Buhari na neman amincewar Majalisa kan Dongban-Mensem

Shugaba Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa takardar neman amincewarta ya tabbatar da nadin Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem a Matsayin cikakkiyar Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya. Majalisar ta tabbatar da samun takardar Shugaba Buhari na neman nada Mai Shari’a Dongban-Mensem, wadda ita ce mukaddashin Shugaban Kotun a yanzu. Shugaban Majalisar Ahmad Lawan ya karanta […]

Buhari na neman amincewar Majalisa kan Dongban-Mensem

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne ”yan Najeriya su tsaya tsayin daka su ga karshen coronavirus

Shugaba Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa takardar neman amincewarta ya tabbatar da nadin Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem a Matsayin cikakkiyar Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya.

Majalisar ta tabbatar da samun takardar Shugaba Buhari na neman nada Mai Shari’a Dongban-Mensem, wadda ita ce mukaddashin Shugaban Kotun a yanzu.

Shugaban Majalisar Ahmad Lawan ya karanta wasikar Shugaban Kasar a zaman Majalisar na ranar Talata.

“Ina neman yardar Majalisa domain nada Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem ta zama Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya, kamar yadda doka ta tanadar.

“Ina fata Majalisa za ta duba tare da amincewa da wannan bukatar a kan kari”, inji wasikar.

A ranar Litinin ne Fadar Shugaban Kasa ta sanar da cewa Buhari na neman ba wa Dongban-Mensem cikakken iko a Kotun.