Buhari na kokarin samo Dala biliyan 50 don farfado da Tafkin Chadi – Shugaban Bankin Afirka
Shugban Bankin Raya Afirka (AfDB) Dokta Akinwunmi Adesina ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi maraba da amincewar da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutterres ya kasance shugaban hadin gwiwa a taron neman Dala biliyan 50 don jawo ruwa daga tafkunan Afirka ta Tsakiya saboda a sake farfado da Tafkin Chadi. Shugaban Bankin Raya […]
Shugban Bankin Raya Afirka (AfDB) Dokta Akinwunmi Adesina ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi maraba da amincewar da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutterres ya kasance shugaban hadin gwiwa a taron neman Dala biliyan 50 don jawo ruwa daga tafkunan Afirka ta Tsakiya saboda a sake farfado da Tafkin Chadi.
Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB) Dokta Akinwumi Adesina, wanda ya bayyana amincewar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ga Shugaba Buhari a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a shekaranjiya Laraba ya kuma ziyarci babban ofishin jaridun Daily Trust da Aminiya inda ya yi karin bayani a kan yunkurin.
Adesina ya ce Shugaban Kasar ya bikaci Bankin Raya Afirka (AfDB) kan ya jagoranci ayarin masu nemo kudin don farfado da tafkunan don aikin jawo ruwan, inda ya bayyana shi da mai muhimmanci lura da girman aikin da ake bukata a Tafkin na Chadi.
Aminiya ta gano cewa kasashe hudu na yankin Tafkin Chadi wato Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru suna faman yaki da ayyukan ta’addanci na Boko Haram. Kuma dubban mazauna yankin da suke gudanar da harkokin rayuwarsu a gabar Tafki Chadi sun rasa madogara ga rayuwarsu sakamakon kafewar tafkin, lamarin da ya dada habakar matsalar ayyukan ta’addanci a yankin.
Dokta Adesina ya bayyana ma ayarin Shugabannin Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya a karkashin jagorancin Shugaban Hkumar Gudanarwar Kamfanin Malam Kabiru A. Yusuf da Babban Edita kuma Jami’in Zartarwar Kamfani Malam Mannir Dan Ali cewa, “Shugaban Kasa yana yin wani kokari a kanTafkin Chadi. Wanda a ganina ya kamata a yaba masa. Idan aka kalli Tafkin Chadi zaa ga a da yana da fadin murabba’in kilomita dubu 25. Amma a yau duka-duka yana da daya bisa goma ne na abin da yake da shi a baya.”
Shugaban Bankin na AfDB ya ce mafi yawan matsalolin da ake samu yanzu a kasar nan sun samo asali ne daga kafewar Tafkin Chadi.
“Shugaba Buhari yana jagorantar wani babban yunkuri na jawo ruwa daga kasar Kwango zuwa Tafkin Chadi. Kuma ya umarce ni in tallafa wajen samo kudi Dala biliyan 50, kuma na karbi wannan aiki da hannu bibbiyu. Domin kuwa idan babu zaman lafiya babu yadda za a yi a samu ci gaba kuma ba wani mai zuba jari da zai zo ya sanya jarinsa. Ba za mu samu komai ba,” inji shi.
Kwararren ta fannin bunkasa harkokin kudi, ya ce Bankin AfDB ya damu kwarai da halin da ake ciki yanzu a yankin Arewa maso Gabas, don haka yana aiki kafada-da-kadada da Shugaba Buhari don sake farfado da yankin. Ya ce Bankin AfDB ya yi niyyar ba da Dala miliyan 280 don sake raya wannan yanki a bangaren samar da ruwa da tsabtace muhalli da kuma koyar da sana’o’i.
Dokta Adesina ya yaba wa jaridun kamfanin Daily Trust, inda ya ce jaridu ne da akullum suke bayyana gaskiya ga shugabannin wanda ba a cika samun haka ba.
Ya ce yana lura da yadda jaridun kamfanin suke sake fasali a shekara da shekaru akasari wajen gudanar da aikin jarida mai sahihanci. “Ina matukar taya jaridun kamfanin Daily Trust murna. Jardidu ne masu aminci da amana. Kuma ina lura da su shekara da shekaru kan fannonin da kuke bayar da labarai a kai da yadda kuke bayarwa da yadda kuke buga labarai masu hujja wadanda suke labarai ne na gaskiya sahihai,” inji shi.