Buhari ya baiwa ma’aikatun gwamnati mako biyu su mika kasafin kudinsu
Shugaba Muhammadu Buhari ya ummarci ma’aikatun gwamnati su mika cikakken kasafin kudinsu na shekarar 2018 ga kwamitocin da suka dace na majalisa kafin ranar Juma’a, 23 ga watan Maris na shekarar 2018. Sakataren gwamnati, Mista Boss Gida Mustapha shi ne ya bayar da ummarnin a ranar 19 ga watan Maris na shekarar 2018 mai […]

Shugaba Muhammadu Buhari ya ummarci ma’aikatun gwamnati su mika cikakken kasafin kudinsu na shekarar 2018 ga kwamitocin da suka dace na majalisa kafin ranar Juma’a, 23 ga watan Maris na shekarar 2018.
Sakataren gwamnati, Mista Boss Gida Mustapha shi ne ya bayar da ummarnin a ranar 19 ga watan Maris na shekarar 2018 mai lamba SGF/OP/1/S.3/XII.
Takardar ummarnin mai taken “ Mika cikakken bayanin kasafin kasafin kudi na shekarar 2018 ga ma’aikatun gwamnati da sauran hukumomin gwamnati ga majalisar tarayya” ta ummarci ma’aikatun gwamnatin su aiwatar da ummarnin da aka basu ta hanyar amsa gayyatar da aka yi musu don kare kasafin kudin.