Buhari ne fatan matasan Arewa maso Gabas a 2019
Idan matasanmu na yankin Arewa maso Gabas suka yi kyakkyawan nazari kan yadda siyasar Najeriya kee tafiya, tabbas mu babu abin da za mu ce wa Allah sia godiya, da ya kawo mana dauki kan musifu da suka baibaye wannan yanki, inda Gwamnatin Buhari ta kawo mana dauki. Don haka fatan da muke yi Allah […]
Idan matasanmu na yankin Arewa maso Gabas suka yi kyakkyawan nazari kan yadda siyasar Najeriya kee tafiya, tabbas mu babu abin da za mu ce wa Allah sia godiya, da ya kawo mana dauki kan musifu da suka baibaye wannan yanki, inda Gwamnatin Buhari ta kawo mana dauki. Don haka fatan da muke yi Allah Ya taimaki Shugaba Muhammadu Buhari da Najeriya baki daya, kamar yadda muke fatan ya ci gaba da aiwatar da ,anyan ayyukan da ya faro, musamman kafa Hukumar inganta wannan yanki. Abin da kawai muke jira shi ne kowa ya bayar da gudunmuwarsa, ta yadda kasarmu za ta ci gaba.
Lallai matasanmu su yi dubi da idon basira kan romon dimokuradiyya, ta wajen samukamai daga jama’ar da ke wakiltar al’ummarmu da Najeriya baki daya. Sannan mu himmmatu wajen bayar da shawarwarin da za su kai kasar nan ga gaci, don dorewar dimokuradiyya da haccdin kan al’umma da kau ce wa fitintinun da ke kokarin tarwatsa kasa.
Editan Aminiya ka ba ni dama in kara jaddada goyon bayan mu “mu matasan Arewa maso gabas ma shugaban kasa muhammadu buhari, shi da gwamnatin sa akan aiyukan alkhairi da mukamai da yayi mana a yankin mu, musamman ma akan ai’yuka dama kula yankin mu na Arewa maso gabas ‘wurin bada kwangilan titonan mu da bamu mukamai a gwamnatin sa dama bada aikin wutan lantarki na manbila akan kudi sama da tiriliyan biyu da kawo dauki a harkan tsaro a wannan yanki namu, a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yau a Arewa maso Gabas, mun samu manya manyan mukamai a Gwamnatin Buhari, kamar irin su Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da Shugaban Rundunan Sojoji Tukur Burtai, da Shugaban Rundunar sojan sama Sadik Abubakar, ga kakakin majalisan wakilai Yakubu Dogara, ga shugaban hukumar zabe na kasa dan wannan yanki namu ne, ga aikin tonon man fetur a jihohin Bauchi da Borno ga shi yanzu haka Shugaba Buhari, ya saka hannu na kafa Hukumar raya wannan yanki namu na Arewa maso Gabas.
“Mu matasan Arewa maso Gabas da mu cigaba da bai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, goyon baya da hadin kai yau da kuma gobe da mu ba shi hadin kai, musamman ma a zaben shekarar 2019, domin mu ba mu taba samun gwamnatin da take kula da wannan yanki namu na Arewa maso Gabas kamar Gwamnatin Buhari ba.
Baya ga kuri’unmu, akwai bukatar mu wayar da kan al’umma dangane da dimbin alfanu da ke tattare da wannan gwamnati, musamman yakin da take yi da rashawa. Da zarar an shawo kan cin hanci da rashawa da fasakwauri da jabun magunguna da daukacin al’amuran da suka kasance zagon kasa ne ga tattalin arzikin kasar nan, matsalolinmu za su yi matukar raguwa. Allah ya taimaki mai taimako, mai gaskiya da rikon amana. Mutanen yankin Arewa maso Gabas ku taya shugaban kasa da addu’a da managartan shawarwari.
Manaja ya rubuto makalarsa daga Bauchi Unguwar Karofin Madaki, 08065189242.