Buhari ya amince a kara wa ‘yan sanda sabon albashi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da a kara wa Hukumar ‘yan sandan Najeriya sabon tsarin albashi don inganta walwalarsu. An sanar da karin albashin ma’aikatan ne bayan tattaunawar da aka yi da shugabannin hukumar ‘yan sandan, wanda Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya jagoranta. Sai dai rahoton bai bayyana mukaman da […]

Buhari ya amince a kara wa ‘yan sanda sabon albashi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da a kara wa Hukumar ‘yan sandan Najeriya sabon tsarin albashi don inganta walwalarsu.

An sanar da karin albashin ma’aikatan ne bayan tattaunawar da aka yi da shugabannin hukumar ‘yan sandan, wanda Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya jagoranta.

Sai dai rahoton bai bayyana mukaman da aka yi wa karin albashin ba.