Buhari: Kafin zaben 2019! (2)

Kai in gajarce muku, MASOYA Buhari ba sa nuna rashin da’a a koyaushe! MASOYA Buhari masu gaskiya da rikon amana ne, ko Buhari na nan ko ba ya nan! Ko Buhari zai sake cin zabe ko zai fadi, domin ba bautar Buhari suke yi ba, kasarsu suke yi wa hidima! A halin da muke ciki […]

Buhari: Kafin zaben 2019! (2)

Kai in gajarce muku, MASOYA Buhari ba sa nuna rashin da’a a koyaushe! MASOYA Buhari masu gaskiya da rikon amana ne, ko Buhari na nan ko ba ya nan! Ko Buhari zai sake cin zabe ko zai fadi, domin ba bautar Buhari suke yi ba, kasarsu suke yi wa hidima!

A halin da muke ciki akwai rikici tattare da nawa tunanin game da MASOYAN Buhari, musamman wadanda ke da ikirarin ba wani da ya iya sai Buhari. Ba wani mai gaskiya sai Buhari. Ba mai iya ceton kasar nan in ba Buhari ba. Saboda haka in muka sake ba mu sake zabar Buhari ba a shekarar 2019 to mun yi wa kasar nan tereren tsiya, mun kuma jawo mata jangwam na har abada. Irin wannan tunani, ni a tawa fahimta shi ne ya kasance babbar matsalar kasar nan, domin kuwa Buhari ba shi ne Najeriya ba. Buhari ba shi ne masanin komai game da matsalolin Najeriya ba. Buhari bai iyawa shi kadai ko da kuwa mun shekara muna hankoron ganin hakan ya tabbata.

Ba wannan kadai ba, ni ina ganin ko da Buhari ya ci zabe a 2019, a ce kuma akwai damar da za mu iya sake zabarsa a shekarar 2023 ko ya rike shugabancin Najeriya har iya rayuwarsa, canjin da muke ta nema da hankoron dabbakawa ba zai taba samuwa ba. Me ya sa? Ba wani abu ke sa ni tababar ba sai damuwa da rashin yardar da nake da ita game da imanin MASOYAN Buhari, domin kuwa ban sani ba, in MASOYAN Buhari su masu gaskiya da rikon amana ne kamarsa! Shin muna jin cewa za mu iya barin Buharin da muke so ya gudanar da mulki yadda ya dace da irin tunanin da muke da shi na cewa shi kadai ya iya, shi ne kuma mai iya fitar da kasar nan daga cikin matsatsin mulki da zamantakewa da take ciki? Mu tambayi kanmu, shin in Osibanjo da ke taimaka wa Buhari yana da dan kyas daga halayen Buhari, shin sauran mukarraban gwamnatinsa, garas suke? In garas suke me ya sa muke ji ana ta kai-kawo da wasu daga cikin mukarraban Buhari, ana cewa suna da kashi a gindinsu, a zamanin mulkin Buhari, a cikin gwamnatin Buhari, bisa jagorancin Buhari? Me ya sa har yau muke ganin an kasa shawo matsalar tsaro da kashe-kashe da sace-sace a zamanin mulkin Buhari, a karkashin jagorancin Buharin? Me ya sa har yau ake ta fama da Boko Haram ko satar mutane ko kashe-kashe tsakanin Fulani da makiyaya ba gaira ba dalili ko kuma sace mutane  domin neman kudin fansa? Me ya sa? Ba Buharin ne ke mulki ba? Shin ba gwamnatin canji ba ce ke mulki a halin yanzu? Shin ba MASOYAN Buhari ba ne a cikin kasar? Ko kuwa abin nan ne da ake ta fada ai matsalar ta gwamnatin PDP ce da ta wuce, ko kuma ai barnar da aka yi ce cikin shekara 16 na gwamnatocin baya, shi ya sa wannan gwamnatin ke tafiyar hawainiya ko gudun kunkuru? Shin wannan gaskiya ne?

Shin MASOYAN Buhari ko masu taimaka wa Buharin, wadanda suke so ya yi aikin ci gaban kasar da ya kudiri aniyar yi in ya sake hayewa bisa kujerar shugabancin Najeriya in Allah Ya kai mu shekarar 2019, shin mun kuwa amince a cikin ranmu cewa da gaske muke so a kawo canji a kasar nan? Ina sauran masoyan Buhari daga cikin gwamnonin kasar nan, su fes suke? Me ke faruwa a wasu jihohin da APC ke mulki da wasu ofisoshin ministocin Buhari da wasu ma’aikatun gwamnatin Buhari, bisa ga dukan alamu kamar ba ta canja zane ba! Ke nan me muke bukata a kasar nan, ba wani abu ba ne face canji daga ko’ina, wato kowa ya canja tun yanzu, ba wai ’yan APC ko PDP ko sauran jam’iyyu ba, kowa da kowa da ke cikin kasar tamu, domin kuwa duk mun lalace tamkar dankali mai sankara.

Abin da ya kyautu mu yi shi ne mu shiga yin aiki tukuru domin kawar da duk wata tambada kafin Buhari ya sake dawowa bisa karagar mulki, mu kuma ci gaba da dauwama a kan wannan tunani ko bayan ya hau karo na biyu. Idan kuma bai ci zaben ba, muna cewa ke nan canji ya yi hijira daga Najeriya? Ko alama, shi ya sa nake cewa ba Buhari ba ne macecin kasar nan, ba kuma Jam’iyyar APC ba ce mai ceto da kawo canji, kadai. Canji namu ne ’yan Najeriya da Buhari ko ba Buhari.

Saboda haka a kullum zan rika nanatawa, ni dai abin da na sani shi ne MASOYA Buhari, ba MASOYAN Buhari ba su ne za su kawo canji a kasar nan, su ne za su riki kasar nan da kyau har canji ya samu; kama daga mace mai sayar da man gyada ko mai Keke-NAPEP ko dan bangar siyasa ko soja ko dan sanda, kama zuwa kansila ko minista ko gwamna ko wadansu daga cikin al’ummar kasar nan da aka ba rikon wani sashe na kasar nan a ma’aikatu ko makamantan haka. Da Buhari ko ba Buhari! Buharin na a matsayin Shugaban Kasa ko kuwa akasin haka. Lokaci ya yi da za mu sake salon biyayya da kauna da muke nuna wa Buhari, mu gyara! Ta yaya za mu yi wannan gyara a halin yanzu? Akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi, wasu daga cikinsu ne zan kawo nan gaba domin mu tattauna, mu ga in za mu iya samar da mafita! In Sha Allah.