Buhari gwarzon namiji ne – Gwamna Fayose
Gwamnan Jihar Ekiti, kuma wanda ya fi kowa caccaka da sukar zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a cikin gwamnonin Jam’iyyar PDP ne ya fara fitowa yana kira ga ’yan Najeriya su amince da sakamakon zaben da Janar din ya yi nasara da hannu bibbiyu daf da za a fadi sakamakon karshe na zaben. Gwamna […]
Gwamnan Jihar Ekiti, kuma wanda ya fi kowa caccaka da sukar zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a cikin gwamnonin Jam’iyyar PDP ne ya fara fitowa yana kira ga ’yan Najeriya su amince da sakamakon zaben da Janar din ya yi nasara da hannu bibbiyu daf da za a fadi sakamakon karshe na zaben.
Gwamna Fayose ya ce Janar Buhari ba karamin jarumi ba ne kuma Najeriya ta fi karfin a ce ta wani ne shi kadai. “Sakamakon zaben nufin Allah ne kuma abin da ’yan Najeriya suke so ke nan, don haka dukkan masoya zaman lafiya da ci gaban Najeriya wajibi ne su amince da shi,” inji Gwamna Fayose.
Gwamna Fayose ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kakakinsa ya Lere Olayinka ya fitar, inda yay aba wa jajircewa da sadaukar da kan Shugaba Jonathan da Janar Muhammadu Buhari.
Gwamnan ya ce bai kamata a kalli zaben a matsayin nasara ko faduwa ga wata jam’iyyar siyasa ba, “Ni a wurina ’yan Najeriya da dimokuradiyya ne suka yi nasara,” inji shi.
Ya yaba wa ’yan Najeriya kan yakinin da suke da ita ga bin tsarin dimokuradiyya, inda ya ce, “Ta hanyar wannan zabe, ’yan Najeriya sun nuna cewa dimokuradiyya ta kafu a kasar nan. Na yaba wa ’yan Najeriya musamman mutanen Jihar Ekiti. Na yaba wa Shugaba Jonathan kan kara karfafa harasashin dimokuradiyya a Najeriya. Na yaba wa Janar Buhari kan jajircewarsa da tsayuwar dakarasa. Ina kira ga ’yan Najeriya ba tare da lura da bambancin kabila ko addini ko jam’iyyun da suka fito ba, su amince da sakamakon zaben domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar nan.”
Ya ce Najeriya a matsayinta ta kasa tana sama da kowane mutum ko rukunin mutane, “Don haka ina kira da kada su yi duk wani abu da zai wargaza zaman lafiyar kasar nan,” inji shi.