Buhari na bukatar addu’a – Oladipo Diya
Tsohon Babban Hafsa a Fadar Shugaban kasa Janar Oladipo Diya ya ce zavavven Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suna bukatar addu’o’i domin samun nasarar mulkinsu. Don haka ya bukaci ’yan Najeriya su yi ta yi wa Buhari da Osinbajo addu’o’i, inda ya ce mutanen biyu suna bukatar Allah Ya tallafa musu […]
Tsohon Babban Hafsa a Fadar Shugaban kasa Janar Oladipo Diya ya ce zavavven Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suna bukatar addu’o’i domin samun nasarar mulkinsu.
Don haka ya bukaci ’yan Najeriya su yi ta yi wa Buhari da Osinbajo addu’o’i, inda ya ce mutanen biyu suna bukatar Allah Ya tallafa musu wajen yaki da cin hanci da rashawa a Nejriya ba tare da an yi musu kafar ungulu ba.
Janar Diya ya ce mutanen biyu, mutane ne masu mutunci da amana, wadanda aka zave su su mulki Najeriya a tsakanin gurvatattun dimbin ’yan siyasa.
Diya ya ce: “Na yi aiki a karshinsa (Buhari) a matsayin Gwamna lokacin da yake Shugaban Gwamnatin Soja kuma Babban Kwamandan Asakarawan Najeriya. Kuma lokacin da nake Mataimakin Shugaban Gwamnatin Mulkin Soja ko Babban Hafsa a Fadar Shugaban kasa, mun nada shi Shugaban Asusun Rarar Man Fetur (PTF), ya ba mu ka’idoji kafin ya karvi aiki, cewa zai yi aiki amma ba a karkashin wani ba kuma muka amince. A karshe ya yi aiki mai kyau kuma ba mu same shi da cin amana ba, don haka zan iya bugun kirji kan nagartarsa a kowane lokaci.”
Janar Diya ya kara da cewa: “Abubuwa kamar alawus din kwamanda da kudin tsaro duk an dakatar da su. Babu Gwamnan soja da zai fita wajen kasar nan ko ya bayar da wata kwangila ba tare da samun amincewar Babban Hafsan Majalisar koli ba, wanda shi kuma yake samun umarni daga Babban Kwamandan Askarawan Sojan kasar nan. Kai babu ma Gwamnan Soja da aka yarda ya yi tafiya wajen Afirka.”
Ya bayyana cewa wadanda suka yi wa Buhari juyin mulki a matsayin Shugaban kasa mutane ne masu almundahana wadanda ba su gamsu da kudirinsa na yaki da almundahana.
Janar Diya ya nuna tsoron cewa akwai babban kalubale a gaban Buhari wajen yaki da cin hanci da rashawa da almundahana a karkashin tsari irin na dimokuradiyya.
Ya nanata cewa ’yan siyasa da dama a kasar nan suna da wani imani na suna neman mulki ne domin tara dukiya.
Tsohon Janar din ya ce idan ’yan Najeriya suka tashi haikan ne wajen yi wa Buhari da mukarrabansa addu’a, gwamnatin za ta samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa ta yadda kasar nan za ta samu ci gaba.
Janar Buhari dai ya yi wa ’yan alkawarin samun canji nagari, duk da cewa ya bukace da kada su sa ran samun sakamakon nan take daga sabuwar gwamnatinsa idan ta kama aiki a ranar 29 ga Mayu.