Buhari: Makiyansa fadawansa
A kullum, kuma a ko’ina mutum ya zagaya, zai ji dubun-dubatan ‘yan Najeriya na yi wa Shugaba Muhamadu Buhari fatan alheri, suna rokon Maiduka ya kare shi daga sharrin masu sharri, ya kuma tserar da shi daga dukkan kulle-kullen mahassada. ‘Yan Najeriya ba su son jin wani abin da za su yi tsammani zai iya […]
A kullum, kuma a ko’ina mutum ya zagaya, zai ji dubun-dubatan ‘yan Najeriya na yi wa Shugaba Muhamadu Buhari fatan alheri, suna rokon Maiduka ya kare shi daga sharrin masu sharri, ya kuma tserar da shi daga dukkan kulle-kullen mahassada. ‘Yan Najeriya ba su son jin wani abin da za su yi tsammani zai iya kawo wa Shugaba Buhari cikas a harkokin gudanar da al’amuransa, ko kuma ya yi wa gwamnatinsa tarnakin da zai hana ta iya aiwatar da kyawawan ayyukan alheri ga dimbin jama’ar da suka tsaya mata. A takaice dai ‘yan Najeriya ba su kaunar raggo, ko wanda ya gaza, Shugaba Muhammadu Buhari kuwa muzakkarin shugaba ne, wanda aka buga, aka bari, aka kuma gwada, aka same shi shiryayye, kuma tsayayye kan yi wa talaka hidimar da za ta daukaka matsayinsa.
To, amma idan shugaban da ya samu yardar jama’a ya nuna damuwarsa game da rashin amincin wasu abokan aikinsa, babu shakka kowa zai tsammaci cewa, da walakin wai goro a miya, akwai abin da ke faruwa wanda kuma bai gamsar da shugaban da zai fito ya yi furuci irin haka ba. Ashe ke nan ana iya cewa, sa’ilin da Shugaba Buhari ya furta kalamu irin haka, a Doha ta kasar katar, a ‘yan kwanakin baya, ana iya cewa, akwai kunama a cikin wandonsa, domin kuwa ya fayyace gaskiyar al’amarin da yake ji ne dangane da haka, da kuma yadda abin ke ci masa tuwo a kwarya.
To, ko da wacce take hirar da shi a tashar talbijin ta Al-jazeera, ta nemi karin haske game da furuncin da ya yi dangane da abin da ya yi kama da kunamar cikin wando, Shugaba Buhari cewa ya yi, ‘Babu shakka akwai marasa aminci a cikin gwamnatinsa,’ domin kuwa babu yadda za a ce dukkan jami’an gwamnati, musamman ma wadanda ya gada daga ta PDP, za su kasance amintattu, kuma masu bayar da cikakken goyon baya ga gwamnatinsa. Daga nan sai ya shawarci abokan adawa da masu saurin sukan lamirin gwamnatinsa da su rika yi musu adalci, musamman ma ganin yadda yake tafiya tare da tsoffin jami’an gwamnatin da ta gabace su, ciki har da manyan sakatarorin da har yanzu su ne ke damawa, suna bayarwa ana kurbawa. Saboda haka nan ba zai iya tabbatar da amincin dukkansu ba da kuma irin goyon bayan da suke bayarwa, dari bisa dari ba. Amma sai dai Shugaba Buhari ya yi kawaici, ya ki tona sunayen wadancan jami’an gwamnatin da ya ce suna yi masa zagon kasa.
Abin tambaya a nan shi ne: su wane ne wadancan jami’an da suke yi wa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa da makarkashiya? Ana iya cewa, Shugaba Buhari ya san su, kuma idan ta kama, zai iya kiransu da sunayensu don kowa ya san su? Idan kuma bai san ko su wane ne ba, to ina fa’idar fadin haka a gare shi, kuma wane tasiri hakan zai yi ga jama’ar kasar nan? Idan kuma har ya san su sarai, to me zai yi don maganinsu? Idan dai har da Shugaba Buhari bai san akwai irin wadancan mutanen dankare a cikin gwamnatinsa ba, ba zai bugi kirji ba haka nan kawai ya yi irin wannan furucin ba, domin kuwa yana ganin irin abubuwan da ke wakana a gwamnatinsa wacce ake hana ruwanta gudu a fannoni da yawa.
Wannan furuci na Shugaba Buhari shi ake kira Kadaran-Kadahan, tamkar kashedi ne ga wadancan mutanen don su fahimci an san da zamansu, za a kuma dauki matakan tona asirinsu muddin ba su canja halayensu ba. Wannan al’amarin dai ya yi kama da kissar wanzamin da ya zo yi wa kwarton matarsa gyaran fuska, bayan ya soka askarsa a cikin hancinsa, sai ya fadakar da shi abin da ya sani, shi kuma kwarton nan take ya ba shi tabbacin cewa, ‘ai ya bari tuni.’ Kowa dai ya san Buhari ba kanwar lasa ba ne, maganarsa karfi ke gare ta, kamar kyaure. Idan ya ce e, bai komowa ya ce a’a, idan kuma ya fadI magana tabbaci hakika babu burbudin karya a ciki. A dai jira a gani, kafa kas, maciji kas, watarana za a hade. Ai Shugaba Goodluck Jonathan ya taba nuna cewa, a cikin gwamnatinsa akwai ‘yan Boko Haram, kuma kungiyar na da wakilai a manyan hukumomin gwamnatinsa, amma sai ya kasa kware masu fuska, don tona asirinsu, har sai da suka yi sanadiyyar tuntserewarsa daga mulki. ‘Yan Najeriya sun tabatar Buhari ba zai yi irin haka ba. Idan ya ce akwai masu zagon kasa a gwamnatinsa, akwai su ne, ba zai fadi haka don neman gindin zama wajen kowa ba, ko kuma don ya dadada wa wasu rai.
Idan har wani shugaba zai yi korafi game da kokarin kwashe masa kafa, a kuma gurgurta gwamnatinsa to akwai daya cikin biyu, ko kuma dukkansu. Imma dai ya ga abubuwan da ya tsara ba su gudana yadda ya kamata, kuma yana nuna damuwa ga take-taken abokan aikinsa, ko kuma akwai wasu a cikin gwamnatinsa da ba su damu da tsare-tsarenta ko al’amuranta ba, sun kuma dukufa wajen ganin sun dagula al’amura, ko sun tadiye gwamnatin. To, a irin wannan marrar da ake ciki ta halin kunci da tsadar kayayyakin abinci da na masarufi da zullumin abubuwan da kan iya faruwa sakamakon rashin tabbas a manufofin gwamnati wajen inganta ayyukan kyautata rayuwar jama’a da jin dadinsu, ana iya cewa, ‘biri ya yi kama da mutum’ dangame da wadancan batutuwan da ake ganin sun kai Shugaba Buhari nuna damuwarsa game da yiwuwar kasancewar wasu da ba su son gwamnatinsa ganin gwamnatinsa da kumbar susa.
Ko ma mene ne, talakawa ne dai suka taru suka cicciba Muhamadu Buhari bisa mulki, su ne kuma suka dage wajen kafuwar gwamnatinsa wacce suke son ta samar da canjin da zai fitar da su daga kangin bakar wahala da aka tsunduma su a ciki shekara da shekaru, saboda haka nan za su ci gaba da ba ta cikakken goyon baya don magance dukkan wasu masu son kawo cikas din da zai wargaza kokarin gwamnati wajen kyautata al’ummominta. Idan kuma har wadancan mutanen da Shugaba Buhari ya fara kuka da su a cikin gwamnatinsa ba su bar aikata ta’asar da ta sa ya bara ba, to su tabbata fa watan shan kunyarsu ya kusa tsayawa, domin kuwa jama’a za su ba shi dukkan goyon bayan da yake bukata don bankado su da kuma tozarta su, a kuma yi masu hukuncin da zai kai su ga yabawa aya zaki. Yanzu dai Buhari ya gane cewa, ‘makiyansa fadawansa,’ to ai sai a dauki matakan awon gaba da su, domin kuwa idan babu rami, me ya kawo batun ramin?