Buhari ya dakatar da kai ziyara Ogoni Land

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da ziyarar ya shirya kai wa a yau (Alhamis) zuwa yankin Ogoni da ke Jihar Ribas a yankin Neja-Delta mai arzikin mai. An shirya shugaban zai kaddamar da share man da ya malala a yankin, amma majiyoyi da dama a fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa shugaban yana […]

Buhari ya dakatar da kai ziyara Ogoni Land

Shugaban Kasa Muhammadu BuhariShugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da ziyarar ya shirya kai wa a yau (Alhamis) zuwa yankin Ogoni da ke Jihar Ribas a yankin Neja-Delta mai arzikin mai.

An shirya shugaban zai kaddamar da share man da ya malala a yankin, amma majiyoyi da dama a fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa shugaban yana nan a fadarsa, inda kuma aka ce Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ne zai wakilce shi.

Har ila yau, an bayyana cewa Kakakin Shugaban Femi Adesina zai yi karin bayani nan gaba kadan game da dalilin da ya sa shugaban fasa ziyarar.