Buhari mai gaskiya ne da rikon amana – Sule Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya sanya ribas kan yadda yake caccakar dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari inda a ranar Litinin ya bayyana cewa Buhari shugaba ne mai gaskiya ne da rikon amana. A baya-bayan nan Gwamna Lamido wanda ya rika sukar Janar Buhari, ya ba masu saurarensa […]

Buhari mai gaskiya ne da rikon amana – Sule Lamido
Buhari mai gaskiya ne da rikon amana – Sule Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya sanya ribas kan yadda yake caccakar dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari inda a ranar Litinin ya bayyana cewa Buhari shugaba ne mai gaskiya ne da rikon amana.

A baya-bayan nan Gwamna Lamido wanda ya rika sukar Janar Buhari, ya ba masu saurarensa mamaki lokacin da ya rika kwarara ruwan yabo ga Buhari a lokacin da yake zagayen kamfe a garin Maigatari da ke Jihar Jigawa inda ya gabatar da dan takarar Gwamnan Jihar karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Aminu Ibrahim Ringim ga jama’a.
“Kamar kowane mutum na yarda Buhari ba mahandami ba ne, mai gaskiya ne tsabtatacce ne kuma dan Najeriya mai kishin kasa. Ba ni da wata matsala da Janar Buhari kamar yadda wasu suke dauka. Damuwata kullum wadanda suka fice daga jam’iyyarmu wadanda PDP ta mayar ministoci da gwamnoni da shugabannin majalisa da wakilan majalisar dokoki ta kasa, wadanda suka bar mu bayan sun ci gajiyar PDP sosai,” inji Gwamna Lamido.
Daga nan sai Gwamna Lamido ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar a yanki su kada wa ’yan takarar PDP a zabe mai zuwa. Ya ce da takarar Gwamnan da mataimakinsa Dokta Nuruddeen Mohammed za su ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba a jihar idan aka zabe su a zaben na watan gobe.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista