Buhari ya fara neman bayanan asusun hukumomin gwamnati

Yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin fara aiki gadan-gadan, ya bukaci a kawo masa bayanan asusun ajiyar bankuna na ma’aikatu da hukumomin gwamnati. Umarnin mai dauke da kwanan wata 1 ga Yuni, 2015, na kunshe ne a cikin wata takarda mai lamba: TRY A4 & B4/2015 /OAGF/CAD/026/b .1/254, kuma tsohon Babban Akantan Tarayya […]

Buhari ya fara neman bayanan asusun hukumomin gwamnati
Buhari ya fara neman bayanan asusun hukumomin gwamnati

Yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin fara aiki gadan-gadan, ya bukaci a kawo masa bayanan asusun ajiyar bankuna na ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Umarnin mai dauke da kwanan wata 1 ga Yuni, 2015, na kunshe ne a cikin wata takarda mai lamba: TRY A4 & B4/2015 /OAGF/CAD/026/b .1/254, kuma tsohon Babban Akantan Tarayya Mista Jonah Otunla, ya bayar da ita kafin ya yi ritaya daga aiki a makon jiya.
Takardar mai taken: “Bukatar gaggawa kan bayanan kudaden da ke cikin asusun ajiyar bankuna na ma’aikatu da hukumomin gwamnati a Babban Bankin Najeriya zuwa 29 ga Mayu, 2015.” Takardar ta ce, a hada da dukkan asusun ajiyar kowace hukuma ciki har da na kasashen waje kuma ya shafi asusun ajiya na ofisoshin jakadancin Najeriya da ke waje, ya alla ana amfani da asusun ko ba a yi, tare da lambobinsu da masu sanya hannu a kan kowane asusu.
Takardar ta yi gargadin cewa za a dauki mataki mai gauni kan duk wani jami’i da ya boye wani asusu ko ya jirkita bayanan wani asusu kamar sake masa fasalin da Fadar Shugaban kasa za ta dauka haramtacce ne. Kuma an umarci hukumomin su samar da bayanan a bugaggun takardu da kuma ta na’urorin kwamfuta.
Ana ganin gwamnatin Buhari ta dauki wannan mataki ne domin daddale daukacin kudaden da gwamnati ke da su ko take samu tun daga tushe domin toshe kafafen sace kudin a daidai lokacin da ake fama da karayar tattalin arzikin kasa. Kuma daya daga cikin matakan da sabuwar gwamnatin ta fara dauka shi ne na dakile dukkan hanyoyin da ake sace dukiyar man fetur.
Majiyoyi masu karfi sun ce mika wa bayanan asusun shi ne mataki na farko da gwamnatin Buhari ta dauka don binciken harkokin kudaden Gwamnatin Tarayya, musamman kan yadda aka zargi gwamnatin da ta gabata da biyan makudan kudi ga ’yan kwangila da wasu kwararru a watanninta na karshe. Kuma bayanai sun ce gwamnatin Buhari za ta sanya ka’idoji masu tsauri ga hukumomin gwamnati musamman sassan ma’aikatu da suke karbar kudi daga hannun jama’a su rika kashe kudin yadda suka ga dama.
A tsari na yanzu, an bar hukumomin gwamnati da ba a bayyana su da “Hukumomin Tara Kudin Shiga” ba, suna kashe kudaden da suka tara su mika wa baitul mali abin da ya saura a karshen kowace shekara. Kuma majiyoyi a Ma’aikatar Kudi sun ce hukumomi kalilan ne suke bin doka, kuma galibinsu sukan yi kokarin kashe kudaden gaba daya kafin karshen shekara ko su dan samar da abin da suka ga dama ga baitul malin, a matsayin “kudin da ba a kashe ba,” yayin da suke ajiya saura a asusunsu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos