Buhari, Masari da kungiyar ACF sun yi ta’aziyyar Kaita

Shugaba Muhammadu Buhari da kungiyar ACF da kuma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masri sun mika ta’aziyyarsu dangane da rasuwar Alhaji Lawal Kaita.   Shugaba Buhari ya isar da jajensa ne ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu inda ya ce rasuwar […]

Buhari, Masari da kungiyar ACF sun yi ta’aziyyar Kaita

Shugaba Muhammadu Buhari da kungiyar ACF da kuma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masri sun mika ta’aziyyarsu dangane da rasuwar Alhaji Lawal Kaita.
 
Shugaba Buhari ya isar da jajensa ne ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu inda ya ce rasuwar Kaita asara ce ga kasa baki daya.
 
Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta bayyana cewa ta kadu yayin da ta samu labarin rasuwar Alhaji Lawal Kaita.
 
Shi ma Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana alhininsa dangane da rasuwarsa inda ya ce Najeriya ta yi asarar dan kasa nagari.