Buhari na ganawa da Daliban Kankara a Katsina

Shugaban Kasa na ganawa da yaran aka yi garkuwa da su a ranar da suka dawo Katsina. 

Buhari na ganawa da Daliban Kankara a Katsina

Daliban Kankara suna sauraron jawabi bayan an dawo da su Katsina. (Tsohuwar ajiya).

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ganawa da daliban Makarantar Sakandaren GSSS Kankara, Jihar Katsina da suka shaki isakar ’yanci bayan makonsu guda a hannun masu garkuwa da mutane. 

Hadimin Shugaba Kansa kan Kafafan Sadarwa na Zamani, Bashir Ahmad ya sanar cewa: “Shugaban Buhari zai gana da daliban GSSS Kankara a yammacin Juma’a a Jihar Katsina.”

Ganawar ta su da daliban tana zuwa ne washegarin ranar da ’yan bindigar sun sake su bayan sun sun yi awon gaba da su a makon jiya.

Tunda farko Buhari ya bayyana farin cikinsa da sakin su da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata, 11 ga watan Disambar 2020.

“Ina maraba da sakin daliban Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kankanra. Hakika sakin su zai kwantar da hankalin jama’ar kasar nan kwarai da gaske da ma duniya baki daya.

“Al’umar kasar nan na cike da farin ciki bisa kwazo da namijin kokarin da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya nuna tare da hukumomin tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda da masu tara bayanan sirri,” inji Shugaba Buhari.

Buhari, ya yi bikin cikarsa shekara 78 a mahaifarsa da ke garin Daura, Jihar Katsina a wata ziyara ta musanman da ya kai garin.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta