Buhari ya cire Kachikwu daga shugabancin NNPC ya nada Baru
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke Minista a Ma’aikatar Man Fetur Mista Ibe Kachikwu daga mukamin Babban Manajan Daraktan Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC), inda ya nada Dokta Maikanti Kacalla Baru a kan mukamin.Nadin ya kawo karshen daukar watanni ana muhawara kan wanda zai karbi shugabancin Kamfanin NNPC daga Kachikwu bayan da aka nada […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke Minista a Ma’aikatar Man Fetur Mista Ibe Kachikwu daga mukamin Babban Manajan Daraktan Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC), inda ya nada Dokta Maikanti Kacalla Baru a kan mukamin.
Nadin ya kawo karshen daukar watanni ana muhawara kan wanda zai karbi shugabancin Kamfanin NNPC daga Kachikwu bayan da aka nada shi a matsayin Minista a watan Nuwamban bara.
Minista Kachikwu yanzu zai shugabancin Hukumar Gudanarwar Kamfanin NNPC da Shugaban kasar ya amince da nadinta, kamar yadda aka tanada a dokar Kamfanin NNPC ta 1997.
Kakakin Shugaban kasa Mista Femi Adesina ne ya bayar da sanarwar nadin da kuma kafa hukumar a ranar Litinin da ta gabata a Abuja.
Sabuwar Hukumar Gudanarwar ta kunshi Minista Kachikwu a matsayin shugaba, sai sabon Babban Manajan Daraktan Kamfanin NNPC, Maikanti Baru da Babban Sakataren Ma’aikatar Kudi da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa, Malam Abba Kyari da Dokta Thomas M.A. John da Dokta Pius O. Akinyelure da Dokta Tajuddeen Umar da Malam Mohammed Lawal da Malam Yusuf Lawal a matsayin wakilan hukumar.
Shugaba Buhari ya bukaci wakilan sabuwar hukumar su tabbatar da sun sauke nauyin da aka dora musu wajen bauta wa kasar nan ta hanyar rikon amana da kula da muhimmiyar dukiyar kasa.
Dokta Maikanti Kacalla Baru, wanda ya fito daga karamar Hukumar Jama’are a Jihar Bauchi mai kimanin shekara 57 ya samu digirinsa na farko ne kan Injiniyan Kanikanci daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da daraja ta kwaloluwa. Kuma ya yi digirinsa na biyu da na uku a dai wannan fanni.
Ya yi aiki a Kamfanin NNPC a matakai da dama da suka hada da Babban Darakta (GED) a harkar hakowa da sarrafa mai, sai Babban Manaja GGM a LNG da Babban Manaja a Kamfanin Zuba Jari kan Mai (NPIMS) da Babban Darakta a Kamfanin Carlson Serbice da ke kasar Ingila da sauransu kafin a nada shi mai ba Minista Kachikwu shawara.