Buhari na ganawar sirri da Gwamnonin APC biyar
A yanzu haka Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na ganawar sirri da Gwamnonin jam’iyyar APC biyar. Mai taimakawa shugaban na musamman kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a yau Laraba Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo sun gana da Gwamnonin da suka hada da: Gwamnan Kano Abdullahi Gamduje […]
A yanzu haka Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na ganawar sirri da Gwamnonin jam’iyyar APC biyar.
Mai taimakawa shugaban na musamman kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a yau Laraba
Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo sun gana da Gwamnonin da suka hada da: Gwamnan Kano Abdullahi Gamduje da Gwamnan Borno Kashim Shettima da Gwamnan Bauchi Muhammed Abubakar da Gwamnan Imo Rochas Okorocha da Gwamnan Legas Akinwunmi Ambode a fadar shugaban kasar.
Cikakken rahoton na nan tafe.