu. Wato akasari Boko Haram sun sace mana kuma har yanzu ba a maye gurbinsu da wasu ba, domin idan ka duba tsaf za ka gane cewa sama da kashi 70 cikin 100 na makamai da motocin da Boko Haram suke amfani da su duk namu ne suke kwacewa ko kuma su sace. Wato kashi 30 ne kawai suke samu a wani wuri na daban. To, kuma abin bakin ciki, ba mu samun wasu sababbi kuma wadanda suke hannunmu tsofaffi ne irin na da can. Kuma da wuya za ka iske suna cikin koshin lafiya. Wani abu shi ne, ’yan ta’addar suna kai hari ne a wani sansanin soja daya da abin da suka samu nasarar sacewa daga wani sansanin sojan na daban. Wannan shi ne dalilin da ya sa Boko Haram suke yawan samun nasara a kanmu a wasu lokuta, idan sun kawo mana hari.”
Wani masanin harkar tsaro kuma mai bibiya da sharhi a kan yakin Boko Haram, Manjo Salihu Bakari (mai ritaya), ya ce: “Dole ne Gwamnatin Tarayya ta hanzarta wadata jami’an tsaro da kayayyakin yaki don ta ceto al’umma kuma wajibi ne a tuna cewa a kwanan nan gwamnonin jihohi 36 sun amince gwamnati ta kashe Dala biliyan daya wajen sayo manyan makamai, to amma fa kada ku yi tsammanin shi ke nan an gama yaki ko wadannan makaman za su zo da wuri. A’a, za su iya kwashe shekara 4 kafin su zo, bai kamata a zauna a rike hannu kawai ba; dole ne a bi ta wata hanyar a yake su. Ina bai wa gwamnati shawara da babbar murya cewa ta bi wata hanyar ta kuma sake dabarar yadda za ta bullo wa wannan batu na tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa.”
Wani masani kuma mai sharhi a kan harkar tsaro, Kabir Adamu, a hirarsa da Aminiya, ya ce “Shugabannin Boko Haram suna kokari ne su ga cewa ko ta halin kaka Daular Borno ta zama a karkashin ikonsu. Kuma muddin gwamnati ba ta yi hobbasa ba a kai, hakan zai iya kasancewa. Wani abin da zai iya kasancewa, shi ne na yadda aka bude wata hanya da suke iya shigo da kayayyakinsu na makamai daga kasashen yankin Sahel, kamar Libya da Mali, inda Kungiyar ISWAP; ke ci gaba da samun nasara. Muddin gwamnati ba ta mike ba, za ta sha mamaki.”