Buhari na neman mulki ne don amfanin Najeriya – Babagoro Mu’azu
Wani tsohon Kwanturola a Kamfanin Man fetur na Najeriya (NNPC), wanda ya yi takarar Sanata a Gombe ta Arewa a Jam’iyyar CPC a shekarar 2011 Alhaji Babagoro Mu’azu ya ce Janar Muhammadu Buhari na neman mulki ne don amfanin ’yan Najeriya da ita kanta Najeriyar amma ba don amfanin kansa ba. Alhaji Babagoro Mu’azu, ya […]
Wani tsohon Kwanturola a Kamfanin Man fetur na Najeriya (NNPC), wanda ya yi takarar Sanata a Gombe ta Arewa a Jam’iyyar CPC a shekarar 2011 Alhaji Babagoro Mu’azu ya ce Janar Muhammadu Buhari na neman mulki ne don amfanin ’yan Najeriya da ita kanta Najeriyar amma ba don amfanin kansa ba.
Alhaji Babagoro Mu’azu, ya ce a wannan lokaci da siyasar kasar nan ta rikice kuma kasar kowa bai san halin da yake ciki ba, ya sa ’yan Najeriya masu kaunarta suka jajirce wajen neman canji da zai ba Janar Buhari damar zama Shugaban kasa a bana don ya ceto Najeriya da ’yan Najeriya daga halaka.
Alhaji Babagoro, ya bayyana haka ne a Gombe lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a lokacin da wata kungiyar Buhari Support Organisation, (BSO) ta kaddamar da asusun tallafa wa Janar Buhari da don ci gaba da gudanar da yakin neman zabensa.
dan siyasar ya ce duk wanda yake ganin idan ya zabi Buhari kamar ya yi masa alfarma ne, to, ya yi kuskure, ya dauka ya zabi Buhari ne don nema wa kansa da al’ummar kasarsa sauki na kangin da suka shiga, amma Buhari ba abin da ya rasa a rayuwa kuma ba alfarma aka yi masa ba.