Buhari na bukatar addu’a – Buba Galadima
A makon jiya ne muka fara kawo muku tattaunawar da muka yi da Injiniya Buba Galadima, kan dalilinsa na barin siyasa. A ci gaba da tattaunawar ya ce, Janar Bubari yana bukatar addu’a daga dukkan dan Najeriya, ko mene ne dalili? Ya bayyana dalilin da kuma sauran batutuwa da dama: Aminiya: Idan muka fahimce ka […]

A makon jiya ne muka fara kawo muku tattaunawar da muka yi da Injiniya Buba Galadima, kan dalilinsa na barin siyasa. A ci gaba da tattaunawar ya ce, Janar Bubari yana bukatar addu’a daga dukkan dan Najeriya, ko mene ne dalili? Ya bayyana dalilin da kuma sauran batutuwa da dama:
Aminiya: Idan muka fahimce ka ta tabbata ke nan cewa, wadannan matsalolin suna daga cikin dalilan da suka sa ka janye daga harkokin siyasa?
Buba Galadima: Eh, a’a. Na koma baya ne don ba ni da mukami a yanzu. Ka sani ko zuwa gobe zan iya neman mukami? Ka sani ko kuma fada ce irin ta rago? Ka bari mana in muna da rai da tsawon kwana ka ga abin da zai auku. Ai yanzu muke wa fadan shiri. Kada mutane su damu, Buban nan dai yana nan. Yana da rai da lafiya da shi za a ’yanta al’ummarmu in Allah Ya so. Ai siyasar ba don wani nake yi ba, sai saboda abu uku. Na farko ina siyasa saboda al’ummata, na biyu ina yi saboda kasata, na uku ina yi saboda bayana. To da al’ummar tawa da kasar tawa da bayan nawa, duka suna nan. Ka san ko a gidanka ma sai ka yi siyasa. Domin in kana da mace daya da ’ya’ya biyu, in ba ka yi siyasa ba a tsakaninsu, ba za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba a gidan. Saboda haka babu dan Adam duk yadda yake da zai ce ya rabu da siyasa gaba daya. Abin da na yi shi ne, tunda ba na rike da mukamin siyasa, na ja da baya irin na rago. Shirin fada ne, zan dawo. Kuma na samu kira daga wurin gwamnoni da ministoci da manyan mutane a Najeriya da tsofaffin shugabannin kasa a kan wannan magana da aka yi, ban yi barci ba cikin dare sai karfe bakwai na safiyar yau (Larabar makon jiya). Duk magana nake a daren da mutane, za ka gani a fuskata yanzu, cewa ban samu hutu yadda ya kamata ba. Ni kaina ban san ina da muhimmanci a siyasar Najeriya ba, sai a yanzu da hakan ta faru da na ce zan ja da baya.
Aminiya: Yanzu ka mika takardar ajiye mukaminka na Sakataren Jam’iyar CPC ne?
Buba Galadima: Ai mun nade tabarmar jam’iyyar jiya. Ba sai na mika ba, ai mun sa hannu. Kuma wannan Jam’iyyar APC da aka ce muna yi mata zagon kasa ba mu yarda a yi hadaka ba, mutanen da suke wannan maganar mahaukata ne. Yaya za a ce ni Buba Galadima ban yarda a yi hadaka ba, bayan ni ne na rubuta memo (bukata) yau shekara daya cewa; in muna son hakarmu ta cimma ruwa, sai mun hada dukkan jam’iyyun adawa, mu kuma shiga cikin PDP mu raba ta. Don mu dauko wadansu mu kara a kanmu. Idan ba a yi haka ba, a yadda muke tafiya inna-rududu, ba ta iya cin zabe. In da ina-rududu na iyya cin zabe a Najeriya da Buhari ya zama Shugaban kasa tun shekarar 2003. Da yanzu kila mutum na biyu ne a jam’iyyar yake neman shugabanci. Amma a siyasance a Najeriya, tunda ba kirga kuri’a ake yi ba, ba zai yiwu ba. Sai ka samu wadanda suka isa, a kowace jiha, a kowace karamar hukuma a kowace unguwa suna wakiltarka wadanda suke da karfin da za su iya zuwa ofishin DPO ko Daraktan SSS na Jiha. Kuma Kwamishinan ya tashi ya sara ya ce maka ranka ya dade. Muddin ba mu samu wannan ba, to, fa ba za mu iya cin zabe ba. Mu kanmu shugabannin tafiyar ba mu natsu, mun zauna mun tattauna da juna mun yi wa tufkar hanci ba. Domin a irin wannan, zama ake yi, a ce wuri kaza da ba mu da mutane, wa za mu nema mu kawo? A wuri kaza da ba mu da shi, ya ya za mu yi mu tafiyar da al’amuran nan? Duk wadannan ba a yi, mun dogara ne da neman jama’a, kuma mun nemi jama’a sun amsa. Jama’ar nan ba su da makiyaya. Muddim ba mu samu makiyaya ba, to, ba za mu cimma nasara ba. A dalilin wannan ne na rubuta ‘memo’, Janar Buhari yana da shi, jam’iyyar tana da shi. Amma wadansu munafukai sun zo sun ce wai ba maso, su ne fa munafukan da suke son su raba shi da mutanensa. Har rokon Allah suke a kansa, don su hada shi da mutanensa. kila sun kusa cin nasara. Rokon Allah suke, su je su gaya masa wannan su je su gaya masa wancan, don su kidimar da shi. Janar Buhari yana neman addu’a daga dukkan dan Najeriya. Don na hakikance cewa yana da kishin kasa, kuma don kasarsa yake yi, amma hannu ya yi masa yawa. Ina son duniya ta sani, tunda muke zaune da Janar Buhari yau muna tare da shi shekara 12 ban taba zuwa gidansa ba ban da sau daya, bayan da ya shiga siyasa. Ban taba zuwa na je na ce Janar mu shiga daki da shi yau ina da magan don mu yi maganar wani mutum ba, ban taba yi ba. In akwai wanda ya ce na yi, a je a tambayi Janar Buharin. Ban taba zuwa na kai gulmar wani wurinsa ba, ba na kuma fadanci, shi ya sa ba ni da maigida a siyasa sai dai abokin tafiya.
Aminiya: To, yanzu da koma gefe a harkokin siyasa, yaya dangantakanka da Buhari za ta ci gaba?
Buba Galadima: Ta wa da kane. Muna nan, muna da dangantaka kwarai da gaske. Zan je gidansa, za mu yi barkwanci, zan ci in sha.
Aminiya: Ka ce Janar Buhari yana bukatar addu’a daga masoya, daga wani bangare kake ganin abubuwan suka taso?
Buba Galadima: Wadanda suke son su raba shi da mutanensa na gaskiya da suke tafiya da shi fisabilillahi. Wadannan bakin hauren da na ce maka suka zo, ba su ba ne suka zauna a Transcorp Hotel, kuma sun fada da bakinsu, suka rubuta sakamakon zabe, tun ba a yi zabe ba, aka fada a rediyo aka ce ’Yar’aduwa ya ci zabe ba? Yau su ne mutane? Anya kai kana ganin babu wani abu, kuma a yarda da su? Su ne wadanda suka yi amfani da soja suka je suka fatattaki mutanenmu, suka karkashe mutanenmu a kan zabubbuka, da mu fa suke yakin amma yau su ne mutane, mu ba mutane ba. Kai kana tsammanin babu wani abu?
Aminiya: Mutane za su iya cewa saboda hade jam’iyyar taku, kana ganin ba wani mukamin da za ka samu, shi ya sa ka watsar da siyasa me za ka ce?
Buba Galadima: Da ma ina tsammanin wannan tambaya, gara kuma da Allah Ya kawo ta. Ni Buba ba na siyasa saboda mukami, ina siyasa ne saboda ra’ayi, saboda akida, saboda al’ummata, saboda kasata, kuma saboda bayana. Idan saboda mukami nake yi, na gaya wa duniya, kuma har yanzu babu wanda ya karyata ni cewa; Obasanjo ya ba ni mukamin minista har sau uku, ya ba ni Shugaba Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) har wata takwas lokacin da aka daure Bode George ba a nada kowa ba. Ni ake jira in karbi mukamin, don suna kokarin su karya Buhari. Shugaba’Yar’aduwa da wani Ambasada yana nan da ransa, sun buga min waya ina Maiduguri, sun ce in zo, yana son mu yi aiki tare, zai ba ni Ministan Abuja. Mun san juna da ’Yar’aduwa shekara 43, kafin ya rasu. Ban dauki ko sakan daya ba na ce da shi ya kai kasuwa. Dokta Goodluck, wannan mukamin da aka ba Bala Mohammed (Ministan Abuja), mu ne da muka yi SNG ya kamata a ba mu, kuma an ba da sunana aka ce a ba ni, na ce a kai kasuwa, ba saboda neman mukami na yi ba. Na yi ne saboda kasata ta zauna lafiya. Shin idan Buhari ya zama Shugaban kasa, wane mukami zai ba ni wanda ya wuce Ministan Abuja? kila ma in ya zama Shugaban kasa ma, a ce in an gan ni kusa da billa a kama ni, saboda irin wadannan maganganu da suke aukuwa. Wane mukami zai ban? Ka ga dai ba zan iya masa Mataimakin Shugaban kasa ba. In ko ba na Mataimakin Shugaban kasa, babu mukamin da ya wuce zama Minista. A ministan ma, abin da dan Najeriya ya fi so ya zama in mai son sata da mulki ne, shi ne ya yi Ministan Abuja ko na mai ko na tsaro. To me zan yi da Ministan Mai ma tunda an ce wai an ba ni rijiyar man? In don mukami nake yi, in karba mana.
Aminiya: Wasu na ganin kila don ka fara gina ’ya’yanka a harkokin siyasa ne, sukan ba da misali da Zainab da ta zama kansila ya sa kake ganin lokaci ya yi ku ja baya ku bar su?
Buba Galadima: Wato akwai abubuwa da yawa, a cikin zarge-zargen da ake yi min, na ce an yi min zargi ya fi a kirga. Ni da kake gani, gwamnoni sun fi a kirga Allah Ya yi su, sannan Buba Galadima ya yi su. Zan ba ka misali, Cif Melford Okilo, Gwamnan Jihar Ribas a 1979, Allah Ya yi masa Gwamna, Buba Galadima ne sanadi. Don ni na ba shi damar da ya je taron tsarin mulki, na ba shi damar da ya samu kudi ya tsaya takarar Gwamna. Ta hanyarsa, sakataren gwamnatinsa, Cif Rufus Ada George muka saba da shi, ya tsaya zabe da Cif Zack Abule, Shugaban Bankin Crystal Bank, ya ba shugabanin Jam’iyyar NRC kudi, ba na son in fadi ko nawa ne, suka ba shi takara. Ni kadai na ce ban yarda ba, aka tafka rigima, Shinkafi yana da rai, Babangida yana da rai. Muka je muka ga Janar Abacha, cewa ga halin da ake ciki, muka sa aka haramta takarar Abule. Muka sa aka yi doka a cikin awa 24 aka ce idan aka soke dan takara wanda aka yi firamare ya zo na biyu, shi ne zai zama dan takarar jam’iyya. Mu muka yi wannan a lokacin da kwai yake da gashi, muka sa Ada George ya zama Gwamna. Abubakar Musa Yawuri an kada shi a zabe da magudi, ni na tsaya tsayin-daka sai da aka ba shi takarar ya zama Gwamna. Peter Odili da kake gani a kofar gidana yake kwana, ni na taimaka masa da Ada George din har ya zo ya zama Gwamna. Duk mutanen nan da na kirga maka ko Clement Ebiri, babu mutumin da na taimaka masa ya zama Gwamna daga baya na tashi takansa ta Kano na je wurinsa cewa tunda na taimaka masa don Allah Ya ba ni masauki, in sauka a gidan gwamnati, ban taba yi ba.
Dadin dadawa, Jam’iyyar CPC ce ta kafa gwamnati a Jihar Nasarawa. Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Jega ya rubuta takarda shafi hudu ga Sufeto Janar na ’Yan sanda cewa mun canja dan takarar Gwamna a Nasarawa. Saboda haka, a kama mu a kulle mu, don irin labaran da PDP suka gaya masa. Babu binciken duniya da ba a yi mana ba, ni da Yarima Tony Momoh, Allah Ya kubutar da mu daga wannan wulakanci, shiryayye. Abin da nake son na gaya maka shi ne, tun lokacin da aka ce Al-Makura ya ci zaben Gwamna, aka je rantsar da shi, ya yi bikin shekara daya, ya yi bikin shekara biyu yana kan mulki, ban taba taka Nasarawa ba, sai sau daya lokacin da ’ya’yansa suka yi hadari wasu suka rasu, na je yi masa ta’aziyya. Kuma Al-Makuran nan, ya ba ni ginin firamare na UBE na Naira miliyan bakwai, aka zo a Majalisar koli ta jam’iyarmu, uwaka, ubanka aka zarge ni cewa na kewaya ta baya ina karbar kwangila a wurin Gwamna. Alhali a jarida na ga an sa tandar kwangilar ta UBE, na nema aka ba ni rukunin aji daya kan Naira miliyan bakwai. Ina Sakataren Jam’iyya ta kasa, koda Naira miliyan bakwai kacokan Al-Makura ya ba ni, me ya yi, in ban da matsiyata? Balle kwangila ce, to, yanzu na yi kwangilar kudina Naira miliyan uku sun makale yau wata hudu ban samu ba, amma fa zagin ubana aka yi, ana zargina ana cewa kaza-kaza. To na gode wa Allah da ’yata ta kai shekara 30 ta yi aure ta kai munzilin shiga siyasa, har ta ci ta zama kansila
A jiya wani daga cikin ma’aikatanku ma ya tambaye ni ko wannan zabe da aka bar ’yarka ta ci, bayan ba a bar kowa ba, yana daga cikin cin hanci da PDP ta ba ka? Na ce, ita yarinyar ta yi aiki ta gaji mahaifinta. A kowane akwati ta ajiye mutum 37 masu tsare mata kuri’a don kada a yi mata magudi. Mutane tun daga Kebbi, Sakkwato, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Filato, Kaduna, Nasarawa, Kogi, Neja, duk sun kawo gudunmawa don taimaka mata. Wadansu akwatunan masu tsare mata akwatin sun fi wadanda suka fito jefa kuri’ar. Wato wadansunmu na kiran kanmu ’yan siyasa amma ba mu da idanuwa na gani ko kunnuwa na ji a siyasance. A wurina in ana ba da mukamin siyasa, bai kamata a ba mutumin da yake da sha’awar tsayawa takara ba, don ba zai yi adalci ba.
Kuma an zarge ni cewa ina surutun banza ne a kasa, ban taba cin zabe a garinmu b, to, ga ’yata ta je garin wadansu ta ci. Kuma ’yar tawa da ake zargin PDP sun ba ni goro, sun yi kokari su kwace mata zaben a wurin kirge, har sai da aka naushi wata ASP mace ta fadi warwas ta suma. Yanzu haka PDP sun kai ta kotu ba ni da kudin biyan lauya, don Allah ku da kuke ganin PDP ta ba ni tsohiya, ku gaya musu su janye karar da suka kai ’yata, ko su ba ni kudin da zan biya lauya.
Aminiya: A baya ka ce an tsare ka saboda Janar Buhari, kuma ga alama ka nuna mutane suna kai maganganu wajen Buhari, inda yake yanke hukunci ba tare da ya yi bincike ba. Shi ma wannan na daga cikin dalilan da suka sa ka janye daga siyasa?
Buba Galadima: A’a, a’a. In kana son ka ji wannan sai ka tambayi Janar Buharin, ko ya yarda ko bai yarda ba, ni ba zan iya sani ba.
Aminiya: A bangarenka kana ganin irin wadannan abubuwa suka daga ciki?
Buba Galadima: Shi bai kira ni ya ce, an ce da ni kaza-kaza a kanka ba, shin gaskiya ne? Bai taba kirana ba, gara mu yi masa adalci. Na biyu, bai taba kirana ya kira wanda ya zarge ne ya zaunar da mu ya ce, sake fadar abin da ka fada game da wane ba, don ya gyara tsakaninmu, bai taba yin haka ba. Sai dai mu yi masa adalci cewa kila bai yarda ba ne. Yanayin shugabancin ya bambanta, domin in da ni ne ake kai kara irin wannan wurina, sai in kira mutanen in zaunar da su, in ce wane me ka ce, ga wanen a zaune. Ko kuma in kira wane tunda yana kasa da ni, in ce kai me ya sa ka yi kaza?
Zan ba ka misali, Allah Ya jikansu duka biyu, Ministana Janar Gumel ya kai karata ta ya ce na saci kudi a Hukumar Jiragen Ruwa, ya yi leja na inda aka dauki kudin ya dauki takarda ya kai wa Janar Abacha ya ce a kore ni ko dakatar da ni a ba wane, sai an gama bincike. Da ya kai bari ka ga shugabanci, da Janar Abacha ya karanta, sai ya kife takardar, ya ci gaba da abin da yake yi. Can sai Gumel ya ce, ina jira. Sai Abacha ya ce, Ibrahim, ni na nada ka, ni na nada Buba, ka kawo min kararsa, ka bari in yi bincike. Janar Abacha bai tashi nemana ba, sai bayan wata uku. Ba wanda ya san cewa mun yi rigima da Gumel har ya fito da bindiga zai harbe ni idan ban saki wannan kudi ba. Ya aika da wani soja mai taimaka masa ya tafi Landan don amsar kudin, sai Bature a bankin ya ce, kai hauka kake yi za mu ba ka, wannan kudi daloli. Ka shigo kana tsammanin nan Najeriya ne. Sai Babban Sakatare a Ma’aikatar Sufuri a lokacin ya bugu waya cewa Buba ya hada baki da manajan bankin an hana kudin. Gumel ya kira ni yana ajiye da bindiga kamar zai harbe ni. Baturen ya ce, kudin ba zai dauku ba, sai an ba da asusun ajiya. Sai Gumel ya ba da asusunsa na Switzsland aka sa masa kudin. Ni kuma a matsaina na Babban Darakta ba ni da hurumin fitar da kudin da ya haura Naira miliyan biyar, wannan kudi ma kwamiti ne ya amince a fitar da sunan za a yi aiki. Abin da ya sa na gagara ke nan, Obasanjo ya bincike ne har sau takwas, duk da ana cewa ni dan PDP ne, amma bai same ni da laifi kansa ba. To ana aikawa da kudin manajan bankin ya aika wa ofishin tuntubar Najeriya a Landan, lokacin da aka aika da kudin da asusun da aka aika da kudin, sai ya ce, masa wannan zai yi muku amfani wani lokaci. Shi kuma jami’in ofishin sai ya ce in bude fas dina zai aikomin takarda, ni yake so in dauka kada wani ya dauka. Na sa ina tsaye a kai, ya aiko da takardar, ya ce manajan banki ya ce, wannan zai yi maka amfani wai lokaci. To da na ji labarin yadda Gumel suka yi da Abacha, sai na dauki wannan takarda da suka aiko daga ma’aikatar sufuri na hada da wannan. Kullum takardar tana aljihuna, yau ne gobe ne Abacha zai kira ni bai kira ba, sai bayan wata uku.
Janar Abacha ya aiko Kanar Abdallah yana nan da ransa yana aiki da Janar Buhari cewa a kirawo ni. Daga cewa a kirawo ni sai gabana ya fadi, na dauki takardar na sa a aljihuna. Sai na tambayi Kanar Abdallah cewa akwai wani abu da ya ce idan zan zo in zo da shi, ko ya gaya maka wata magana don kada in zo a nemi abin babu? Sai ya ce da can da kake zuwa wurinsa ni nake gaya maka abin da za ka kawo ko maganar da ta sa ya kira ka? Ina zuwa na je wurinsa (Kanar Abdallah) ya ce ka hau. Wasu Janar-Janar ciki har Gumel suna jira ba wanda Abacha ya gan shi, na hau wurinsa. Kamar su kashe ni, ga su Janar-Janar sun sha jan wuya, ga wani farar hula wanda ba komai ba ya zo Shugaban kasa ya ce ya hau wurinsa. Shi ya sa da su Abdulsalam suka hau gwamnati, aka je ana gaya musu cewa ni ne gaba daya nake tafiyar da harkokin siyasar Najeriya, saboda haka ni ne, babban mai laifi. Jam’iyyar UNCP suka shigar da wannan a karkashin Alhaji Isa Mohammed na garin Madi.
Da na hau wurin Abacha na tsaya bai daga kai ba, sai na ja kujera na zauna. Sai ya ce, wa ya ce ka zauna? Sai na tashi, ya bata rai. Ya ce da ni Buba, ka san dalilin da ya sa na kai ka wannan wuri kuwa? Na ce ban sani ba ranka ya dade. Ya ce, duniya, wato mutane na canjawa. Na tabbata ko ranstuwa zan yi da Alkur’ani cewa in an ba ka kudin jama’a ba za ka taba ba. Saboda aikin da na yi a Fatakwal lokacin Janar Zamani Lekwot na Gwamna Janar Abacha yana Birged Kwamnda ni ne na uku a gwamnatin jihar, akwai wasu kudi na musamman da Gwamnatin Tarayya ta aika Naira miliyan 300 daidai da Dalar Amurka miliyan biyar a lokacin, ni nake kula da su. Abacha ya san ni, sai ya ce ka yi sata? Ka ba ni kunya. Na ce wane irin sata ne ranka ya dade? Ya ce, wasa ma kake yi da ni? Ya bata rai, ya ce, rana kaza, lokaci kaza ba ka saci kaza ba? Na ce da shi ranka ya dade na sata. Sai jikinsa ya yi sanyi ya koma ya zauna a kan kujera, ya ce in zauna. Sai na sa hannu a aljihu na ciro wannan takarda na mika masa. Da ya gani, ya dora hannu a baki. Gumel ne ya sa wani mataimaki na musamman ga babban sakataren ma’aikatar na lokacin ya rubuta min wannan takarda cewa akwai wani aiki na tsaro da za a yi saboda haka a ba da Dala kaza. Kuma dalolin ga inda suka shiga asusun kashin kai na Janar Gumel a Switzland. To mutumin da ya ga akwai ya ga babu irina wanda duk inda na yi aiki a bangaren kudi ne, daga injiniyan aiki, sai sakataren kwamiti a Ribas, sai injiniyan yanki a Maiduguri sai injiniyan kula da gari a Maiduguri. Ni na fara tagwayen hanya a nan Arewa a Maiduguri. Na yi babban injiniya a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, darakta a kamfanin karafa na Delta, darakta a kamfanin karafa na Ajaokuta shekara bibbiyu, darakta a bankuna da sauransu. Sakataren Kudi na Jam’iyyar NRC, lokacin da Janar Babangida ya ba mu kudi kamar za ka yi kwallo da su, saboda sun yi yawa ba mu san yadda za mu yi da su ba. Na yi Darakta Janar na Hukumar Jiragen Ruwa, duk wadannan ban ci kudin jama’a ba, ko ban ci amana ba, sai a wadannan shekarun fiye da 60. In ana neman mai gaskiya a Najeriya zan fara cire kaina daga wadanda ake zugawar nan. Na fi su rikon amana da tsare gaskiya. In kuma ba haka ba, ko makiyina ya isa ya san cewa in ba ni da kwatankwacin gaskiya ban isa in rika maganganun da nake yi ba.
Aminiya: Idan ka yunkuro, wace jam’iyya za ka shiga?
Buba Galadima: Ai ina da jam’iyya. Ba ku san ina da jam’iyya ba. To, duk mutumin da ya yi ANPP ko Gwamna ko dan majalisa ko shugaban karamar hukuma ko wani abu, ina da lada a ciki. Domin ni da Shinkafi a kasar nan mu ne muka gi ba da gudunmawa wajen kafa Jam’iyyar APP har ta zama ANPP. Haka duk wanda ya samu wani ko ya zama wani abu ko yayi wani abu, Buba Galadima yana da kamasho a ciki. Domin da ni da Sule Hamma ba mu kawo shawarar a kafa jam’iyyar ba, da bai samu abin ba, ko da bai aikata ashhar ba, don haka ni da Sule Hamma muna da kamasho a ciki. Kuma ko mutum yana so, ko ba ya so hadaka aka yi na jam’iyyu ANPP, ACN da CPC, wadanda suka yi unguzomar hadakar suka sa hannu aka kai wa INEC na a yi hadakar a kafa APC da Buba Galadima a ciki. Saboda haka ba na gudu in bar ladana, nid an Jam’iyyar APC ne ka san ba zan shiga PDP ba, saboda babu dan Adam da yake Najeriya da yake da abin da zai ba ni ya sayi ra’ayina. Kuma duk wanda ya san ni, ya san cewa Buba Galadima dattijo ne mai magana daya, babu mutumin da ya isa ya hana shi abin da ya tunkara ya sa a gabansa. Saboda haka nid an APC ne, amma idan aka kasa abubuwa a tebur ’yan neman mukamai suka fito a yanzu ban san wanda zan yi ba, sai wanda hankalina ya dauka.
Buba Galadima ne sanadi. Don ni na ba shi damar da ya je taron tsarin mulki, na ba shi damar da ya samu kudi ya tsaya takarar Gwamna. Ta hanyarsa, sakataren gwamnatinsa, Cif Rufus Ada George muka saba da shi, ya tsaya zabe da Cif Zack Abule, Shugaban Bankin Crystal Bank, ya ba shugabanin Jam’iyyar NRC kudi, ba na son in fadi ko nawa ne, suka ba shi takara. Ni kadai na ce ban yarda ba, aka tafka rigima, Shinkafi yana da rai, Babangida yana da rai. Muka je muka ga Janar Abacha, cewa ga halin da ake ciki, muka sa aka haramta takarar Abule. Muka sa aka yi doka a cikin awa 24 aka ce idan aka soke dan takara wanda aka yi firamare ya zo na biyu, shi ne zai zama dan takarar jam’iyya. Mu muka yi wannan a lokacin da kwai yake da gashi, muka sa Ada George ya zama Gwamna. Abubakar Musa Yawuri an kada shi a zabe da magudi, ni na tsaya tsayin-daka sai da aka ba shi takarar ya zama Gwamna. Peter Odili da kake gani a kofar gidana yake kwana, ni na taimaka masa da Ada George din har ya zo ya zama Gwamna. Duk mutanen nan da na kirga maka ko Clement Ebiri, babu mutumin da na taimaka masa ya zama Gwamna daga baya na tashi takanas- ta-Kano na je wurinsa cewa tunda na taimaka masa don Allah Ya ba ni masauki, in sauka a gidan gwamnati, ban taba yi ba.
Dadin dadawa, Jam’iyyar CPC ce ta kafa gwamnati a Jihar Nasarawa. Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Jega ya rubuta takarda shafi hudu ga Sufeto Janar na ’Yan sanda cewa mun canja dan takarar Gwamna a Nasarawa. Saboda haka, a kama mu a kulle mu, don irin labaran da PDP suka gaya masa. Babu binciken duniya da ba a yi mana ba, ni da Yarima Tony Momoh, Allah Ya kubutar da mu daga wannan wulakanci, shiryayye. Abin da nake son na gaya maka shi ne, tun lokacin da aka ce Al-Makura ya ci zaben Gwamna, aka je rantsar da shi, ya yi bikin shekara daya, ya yi bikin shekara biyu yana kan mulki, ban taba taka Nasarawa ba, sai sau daya lokacin da ’ya’yansa suka yi hadari wasu suka rasu, na je yi masa ta’aziyya. Kuma Al-Makuran nan, ya ba ni ginin firamare na UBE na Naira miliyan bakwai, aka zo a Majalisar koli ta jam’iyarmu, uwaka, ubanka aka zarge ni cewa na kewaya ta baya ina karbar kwangila a wurin Gwamna. Alhali a jarida na ga an sa tandar kwangilar ta UBE, na nema aka ba ni rukunin aji daya kan Naira miliyan bakwai. Ina Sakataren Jam’iyya ta kasa, koda Naira miliyan bakwai kacokan Al-Makura ya ba ni, me ya yi, in ban da matsiyata? Balle kwangila ce, to, yanzu na yi kwangilar kudina Naira miliyan uku sun makale yau wata hudu ban samu ba, amma fa zagin ubana aka yi, ana zargina ana cewa kaza-kaza. To na gode wa Allah da ’yata ta kai shekara 30 ta yi aure ta kai munzilin shiga siyasa, har ta ci ta zama kansila
A jiya wani daga cikin ma’aikatanku ma ya tambaye ni ko wannan zabe da aka bar ’yarka ta ci, bayan ba a bar kowa ba, yana daga cikin cin hanci da PDP ta ba ka? Na ce, ita yarinyar ta yi aiki ta gaji mahaifinta. A kowane akwati ta ajiye mutum 37 masu tsare mata kuri’a don kada a yi mata magudi. Mutane tun daga Kebbi, Sakkwato, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Filato, Kaduna, Nasarawa, Kogi, Neja, duk sun kawo gudunmawa don taimaka mata. Wadansu akwatunan masu tsare mata akwatin sun fi wadanda suka fito jefa kuri’ar. Wato wadansunmu na kiran kanmu ’yan siyasa amma ba mu da idanuwa na gani ko kunnuwa na ji a siyasance. A wurina in ana ba da mukamin siyasa, bai kamata a ba mutumin da yake da sha’awar tsayawa takara ba, don ba zai yi adalci ba.
Kuma an zarge ni cewa ina surutun banza ne a kasa, ban taba cin zabe a garinmu b, to, ga ’yata ta je garin wadansu ta ci. Kuma ’yar tawa da ake zargin PDP sun ba ni goro, sun yi kokari su kwace mata zaben a wurin kirge, har sai da aka naushi wata ASP mace ta fadi warwas ta suma. Yanzu haka PDP sun kai ta kotu ba ni da kudin biyan lauya, don Allah ku da kuke ganin PDP ta ba ni tsohiya, ku gaya musu su janye karar da suka kai ’yata, ko su ba ni kudin da zan biya lauya.
Aminiya: A baya ka ce an tsare ka saboda Janar Buhari, kuma ga alama ka nuna mutane suna kai maganganu wajen Buhari, inda yake yanke hukunci ba tare da ya yi bincike ba. Shi ma wannan na daga cikin dalilan da suka sa ka janye daga siyasa?
Buba Galadima: A’a, a’a. In kana son ka ji wannan sai ka tambayi Janar Buharin, ko ya yarda ko bai yarda ba, ni ba zan iya sani ba.
Aminiya: A bangarenka kana ganin irin wadannan abubuwa suka daga ciki?
Buba Galadima: Shi bai kira ni ya ce, an ce da ni kaza-kaza a kanka ba, shin gaskiya ne? Bai taba kirana ba, gara mu yi masa adalci. Na biyu, bai taba kirana ya kira wanda ya zarge ne ya zaunar da mu ya ce, sake fadar abin da ka fada game da wane ba, don ya gyara tsakaninmu, bai taba yin haka ba. Sai dai mu yi masa adalci cewa kila bai yarda ba ne. Yanayin shugabancin ya bambanta, domin in da ni ne ake kai kara irin wannan wurina, sai in kira mutanen in zaunar da su, in ce wane me ka ce, ga wanen a zaune. Ko kuma in kira wane tunda yana kasa da ni, in ce kai me ya sa ka yi kaza?
Zan ba ka misali, Allah Ya jikansu duka biyu, Ministana Janar Gumel ya kai karata ta ya ce na saci kudi a Hukumar Jiragen Ruwa, ya yi leja na inda aka dauki kudin ya dauki takarda ya kai wa Janar Abacha ya ce a kore ni ko dakatar da ni a ba wane, sai an gama bincike. Da ya kai bari ka ga shugabanci, da Janar Abacha ya karanta, sai ya kife takardar, ya ci gaba da abin da yake yi. Can sai Gumel ya ce, ina jira. Sai Abacha ya ce, Ibrahim, ni na nada ka, ni na nada Buba, ka kawo min kararsa, ka bari in yi bincike. Janar Abacha bai tashi nemana ba, sai bayan wata uku. Ba wanda ya san cewa mun yi rigima da Gumel har ya fito da bindiga zai harbe ni idan ban saki wannan kudi ba. Ya aika da wani soja mai taimaka masa ya tafi Landan don amsar kudin, sai Bature a bankin ya ce, kai hauka kake yi za mu ba ka, wannan kudi daloli. Ka shigo kana tsammanin nan Najeriya ne. Sai Babban Sakatare a Ma’aikatar Sufuri a lokacin ya bugu waya cewa Buba ya hada baki da manajan bankin an hana kudin. Gumel ya kira ni yana ajiye da bindiga kamar zai harbe ni. Baturen ya ce, kudin ba zai dauku ba, sai an ba da asusun ajiya. Sai Gumel ya ba da asusunsa na Switzsland aka sa masa kudin.
Ni kuma a matsaina na Babban Darakta ba ni da hurumin fitar da kudin da ya haura Naira miliyan biyar, wannan kudi ma kwamiti ne ya amince a fitar da sunan za a yi aiki. Abin da ya sa na gagara ke nan, Obasanjo ya bincike ne har sau takwas, duk da ana cewa ni dan PDP ne, amma bai same ni da laifi kansa ba. To ana aikawa da kudin manajan bankin ya aika wa ofishin tuntubar Najeriya a Landan, lokacin da aka aika da kudin da asusun da aka aika da kudin, sai ya ce, masa wannan zai yi muku amfani wani lokaci. Shi kuma jami’in ofishin sai ya ce in bude fas dina zai aikomin takarda, ni yake so in dauka kada wani ya dauka. Na sa ina tsaye a kai, ya aiko da takardar, ya ce manajan banki ya ce, wannan zai yi maka amfani wai lokaci. To da na ji labarin yadda Gumel suka yi da Abacha, sai na dauki wannan takarda da suka aiko daga ma’aikatar sufuri na hada da wannan. Kullum takardar tana aljihuna, yau ne gobe ne Abacha zai kira ni bai kira ba, sai bayan wata uku.
Janar Abacha ya aiko Kanar Abdallah yana nan da ransa yana aiki da Janar Buhari cewa a kirawo ni. Daga cewa a kirawo ni sai gabana ya fadi, na dauki takardar na sa a aljihuna. Sai na tambayi Kanar Abdallah cewa akwai wani abu da ya ce idan zan zo in zo da shi, ko ya gaya maka wata magana don kada in zo a nemi abin babu? Sai ya ce da can da kake zuwa wurinsa ni nake gaya maka abin da za ka kawo ko maganar da ta sa ya kira ka? Ina zuwa na je wurinsa (Kanar Abdallah) ya ce ka hau. Wasu Janar-Janar ciki har Gumel suna jira ba wanda Abacha ya gan shi, na hau wurinsa. Kamar su kashe ni, ga su Janar-Janar sun sha jan wuya, ga wani farar hula wanda ba komai ba ya zo Shugaban kasa ya ce ya hau wurinsa. Shi ya sa da su Abdulsalam suka hau gwamnati, aka je ana gaya musu cewa ni ne gaba daya nake tafiyar da harkokin siyasar Najeriya, saboda haka ni ne, babban mai laifi. Jam’iyyar UNCP suka shigar da wannan a karkashin Alhaji Isa Mohammed na garin Madi.
Da na hau wurin Abacha na tsaya bai daga kai ba, sai na ja kujera na zauna. Sai ya ce, wa ya ce ka zauna? Sai na tashi, ya bata rai. Ya ce da ni Buba, ka san dalilin da ya sa na kai ka wannan wuri kuwa? Na ce ban sani ba ranka ya dade. Ya ce, duniya, wato mutane na canjawa. Na tabbata ko ranstuwa zan yi da Alkur’ani cewa in an ba ka kudin jama’a ba za ka taba ba. Saboda aikin da na yi a Fatakwal lokacin Janar Zamani Lekwot na Gwamna Janar Abacha yana Birged Kwamnda ni ne na uku a gwamnatin jihar, akwai wasu kudi na musamman da Gwamnatin Tarayya ta aika Naira miliyan 300 daidai da Dalar Amurka miliyan biyar a lokacin, ni nake kula da su. Abacha ya san ni, sai ya ce ka yi sata? Ka ba ni kunya. Na ce wane irin sata ne ranka ya dade? Ya ce, wasa ma kake yi da ni? Ya bata rai, ya ce, rana kaza, lokaci kaza ba ka saci kaza ba? Na ce da shi ranka ya dade na sata. Sai jikinsa ya yi sanyi ya koma ya zauna a kan kujera, ya ce in zauna. Sai na sa hannu a aljihu na ciro wannan takarda na mika masa. Da ya gani, ya dora hannu a baki. Gumel ne ya sa wani mataimaki na musamman ga babban sakataren ma’aikatar na lokacin ya rubuta min wannan takarda cewa akwai wani aiki na tsaro da za a yi saboda haka a ba da Dala kaza. Kuma dalolin ga inda suka shiga asusun kashin kai na Janar Gumel a Switzland. To mutumin da ya ga akwai ya ga babu irina wanda duk inda na yi aiki a bangaren kudi ne, daga injiniyan aiki, sai sakataren kwamiti a Ribas, sai injiniyan yanki a Maiduguri sai injiniyan kula da gari a Maiduguri. Ni na fara tagwayen hanya a nan Arewa a Maiduguri. Na yi babban injiniya a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, darakta a kamfanin karafa na Delta, darakta a kamfanin karafa na Ajaokuta shekara bibbiyu, darakta a bankuna da sauransu. Sakataren Kudi na Jam’iyyar NRC, lokacin da Janar Babangida ya ba mu kudi kamar za ka yi kwallo da su, saboda sun yi yawa ba mu san yadda za mu yi da su ba. Na yi Darakta Janar na Hukumar Jiragen Ruwa, duk wadannan ban ci kudin jama’a ba, ko ban ci amana ba, sai a wadannan shekarun fiye da 60. In ana neman mai gaskiya a Najeriya zan fara cire kaina daga wadanda ake zugawar nan. Na fi su rikon amana da tsare gaskiya. In kuma ba haka ba, ko makiyina ya isa ya san cewa in ba ni da kwatankwacin gaskiya ban isa in rika maganganun da nake yi ba.
Aminiya: Idan ka yunkuro, wace jam’iyya za ka shiga?
Buba Galadima: Ai ina da jam’iyya. Ba ku san ina da jam’iyya ba. To, duk mutumin da ya yi ANPP ko Gwamna ko dan majalisa ko shugaban karamar hukuma ko wani abu, ina da lada a ciki. Domin ni da Shinkafi a kasar nan mu ne muka gi ba da gudunmawa wajen kafa Jam’iyyar APP har ta zama ANPP. Haka duk wanda ya samu wani ko ya zama wani abu ko yayi wani abu, Buba Galadima yana da kamasho a ciki. Domin da ni da Sule Hamma ba mu kawo shawarar a kafa jam’iyyar ba, da bai samu abin ba, ko da bai aikata ashhar ba, don haka ni da Sule Hamma muna da kamasho a ciki. Kuma ko mutum yana so, ko ba ya so hadaka aka yi na jam’iyyu ANPP, ACN da CPC, wadanda suka yi unguzomar hadakar suka sa hannu aka kai wa INEC na a yi hadakar a kafa APC da Buba Galadima a ciki. Saboda haka ba na gudu in bar ladana, nid an Jam’iyyar APC ne ka san ba zan shiga PDP ba, saboda babu dan Adam da yake Najeriya da yake da abin da zai ba ni ya sayi ra’ayina. Kuma duk wanda ya san ni, ya san cewa Buba Galadima dattijo ne mai magana daya, babu mutumin da ya isa ya hana shi abin da ya tunkara ya sa a gabansa. Saboda haka nid an APC ne, amma idan aka kasa abubuwa a tebur ’yan neman mukamai suka fito a yanzu ban san wanda zan yi ba, sai wanda hankalina ya dauka