Buhari ya bayyana ayyukan da zai gudanar a shekarar 2018
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa al’ummar kasar jawabi na sabuwar shekara inda ya bayyana ayyukan dogo da hanyoyi da kuma wutar lantarki da gwamnatinsa za ta gudanar a shekarar 2018. Daga cikin manyan ayyukan da za a gudanar a wannan shekarar, akwai titin jirgin kasa (dogo) da zai kama daga Kano ya ratsa da […]
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa al’ummar kasar jawabi na sabuwar shekara inda ya bayyana ayyukan dogo da hanyoyi da kuma wutar lantarki da gwamnatinsa za ta gudanar a shekarar 2018.
Daga cikin manyan ayyukan da za a gudanar a wannan shekarar, akwai titin jirgin kasa (dogo) da zai kama daga Kano ya ratsa da Kazaure da Katsina har zuwa Maradi na Jamhuriyar Nijar. Da kuma titin hanyar Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano.