‘Buhari ne talaka a cikin shugabannin Afirka’

Bayan da Kakakin Shugaban kasa Garba Shehu ya saki bayanin dukiyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mallaka a ranar Alhamis da ta gabata jaridar Washington Post ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin talaka a cikin shugabannin Afirka.A makon jiya ne gwamnati ta bayyana cewa Shugaba kasa Buhari yana da Dala dubu 150 ne […]

‘Buhari ne talaka a cikin shugabannin Afirka’

Bayan da Kakakin Shugaban kasa Garba Shehu ya saki bayanin dukiyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mallaka a ranar Alhamis da ta gabata jaridar Washington Post ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin talaka a cikin shugabannin Afirka.
A makon jiya ne gwamnati ta bayyana cewa Shugaba kasa Buhari yana da Dala dubu 150 ne kacal (kimanin Naira miliyan 30) a asusun ajiyarsa sai kuma gidaje biyar da ya mallaka tare da gona da shanu 270 da tumaki 25 da dawaki biyar da tsuntsaye nau’i-nau’i. Sanarwar ta kuma ce Shugaban kasa ya sayi motoci biyu daga tattalin da ya rika yi daga dukiyarsa.
“Shugaba Buhari ba ya da asusun ajiyar banki a waje. Kuma ba ya da kamfani ko masa’anta ko wani wani kamfanin harkar kasuwanci mallakarsa kuma ba ya da rijiyar mai,” inji sanarwar da Garba Shehu ya fitar.
 Jaridar Washington Post ta ce tambayar da take cikin zukatan jama’a ita ce: A matsayin Buhari na tsohon Shugaban kasa na soja kuma tsohon Ministan Man Fetur gaskiya yake fadi?
Almundahana dai shi ne babban matsalar da ke barazana ga Najeriya wadda ta fi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afirka.
Shi kansa Shugaba Buhari ya ce sama da Dala biliyan 150 (kusan Naira tiriliyan hudu) ne suka yi batan dabo daga asusun gwamnati. Sai dai duk da haka bayyana wa jama’a dukiyar da ya mallaka wani yunkuri ne na nuna misali nagari wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana. An zabi Shugaba Buhari ne a watan Maris sakamakon yadda ya sha alwashin yaki da almundahana.
A cewar jaridar, abin da yake fili shi ne, abin da Shugaba Buhari ya yi abu ne da galibin magabatansa – da sauran shugabannin kasashen Afirka suke kin yi ko ma ba su taba yi ba.
Bayyana dukiyar da shugabanni da ma’aikata suka mallaka  ga Hukumar Kula da da’ar Ma’aikata ta Najeriya (CCB) wajibi ne a karkashin tsarin mulkin Najeriya, sai dai bayyana shi a bainar jama’a wannan ganin dama da zabin mutum ne.
Hukumar CCB daga farko ta yanke hukuncin cewa ma’aikatan da ke kan matakin albashi na 14 zuwa sama ne (wadanda suke matakan manajoji) ne kawai za a bukaci su bayyana mata kadarorinsu. Daga baya ta rage zuwa masu matakin albashi na 10. Yanzu kuma hukumar ta bukaci wadanda suka kai matakin albashi na Bakwai zuwa sama su bayyana mata kadarorinusu a rubuce.
An rika fadakarwa kan wannan batu domin ganin an samu sakamakon da ya kamata. Kuma hukumar ta ce idan ta samu kudi da wadatattun ma’aikatan da take bukata nan gaba za ta bukaci ma’aikata tun daga mai matakin albashi na daya zuwa sama ya bayyana dukiyar da ya mallaka gare ta.
 A karkashin sashi na 11. (1) na tsarin mulkin Najeriya wajibi ne duk ma’aikacin da wannan doka ta shafa ya bayyana wa Hukumar CCB dukiyar da ya mallaka bayan kafa ta da wata uku ko kuma da zarar ya fara aiki ko an rantsar da shi.
karamin kashi na (a) (b) ya kara da cewa kuma duk wanda dokar ta shafa zai: “sake bayyana dukiyar da ya mallaka a bayan shekara hudu, kuma a karshen mulkinsa ko yin ritaya daga aiki, zai mika wa Hukumar CCB rubutaccen bayani kan dukiyarsa na kudi da kadara da bashin da ke kansa da na ’ya’yansa da bai aurar ba da su da suke kasa da shekara 18.”
Kashi na (2) ya ce “Duk wani bayani kan bayyana kadarorin da hukuma ko wanda hukuma ta sanya ya gano karya ne, za a dauki hakan a matsayin keta wannan doka da za a iya hukunta mutum a kai.”
A cikin fom din bayyana kadarorin hatta kayan dakin girki da na dakunan kwanan iyalin ma’aikaci ko shugaba sai mutum ya bayyana. Sannan sai ya bayyana yadda aka yi ya same su ko ta saya ko gado ko kyauta ko bashi. Sannan bayan ya cika fom din zai je gaban alkalin Babbar Kotu ya yi rantsuwar cewa abin da ya fada gaskiya ne kafin ya koma wa Hukumar ta CCB da fom din. Hukumar kuma tana iya sanya ma’aikatanta su je su bincika don tabbatar da abin da aka fada a cikin fom din gaskiya ne ko ko akasin haka.
Jaridar Washington Post ta kawo misalan wasu shugabannin Afirka biyar da ta ce mujallar Forbes ta bayyana su da  cewa: shugabannin Afirka biyar da suka fi gazawa da kuma wawurar dukiya. Shugabannin su ne:

1.  Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, Shugaban kasar Ekuatorial Guinea
Shi ne Shugaban da ya fi kowane shugaba a Afirka dadewa a kan mulki, dan mulkin kama-karya da ke jagorantar karamar kasa mai arzikin man fetur a Afirka ta Yamma. Sai dai duk da dimbin arzikin albarkatun kasa, mafi rinjayen jama’arta suna rayuwa cikin bakin talauci da ko ruwan sha mai kyau ba su samu, babu ilimi mai inganci babu ingantacciyar kiwon lafiya. An gano kowane yaro daya daga cikin yara biyar da ake haihuwa a kasar yana mutuwa kafin ya cika shekara biyar. Ana zargin kudi kasar suna fadawa ne cikin aljihun Shugaba Mbasogo da iyalansa. Sun mallaki gine-gine na gani a fada a Amurka da sauran kasashen Turai da jirgin kashin kai da dimbin motoci na kasaita.

2. Jose Eduardo dos Santos, Shugaban Angola
Shi ne Shugaba na biyu mafi dadewa a Afirka, kuma kasar Angola ce kasa ta biyu wajen arzikin man fetur a Nahiyar Afirka, kuma daya daga cikin wadanda suka fi samar da mai ga Amurka. Sannan tana da dimbin arzikin lu’u-lu’u. Dangin Santos suna rike da manyan mukamai a gwamnatinsa tare da juya mafi yawan dukiyar Angola a daidai lokacin da ake kuka da muguwar almundahana a kasar. Bayanai sun nuna cewa kashi 70 cikin 100 na jama’ar kasar suna fama da kuncin talauci, kuma sulusin yaran kasar suna fama da rashin abinci mai gina jiki saboda bakar yunwa.

3. Robert Mugabe, Shugaban Zimbabwe
Ya mulki kasar da ke Kudancin Afirka na fiye da rubu’in karni. Ya rika kirkiro tsare-tsare marasa kan gado da suka hada da kwace gonakin kasuwanci na fararen fatar kasar, lamarin da ya jawo faduwar darajar kudin kasar da miliyan guda ba ta isar mutum karya kumallo a teburin mai shayi. Sai dai a baya-bayan nan tattalin arzikin kasar ya rika farfadowa, yayin da Mugabe ya ci gaba da nuna mulkin kama-karya. Ya zama gagarabadau inda ya zama shi ne wuka da nama wajen juya daukacin hukumomin gwamnati, kuma magoya bayansa na amfani da tashin hankali don ci gaba da rike gwamnati.
 
4. Omar Al-Bashir, Shugaban Sudan
Janar Hassan Al Bashir wanda ya zama Shugaban Sudan bayan juyin mulkin da ba a zubar da jini ba a 1989 ya haramta jam’iyyun siyasa da majalisa da rufe wasu gidajen jaridu. An fafata yakin basasa a zamaninsa inda ake zargin an kashe mutum miliyan guda, lamarin da ya sa Kotun Duniya take neman Shugaba Bashir ruwa a jallo kan laifuffukan yaki da cin zarafin dan Adam kan   abin da ta kira rawar da ya taka a kisan fararen hula da fyade a yankin Darfur da ke kasar Sudan. Sannan wani sakon da wani jami’in diplomasiyyar Amurka da kafar tereren nan ta Wikileaks, ta sake ya bayyana cewa akwai yiwuwar Shugaba Bashir ya sace akalla Dala biliyan tara (kimanin Naira tiriliyan daya da biliyan 800) na jama’ar kasar ya sanya shi a asusunsa na banki a Birtaniya.

5.  Sarki Mswati III, Sarkin Swaziland
Mutum na biyar a cikin shugabannin Afira biyar da mujallar ta zarga da gazawa shi ne Sarki mafi dadewa a gadon mulki da ke mulkin kasar da take cikin kasashen duniya mafi fama da cutar kanjamau tare da saurin mutuwa ta yadda akasarin jama’ar kasar ke macewa suna da shekara 33.
Duk da wahalar da jama’arsa ke ciki, Sarkin yana gudanar da rayuwa ta fantamawa da facaka da dukiya inda yake shiga motocin kasaita da tafiye-tafiye a jirage mafiya tsada da gudanar da bukukuwan da ake kashe makudan kudi a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke makyarkyatar mutuwa.