Buhari ya bukaci manoma su rungumi noman alkama

Abin takaici ne irin makudan kudaden da ake kashewa duk shekara wajen shigo da alkamar.

Buhari ya bukaci manoma su rungumi noman alkama

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci manoman Najeriya su rungumi noman alkama don samar da alkamar da za a rika amfani da ita a kasar nan, ba sai an rika shigo da ita daga kasashen waje ba.

Shugaban Kasar ya bayyana haka ne, a jawabinsa wajen bikin kaddamar da noman alkama na bana da aka gudanar a kauyen Kwall da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato.

Gwamnan Jihar Filato, Mista Simon Lalong wanda ya wakilci Shugaban Kasar ya ce, harkokin noma na ba da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Kuma a bana harkokin noma sun bayar da kashi 23 cikin 100 na kudaden shigar da ake samu a kasar nan.

Shugaban Kasar ya ce, don haka ne gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen bunkasa harkokin noma don ganin an bunkasa tattalin arzikin kasar nan, tare da samar da wadataccen abinci a kasa.

Ya kara da cewa, Najeriya kasa ce da ake noman shinkafa da masara da waken soya da gyada da rogo da kwarar manja da koko kuma nan ba da dadewa ba za a rungumi noman alkama.

“Abin takaici ne irin makudan kudaden da ake kashewa, wajen shigo da alkamar da kamfanonin sarrafa fulawa da ke kasar nan suke yi. A duk shekara ana kashe sama da Dala biliyan biyu wajen shigo da alkama daga waje zuwa kasar nan.

“Bayan za mu iya noman alkamar, kamar yadda muke noman shinkafa musamman a lokacin rani.

“Bincike ya nuna cewa za a iya noman alkama a jihohin Filato da Taraba da Kuros Riba da sauran jihohin Arewa,” inji Shugaban Kasar.

A jawabin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele wanda Mataimakinsa Edward Lamtek Adamu ya wakilta ya ce, a kokarin bankin na ganin ya cike gibin da ake samu na noman alkama, bankin ya yanke shawarar tallafa wa noman alkama ta hanyar tsare-tsaren Bankin Manoma na Najeriya.

Mista Adamu ya ce, babban bankin ya tallafa wajen samar da ingantaccen irin alkama daga kasar Meziko, wanda zai rika samar da tan biyar zuwa tan bakwai a duk eka daya.