Buhari na jagorantar Taron Majalisar Zartarwa na Kasa
Taron farko bayan nasa sabbin Manyan Hafsoshin tsaro.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Kasa, karo na 32 ta bidiyo.
Taron na ranar Laraba shi ne na farko bayan Shugaba Buhari ya nada sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro, kuma kwana biyu bayan cikar wa’adin Shugaban Rundunar ’Yan Sanda.
- Yadda za ki sa namiji ya nutse cikin kaunar ki
- Harin ’yan bindiga ya sa mutane kaura a Zariya
- Kai wa Fulani hari ba zai haifar wa da Najeriya da mai ido ba —Bashir Tofa
- Dogo Gide: Mutumin da ya hallaka Buharin Daji
Zaman na ranar Laraba ya yi shiru na minti daya domin juyayin rasuwar tsoffin ’yan Majalisar Zartarwa ta Tarayya biyu da suka kwanta dama; Alhaji Alfa Wali da kuma Prince Tony Momoh.
Alhaji Alfa Wali, tsohon Ministan Noma ne kuma tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro da sauransu, ya rasu ne a ranar Litinin 25 ga Janairu, 2021.
Shi kuma Prince Tony Momoh, tsohon Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, ya rasu ne ranar Litinin 1 ga watan Fabrairu, 2021, yana da shekara 82.
Mahalarta taron su hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Mashawarci kan Tsaron Kasa, Babagana Mongunu da wasu ministoci bakwai.
Ministocin da suka halarci zaman sun hada da Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed; Minsitan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Raya Albarkatun Kasa, Olamilekan Adegbite; da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Sauran su ne Ministan Ma’adinai, Niyi Adebayo; Ministan Ilimi, Adamu Adamu; da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.
Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan da sauran Ministocin kuma suna halartar zaman ne ta bidiyo daga ofisoshinsu a Abuja.