Buhari: Hadari sa gabanka inda kake so

Idan da rai da rabo, saboda haka nan mutum bai fitar da rai daga rahamar Ubangiji. Nacewar da Malam Muhammadu Buhari ya sha yi a fafutukarsa ta neman shugabancin kasar nan abar yabawa ce matuka, domin kuwa ga shi nan hakarsa ta cimma ruwa a karo na hudu. Bayan ya sha turzawa har sau uku […]

Buhari: Hadari sa gabanka inda kake so
Buhari: Hadari sa gabanka inda kake so

Idan da rai da rabo, saboda haka nan mutum bai fitar da rai daga rahamar Ubangiji. Nacewar da Malam Muhammadu Buhari ya sha yi a fafutukarsa ta neman shugabancin kasar nan abar yabawa ce matuka, domin kuwa ga shi nan hakarsa ta cimma ruwa a karo na hudu. Bayan ya sha turzawa har sau uku yana cin karo da matsalolin da suka buwaye shi. ‘Yan Najeriya ma sun tabbatar da cewa mai nema na tare da samu, domin kuwa sun sha ba shi cikakken goyon baya a dukkan lokutan da ya fito neman shugabancin kasarsu.Kuma ba su gajiya da tallaba masa duk kuwa da cewa bai kai wa ga nasara, domin sun san cewa abin da ya bayar da tsoro wata rana shi zai komo yana ba da tausayi. To ga shi nan a yanzu Malam Muhammadu Buhari ake tsoro, alhali kuwa da can shi ake ta tausaya wa don ana kayar da shi a zabe.

Nasarar da Malam Muhammadu Buhari ya samu a wannan karon ta girgiza daukacin al’ummomin kasar nan, hatta ma jami’an manyan kasashen duniya sun jinjina masa.Sun kuma aiko masa da sakon taya murna, da yawa kuma daga cikinsu sun garzayo Abuja don halartar bukin rantsar da shi. Taron ya yi armashi ainun, kuma an kammala shi ba tare da wani targarda ko bacin rai ba. Domin hatta tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Ebele Jonathan ya halarta, cike da farin ciki da annashuwa, ya kuma fita da fitarsa salim-alin, ba kare bin damo, amma idan har an gano ya debo da zafi, to a bakinsa zai jefa.
A jawabin da ya yi, jim kadan bayan rantsar da shi Malam Muhammadu Buhari ya sosa wa kowa inda ke yi masa kaikayi dangane da matsalolin da suka dade suna ci wa kowa tuwo a kwarya. Ya kuma nuna cewa wasu daga cikin wadancan matsalolin da ya zayyana abin kunya ne ma a ji cewa suna wanzuwa a wannan kasa mai dimbin arziki da albarkar jama’a.Ya kuma bayar da tabbacin cewa wajibi ne a tashi haikan don magance su, domin dama can kyale wa aka yi har suka gawurta, suka buwayi jama’a.
Amma babban abin da ya fi daukar hankulan jama’a shi ne furucin Shugaba Buhari game da matsayinsa, na Malam Muhammadu Buhari, bisa wasu al’amura da za su iya tasowa dangane da alkawuran da ya dauka na kawar da rashawa da cin hanci da kuma yaki da rashin da’a da sanin-ya-kamata. Ya bayar da tabbacin cewa shi dai ba zai yi wa kowa bi-ta-da-kulli ba. Abin da ya gano, ko kuma wanda ya fito fili zai yi aiki da shi, kuma akwai dokokin kasa wadatattu da zai yi aiki da su wajen yanke hukunci. Shugaba Buhari ya kuma nuna cewa zai yi aikinsa ne ba tare da shakkun komai ba ko bayar da kariya ga wasu, domin shi na-kowa ne, zai kasance tare da kowa, ya kuma kare mutuncin kowa, da share hawayen wanda duk ya koka a gabansa.Ba kuma zai fake da guzuma ya harbi karsana ba. Ya ce zai yi adalci wajen ajiye komai a muhallinsa, zai ba mai gaskiya gaskiyarsa a dukkan al’amura, ya kuma dage wajen fahimtar mara gaskiya, ya bi da shi ta hanyar da ta dace.
Dangane da haka ne Shugaba Buhari ya ce shi zai kasance tamkar saniyar sake, babu wani wanda zai juya shi yadda yake so ba bisa tsarin dokoki ba, ko don a karkata akalarsa bisa son zuciyar wasu can dabam. Saboda haka nan Shugaba Buhari ya ce shi ba yaron kowa ne ba, kuma babu wanda zai bugi kirji, ya ce linzaminsa na hannunsa. Irin wannan hali ne ya dace da Shugaban Najeriya, domin hakan ya nuna cewa Malam Muhammadu Buhari ba zai zamanto tamkar sauran Shugabannin Najeriya da suka gabace shi ba, wadanda suke bari ‘yan-a-bi-Yarima- a-sha-kida, ko ‘yan baranda na zagaye su, suna masu fadanci har su samu gindin zama, su zame masu karfen kafa ko alakakai, kadangaren bakin tulu.
Shugaba Buharin yanzu ba irin na zamanin mulkin soja ne ba.Zai yi aiki ne da abubuwan da ke gabansa, wadanda ya tantance sahihancinsu da kuma ingancinsu ga dukkan matakan da zai dauka don yi wa jama’a hidimar da za ta janyo masu alheri, ta kuma kawar masu da matsalolin da ke addabar su. Shi ya sa tun daga ranar farko ta kama aiki, yake ta taka-tsantsan don gudun kada ya dauki wani mataki ko yanke hukuncin da ya saba ka’idojin rantsuwar aikin da zai yi.Bai kuma sha alwashin yin wani abu game da alkawurran da ya dauka yayin yakinsa na neman zabe, ko koke-koken jama’a game da wasu matsaloli ba sai idan ya nazarci salsalarsu da kuma tasirinsu ko akasin haka game da damuwar da ke kansu.
Shi ya sa tun da sanyin safiyar mulkinsa bai zake ba kamar yadda wasu jami’an hukuma suka dinga hana wasu manyan jami’an gwamnatin da ta shude daga ficewa kasar zuwa kasashen ketare da yawunsa.Yana mai cewa shi bai ce a hana kowa ficewa daga kasar ba, domin alkalan kotuna ne kadai ke da ikon yin haka, bisa tsarin shari’a, ba shi ba. Wannan wata babbar alama ce da ke nuna cewa Shugaba Buhari ba zai yi katsalandan cikin harkokin da suka shafi dokoki da al’amuran shari’a ba.Zai ba kowane bangare hakkinsa da kuma daman gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba tare da katsalandan ba. Amma hakan ba yana nufin cewa zai kawar da kai idan an saki hanya ba, ko an tafka zaluncin da zai cutar da jama’a.
Saboda haka nan idan aka yi hakuri, aka bi Shugaba Buhari a-sannu-a-sannu, za a kai ga biyan dukkan bukatun da ake da su game da shi, amma fa wajibi ne a tuna cewa Shugaba Buhari bai da garaje, ya kuma ki garaje, domin wannan aikin shaidan ne. Shugaba Buhari tamkar hadari yake, yana sanya gabansa inda duk yake so, kuma inda duk ya nausa alheri ne zai ta zubowa, kowa ya amfana.