Buhari: Kada jama’a su zaci dadi zai zo nan take – Babban Joji
Tsohon Babban Jojin Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim Umar ya ce yanzu ne al’ummar Najeriya suka san sun zabi shugabanni na kwarai, ba wadanda ake dora musu tilas ba. Alhaji Ibrahim Umar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Birnin Kebbi, inda ya ce kuma al’ummar Najeriya za su amfana da […]
Tsohon Babban Jojin Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim Umar ya ce yanzu ne al’ummar Najeriya suka san sun zabi shugabanni na kwarai, ba wadanda ake dora musu tilas ba.
Alhaji Ibrahim Umar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Birnin Kebbi, inda ya ce kuma al’ummar Najeriya za su amfana da dimbin arzikin da Allah Ya yi wa kasar nan, sakamakon zaben Shugaba Muhammadu Buhari da sauran shugabanni a matakai daban-daban.
Ya ce a nasa hasashen, yanzu ne Najeriya za ta samu ribar dimokuradiyya cikin adalci da kyautata wa al’umma musamman ganin yadda zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake da hangen nesa da kuma gaskiya cikin al’amuransa.
Alhaji Ibrahim Umar ya ce a yayin da ’yan Njeriya suke murna da godiya ga Allah saboda samun jagora adali mai fada da cikawa, “abin da ya rage shi ne mu yi ta yi wa zababbun shugabanninmu addu’o’in samun jagoranci daga Allah,” inji shi.
Tsohon Babban Jojin ya ce, kada jama’a su zaci cewa dadi zai zo nan take, domin yanzu ne ’yan Najeriya ke da jan aiki a gabansu, ganin shekarun da aka kwashe ana almubazzaranci da dukiyar jama’a a kasar nan. Ya ce yana da tabbacin duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi mulki ne a tafarkin dimokuradiyya, amma ya hakikance cewa zai yi kokarin tabbatar da adalci da ba kowa hakkinsa. Ya ce kuma na tabbata yadda na san Muhammadu Buhari, na yi imani duk wanda ya kwashi kudin kasar nan zai sa a maido su a yi wa jama’a aiki, domin azzalumi ba ya kusantar gwamnatinsa koda dan uwansa ne.”