Buhari na zaba duk da ya daure mijina – Lucy Onabanjo

Uwargidan Gwamnan Jihar Ogun a jamhuriya ta biyu, Lucy Onabanjo ta bayyana dalilan ta na zabar Shugaba Muhammadu Buhari duk da daure mijinta da ya taba yi bayan da soji suka kifar da mulkin farar hula a shekarar 1983. “Na san Muhammadu Buhari zai kawo kyawawan sauye-sauye, zai kuma yaki cin hanci da rashawa. Hakan […]

Buhari na zaba duk da ya daure mijina – Lucy Onabanjo
Buhari na zaba duk da ya daure mijina – Lucy Onabanjo

Uwargidan Gwamnan Jihar Ogun a jamhuriya ta biyu, Lucy Onabanjo ta bayyana dalilan ta na zabar Shugaba Muhammadu Buhari duk da daure mijinta da ya taba yi bayan da soji suka kifar da mulkin farar hula a shekarar 1983.

“Na san Muhammadu Buhari zai kawo kyawawan sauye-sauye, zai kuma yaki cin hanci da rashawa. Hakan ne ya sa na zabe shi a zaben da ya gabata. Lokacin da ya daure maigidana ya wuce ya kuma rage nasa. Ina yi wa Buhari fatan alkhairi.” A cewar Mama Lucy, a yayin da take tattaunawa da ’yan jarida a gidanta da ke Ijebu-Ode a Jihar Ogun.
A farkon makon nan ne ta cika shekaru 90 a duniya, amma duk da yawan shekarun nata tana cike da koshin lafiya; fatar jikinta na sheki, muryarta wasai, ganinta daram da taimakon madubin ido, kamar yadda Aminiya ta ankara.
Dattijiyar ta bayyana mijinta a matsayin dan jarida mai kwazo da kazar-kazar da yawan tafiye-tafiye, domin neman labarai wanda ya yi rubuce-rubuce da dama a kan illar cin hanci da rashawa a lokacin da yake bakin aiki. “In yau yana Sakkwato to gobe yana Zariya, a haka ya karade jihohin kasar nan kaf kafin daga bisani ya zama Gwamnan Jihar Ogun a 1983,” inji ta.