‘Buhari Shugaba ne mai hakuri da ke bukatar addu’a’
Shugaban Riko na Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta gundumar Kafanchan a Jihar Kaduna, Malam Hamza Ibrahim, ya ce ba abin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake bukata da ya wuce a taimaka masa da addu’a domin Allah Ya ba shi nasara a shugabancin da yake yi saboda shi mutum […]
Shugaban Riko na Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta gundumar Kafanchan a Jihar Kaduna, Malam Hamza Ibrahim, ya ce ba abin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake bukata da ya wuce a taimaka masa da addu’a domin Allah Ya ba shi nasara a shugabancin da yake yi saboda shi mutum ne mai matukar hakuri da kishin kasa. ya Malam Hamza Ibrahim ya bayyana haka ne a Kafanchan lokacin da yake ganawa da Aminiya, inda ya ce “amma kuma duk wanda ya shiga rigar Buhari ya fake yana kashe al’umma, yana satar dukiyar gwamnati yana cutar jama’a, to wannan ya sani shi da Allah.”
Malamin ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dubi matsalar rashin wutar lantarki da ruwa da sauran abubuwan more rayuwa da suke addabar kasar nan don ta magance su saboda jama’ar kasa su ga canjin da suka dade suna sauraro, kuma ya yi kira ga jama’a su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, domin sai da zaman lafiya ne a ke samun ci gaba.
Da ya juya kan cikar gwamnatin Jihar Kaduna shekara daya a kan karagar mulki, Malamin ya yaba wa Gwamnan Jihar, Malam Nasiru El-Rufa’i da sanadiyyar zuwansu Allah Ya kawo karshen tashe-tashen hankulan da jihar ke ciki aka samu zaman lafiya.
“Ya zama dole mu gode wa Allah, amma duk da haka mutum tara yake bai cika goma ba, don haka muna kira ga Gwamna El-Rufa’i ya saurari irin koke-koke kan halin da jama’a ke ciki musamman wajen biyan albashin ma’aikata domin akwai ma’aikacin da tun watan azumin bara har yau bai sake ganin albashi ba alhali da wannan albashin ya dogara wajen ciyar da iyalansa da sauran bukatu, na tabbata idan Gwamna ya taimaka irin wadannan ma’aikata suka ji dadi a wannan wata, to shi ma zai samu albarkarsu,” inji Malamin.
Malam Hamza ya kuma bukaci al’ummar Musulmi su yi amfani da watan Ramadan wajen neman kusanci da Allah da kuma neman gafararSa domin Allah Ya kawar da musifun da ake ciki, inda ya ce tuba da istigfari suna kawo sauki a rayuwa ba gwamnati ce ke kawo talauci ko arziki ba.
“Dole ne Musulmi su kaunaci juna, su hadu su rufa wa kansu asiri ba masu hali ne kawai za su iya taimako ba, a’a idan ni da kai da wannan da wancan muka hadu za mu iya saya wa mabukaci abinci, ko biya masa kudin asibiti ko na makarantar ’ya’yansa da sauran ayyuka na taimakon kai-da-kai kuma da shi ne za mu rufa wa junanmu asiri ba mu rika barin zuciyar ’yan uwanmu na mutuwa wadansu na shiga barace-barace tun daga nan har kasar Saudiyya da sauran abubuwan kaskanci,” inji shi.